Daga Khalid Yusuf Sambo
Kamar yadda a ke ganin a hoton da ke kasa, shahararriyar Jami'ar nan ta Musulunci ta Duniya da ke Birnin Madinar Manzon Allah (S.A.W) ta ayyana Littafin:
ضوابط الجرح والتعديل عند الحافظ الذهبي
Wallafar Prof. Muhd Sani Umar R/lemo (Hafizahullah) a cikin jerangiyar littafan da za ta yi wa daliban da ke gurbin karatun Digiri na uku (Ph.D) Jarrabawa a cikinsa. Shi ne Littafi daya tilo na mutumin yankin kaf Afirka da ya samu wannan tagomaci.
Hakika wannan yana sake nuna karbuwar Littafin da ficensa a Duniyar ilimi. Da ma kuma Littafi ne da ba a shaida kamarsa a bangarensa ba. Littafin shi ne kundinsa na samun shaidar kammala matakin Digiri na biyu a Jami'ar Musulunci ta Madina, wanda a lokacin ya rabauta na samun koluluwar mataki da jinjina mafi girma a fanni...
ABIN MAMAKI: Wasu Mabiya Shi'a Sun Aikawa Fàĺàšďìnawa Tallafìn Ķayan Àbinci Ta Hanyar Jefàwà Cìkin Kogin Legas, Inda Sùke Fatàn Sakòn Tàllafin Ya Kài Kasaŕ Fàlàsdìñ
Ko kuna ganin sakon zai kai?
Daga A Sayyadee Funtua A
ADC TA RIKICI A KEBBI: Shugabanin Jam'iyar ADC A Jihar Kebbi Sun Dakatar Da Ciyaman Engr. Sufiyanu Bala Da Mataimakinsa Junaidu Muhd Da Kuma Sakataren Jam'iyyar Hauwa'u Muhammad
A sanarwar da suka fitar ga manema labarai, Shugabannin su sha bakwai dukkansu sun aminta da dakatarwa a bisa zaŕge-zargen da suka gabatar.
Masu laifi 16 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Keffi dake jihar Nasarawa
Lamarin ya farune da sassafiyar ranar Talata.
Me magana da yawun hukumar kula da gidajen gyara hali na kasa, Umar Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami'an hukumar 5 ne suka jikkata sanadiyyar lamarin.
Yace 2 daga ciki suna cikin mawuyacin hali
Saidai yace an kama 7 daga cikin wadanda suka tsere kuma ana bin sahun sauran.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta mika sakon godiya ga 'yan uwa da abokan arziki da suka tayata Biki.
Rahama ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace bata da kalaman godiya da zata iya bayyana irin farin cikin da take ciki.
"Ina mika sakon godiya ta musamman ga dangi, ’yan uwa da abokan arziki bisa fatan alheri da addu’o’in ku a game da Auren mu. Kalmominku da addu’arku sun karfafa mana guiwa kuma sun sa ranar ta kasance ta musamman. Allah Ya saka da alkhairi.
Bani da kalmomin yi muku godia sai dai nace Allah ya saka muku da alheri, Allah yabar zumunchi na gode, na gode, Allah ya biyawa kowa bukatun sa na alheri. Ameen
Ni kuma Allah ya bamu zaman lafia da Miji na Allah ya Albarkachi rayuwar auren mu. Ameen ya rabbil Alameen.
Ina yiwa kowa fatan alhe...
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana cewa, Akwai wata kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da yake cikinta wadda suka ce 'yan Arewa jahilaine.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace ya gaya musu cewa wannan mutane sune ake neman kuri'arsu.
Yace Salon Mulkin Tinubu bai yi masa ba inda yace da ace yana cikin gwamnatin Tinubu da tuni ko dai ya sauka daga mukaminsa ko an koreshi ko wani abun.
Malamin darikar Tinjaniyya, Sheikh Abdulfatahi Sani ya bayyana cewa, Salatul Fatih bai fi Qur'ani ba.
Yace amma ana maganar lada ne.
Yace Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya gayawa shehu duk wanda ya karanta Salatil Fatih zai sau ladar sauke Qur'ani sau 1000 zuwa sama.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
https://www.tiktok.com/@zubairuabdullahi77/video/7536898346557000965?_t=ZS-8yoKXxpimIr&_r=1
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta gayyaci tsaffin Gwamnoni 3 na jam'iyyar ADC.
Hakan ya saka rudani a jam'iyyar ta ADC inda sukw zargin kokarin murkushe su ne yasa EFCC ta fara bincken membobin jam'iyyar.
Tuni dai EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal inda take tuhumarsa bisa cire wasu kudi da suka kai Naira Biliyan 189 lokacin yana gwamnan Sokoto.
Me magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa, wannan abu ana kokarin ganin an tursasa mutane sun bar jam'iyyar ta ADC ne.
Inda ya tabbatarwa da jaridar Punchng cewa an gayyaci tsaffin gwamnoni 3 zuwa EFCC amma yace ba zai fadi sunayensu ba.