Monday, December 22
Shadow
Ba kamar yanda ake cewa mun Kàshè ‘yan sa kai da yawa ba a Zamfara, Guda biyu ne kawai suka mùtù bayan jirgin saman mu yayi kuskuren jefa musu Bàm da tunanin cewa ‘yan Bìndìgà ne>>Hukumar Sojojin Najeriya

Ba kamar yanda ake cewa mun Kàshè ‘yan sa kai da yawa ba a Zamfara, Guda biyu ne kawai suka mùtù bayan jirgin saman mu yayi kuskuren jefa musu Bàm da tunanin cewa ‘yan Bìndìgà ne>>Hukumar Sojojin Najeriya

Duk Labarai
Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai hare-hare ta sama a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar, tana mai cewa dakarun sa-kai biyu sun rasu yayin da take harar 'yanfashin daji. A jiya Litinin ne mazauna ƙaramar hukumar Maru suka shaida wa BBC Hausa cewa jirgin yaƙin sojin ya kashe 'yan sa-kai, yayin da ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mayaƙa 20 aka kashe a lokacin da suke bin sawun 'yanbindigar da suka kai musu hari da sace wasu mutane. Kakakin rundunar Ehimen Ejodame ya ce hare-haren da suka kai bayan samun bayanan sirri sun yi sanadiyyar kashe 'yanbindigar 20. "A martanin da muka mayar cikin gaggawa ranar 31 ga watan Mayu, dakarunmu sun kashe sama da 'yanta'adda 20 tare da lalata babura fiye da 21," a cewarsa yayin wani taron manema labarai&...
Kalli Hotuna: An kàshè sojojin Isra’ila uku a Gàzà

Kalli Hotuna: An kàshè sojojin Isra’ila uku a Gàzà

Duk Labarai
Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sunayen dakarunta uku da ta ce an kashe a arewacin Zirin Gaza ranar Litinin. Mutanen uku da ke da shekaru 20 da ɗoriya sun fito daga bataliya ɗaya - an ce biyu daga ciki likitoci ne, na ukun kuma kwamanda, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin ta IDF ta fitar. Jaridar Times of Israel ta bayar da rahoton cewa an kashe su ne sakamakon wani bam da ya tashi da su lokacin da suke tsaka da fafatawa da mayaƙan ƙungiyar Hamas a yankin Jabalia.
Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Duk Labarai
Sanata Orji Uzor Kalu dake wakiltar mazabar Abia North a majalisar Dattijai ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ne da manyan ma'aikatan Gwamnati da 'yan Kasuwa ke daukar nauyin ayyuka Kungiyar Bòkò Hàràm. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV. Yace kuma masu yin hakan suna yi ne dan kawai su hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu iya gudanar da Gwamnatinsa yanda ya kamata. Yace amma ba ta haka bane ake karbar mulki, yace yawanci suna yi ne dan su kwace mulki daga hannun Tinubu ba kudi bane a gabansu.
Gwamnatin Tarayya zata biya bashin Naira Tiriliyan 2 na kudin wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya zata biya bashin Naira Tiriliyan 2 na kudin wutar lantarki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara amincewa da batun biyan bashin Naira Tiriliyan 2 na wutar lantarki da akw binta. Hakan kokarine na samar da ingantacciyar wutar Lantarki a Najeriya. Na kusa da me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar makamashi, Eriye Onagoruwa ce ta bayyana hakan a wajan wani taron masu ruwa da tsaki na harkar wutar da aka gudanar. Tace gwanatin na duba muhimmancin hakan wajan samar da wutr Lantarki me karfi. Inda tace gwamnatin na kokarin ganin ta samar da wata hanya ta bashi dan biyan wannan bashi musaman lura da karancin kudin da gwamnatin ke fama dashi.
Kalli Bidiyon: Mutum daya ya rasu, 69 sun jikkata yayin girgizar kasa a Turkiyya

