Shugaban kasar Nijar ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da kasarsa
Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya da haɗa baki da Faransa da China da Amurka wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a ƙasarsa.
A cikin wani jawabi na awa uku da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na Radio-Télévision du Niger (RTN) a ƙarshen mako, Tchiani ya yi magana da harshen Hausa, Zabarma da Faransanci, inda ya zargi Najeriya da Jamhuriyar Benin da Faransa da China da Aljeriya da Amurka da kokarin dagula ko cutar Nijar da sauran ƙasashen da ke cikin ƙawancen AES.
Wannan shi ne karo na biyu da Tchiani ke zargin Najeriya a yayin wata hira da ya yi ta ranar Kirsimeti a bara, inda ya ce Faransa na haɗa baki da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin tafkin Chadi domin lalata tsaron Nijar, tare da sanin Najeriya.
Tchiani ya ƙara da cewa an ...