Kalli Bidiyon: Mutum daya ya rasu, 69 sun jikkata yayin girgizar kasa a Turkiyya

Duk Labarai
Girgizar kasa ta faru a kasar Turkiyya inda mutane 69 suka jikkata. Yawanci wadanda suka jikkatar sun diro ne daga benaye saboda fargabar kada gidan da suke ciki ya rushene. Saidai mutum daya ya mutu. Karfin girgizar kasar ya kai maki 6.2 kamar yanda masana suka sanar. https://twitter.com/geotechwar/status/1929690994091741373?t=qa7qPmG2xXaNo2yyCcmrog&s=19 Kasar Turkiyya dai na daga cikin kasashe masu yawan fuskantar Ambaliyar ruwa.
Da Duminsa: Wani Dan Bìndìgà da yafi Bèllò Tùrjì rashin Imagi da hadari ya bayyana, ji mummunar ta’asar da ya aikata

Da Duminsa: Wani Dan Bìndìgà da yafi Bèllò Tùrjì rashin Imagi da hadari ya bayyana, ji mummunar ta’asar da ya aikata

Duk Labarai
Rahotanni sun ce wani dan Bindiga me suna Dan Sadiya ya bayyana inda aka bayyana shi da cewa yafi Bello Tùrji illa. Rahoton yace ya jagoranci kai hare-hare a jihar Zamfara wanda suka yi sanadiyyar kashe fararen hula da kuma kona kauyuka. A cikin wasu Bidiyon da ya saki an ga ya nuna motar APC ta sojojin Najeriya da ya kwace wadda ake amfani da ita ana harbo jirgin sama. An yi kira ga jami'an tsaro da su gaggauta daukar mataki akansa. https://twitter.com/Edrees4P/status/1929462831486804314?t=oL_F3FzI0FsqZR9Rrwi0EQ&s=19 Ko kuna ganin wane mataki ya kamata a dauka akansa?
Da Dumisa: Kasar Sifaniya ta bi sahun kasar Afrika ta kudu wajan kai karar kasar Israyla kan kìsàn kiyashin da takewa Falasdiynawa

Da Dumisa: Kasar Sifaniya ta bi sahun kasar Afrika ta kudu wajan kai karar kasar Israyla kan kìsàn kiyashin da takewa Falasdiynawa

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Spain na cewa kasar ta bi sahun kasar Afrika ta Kudu wajan kai karar kasar Israyla kotun Duniya saboda zargin kisan kiyashi da Israyla kewa Falasdinawa. Kasar Sifaniya dai ta dade tana kira ga kasashen Turawa da su kakabawa kasar Israyla takunkumi saboda kisan da takewa falasdinawa. A kwanannan ne dai Birnin Barcelona na kasar ya yanke dukkan wata hulda da kasar Israela saboda kisan da sukewa Falasdiynawa. Kasar Afrika ta kudu itace kasa ta Farko a Duniya data fara kalubalantar kasar Israela saboda kisan da takewa Falasdiynawa.
Nine kashin bayan Nasarar Tinubu ya zama shugaban kasa, Kuma idan PDP ta isa ta dakatar dani>>Wike

Nine kashin bayan Nasarar Tinubu ya zama shugaban kasa, Kuma idan PDP ta isa ta dakatar dani>>Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, shine kashin bayan nasarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a shekarar 2023. Ya kuma bayyana aniyarsa ta goyon bayan shugaba Tinubun a zaben shekarar 2027. Saidai hakan baiwa jam'iyyun adawa dadi ba inda suke ta sukarsa. Jam'iyyun da suka soki Wike kan bayyana ci gaba da goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu sun hada da NNPC, PDP, CUPP. Wike ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja ranar Litinin. Wike yace bai aikata laifin yiwa jam'iyyarsa ta PDP zagon kasa ba inda ya kalubalanci jam'iyyar da cewa idan kuma ya aikata laifin to su dakatar dashi. Saidai mataimakin shugaban matasa na jam'iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor ya gayawa '...