Friday, December 19
Shadow
Zamu daina baka makamai da yanke duk wata hulda da kai idan ka ci gaba da Kàshè Palasdiynawa>>Shugaba Trump ya gargadi Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu

Zamu daina baka makamai da yanke duk wata hulda da kai idan ka ci gaba da Kàshè Palasdiynawa>>Shugaba Trump ya gargadi Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu

Duk Labarai
Rahotanni daga fadar White House ta kasar Amurka na cewa, shugaban kasa, Donald Trump na ci gaba da matsawa Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu akan ya dakata da yakar Falasdinawa. Rahotan yace Shugaba Trump har ta kai ga ya gayawa Benjamin Netanyahu cewa ko dai ya daina wannan yaki ko su yanke duk wata hulda dashi. Benjamin Netanyahu dai ba zai so hakan ba saboda mafi yawa kasar Amurka ce ke sayar musu da makamai. Saidai a wata majiyar an ji cewa, Benjamin Netanyahu na fadar zasu ci gaba da yakin kuma zasu samu nasara ba tare da taimakon kasar Amurka ba. Hakanan a wani Rahoto me kama da wannan, kasashen Ingila, Faransa da Canada sun yi barazanar daukar kwakkwaran mataki muddin Israela bata dakata da sabbin munanan hare-haren da take kaiwa a Gaza ba da kuma janye hana ka...
Zamu ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya >>Matatar Dangote ta sha Alkawari

Zamu ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya >>Matatar Dangote ta sha Alkawari

Duk Labarai
Matatar man Dangin ta sha Alwashin ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya. Matatar tace tana ci gaba da rage farashin man ne saboda amincewa da ta rika sayen danyen man fetur din da kudin Naira. Tace tana godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya amince da yin hakan, kamar yanda wakilin matatar me suna Anthony Chiejina ya tabbatar. Matatar tace zata ci gaba da goyon bayan karfafa ci gaban tattalin arziki Najeriya da kuma tabbatar da saukin man fetur.
PDP ta koka da cewa, APC na ta mata kwacen mutanenta inda a yanzu haka Gwamnonin da suka rage ana musu Alkawari me gwabi idan suka shiga APC

PDP ta koka da cewa, APC na ta mata kwacen mutanenta inda a yanzu haka Gwamnonin da suka rage ana musu Alkawari me gwabi idan suka shiga APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar APC me mulki nawa gwamnonin PDP da tsaffin Gwamnonin jam'iyyar Alkawura masu gwabi idan suka yadda suka koma jam'iyyar. Rahotanni daga Punchng sun ce APC nawa Gwamnoni masu ci alkawarin za'a basu tikitin sake tsayawa takara idan suka yadda suka koma jam'iyyar ba tare da abokin takara ba, sannan kuma za'a basu dama su zabi wanda zai gajesu da wadanda zasu tsaya takarar 'yan majalisa. Sannan tsaffin Gwamnonin dake cikin PDP ana musu Alkawarin za'a basu mukaman Minitoci. Saidai Rahotan yace Atiku Abubakar yana jan hankalin su da cewa goyon bayan Tinubu kamar goyon bayan Rashin Nasara ne da Gwamnatin data gaza, inda yake jan hankalinsa da su goyi bayansa. Kakakin PDP, Debo Ologunagba ya koka da cewa, ana Amfani da Mulki wajan matsawa 'yan jam'...
An kara kama wani kasurgumin me Gàrkùwà da mutane a Filin jirgin Sokoto yana shirin zuwa Hajji

An kara kama wani kasurgumin me Gàrkùwà da mutane a Filin jirgin Sokoto yana shirin zuwa Hajji

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa, an kama wani Kasurgumin me Garkuwa da mutane a filin Jirgin jihar yana shirin zuwa aikin Hajji. Wanda aka kama din shine Sani Galadima a yayin fa yake daf da hawa Jirgi. An kamashi ne daidai wajan da ake tantance mutane. Rahoton yace hukumar 'yansandan farin kaya ce ta kamashi kuma za'a gurfanar dashi a kotu, da zarar an kammala bincike.
Hotuna: EFCC Ta Kama Masu Zamba a Yanar Gizo 120, Ta Kwato Motoci Masu Tsada a Jihar Legas

Hotuna: EFCC Ta Kama Masu Zamba a Yanar Gizo 120, Ta Kwato Motoci Masu Tsada a Jihar Legas

Duk Labarai
EFCC Ta Kama Masu Zamba a Yanar Gizo 120, Ta Kwato Motoci Masu Tsada a Jihar Legas. A ranar Litinin ɗinnan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC) reshen Lagos ta kama mutane 120 da ake zargi da aikata zamba ta yanar gizo — maza 95 da mata 25 — a wani samame da aka kai a wurare daban-daban cikin jihar Legas. An gudanar da samamen ne bayan samun sahihin bayanan sirri kan ayyukan masu damfara ta intanet. Abubuwan da EFCC ta kwato sun hada da: Motoci masu kyau guda 26 Kayan adon alfarma Wayoyi masu kyau da kwamfutoci Takardu da shaidu da ke da nasaba da zamba ta intanet EFCC ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike a kan wadanda ake zargin, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala binciken.
Da Duminsa: An kama daya daga cikin wanda suka kirkiro Manhajar Criypto ta Blum da zargin Damfara

Da Duminsa: An kama daya daga cikin wanda suka kirkiro Manhajar Criypto ta Blum da zargin Damfara

Duk Labarai
R ahotannin da hutudole ke samu na cewa an kama daya daga cikin wadanda suka kirkiro manhajar Crypto ta Blum sannan kuma tsohon ma'aikacin Binance bisa zargin hannu a wata damfara da aka tafka. Dama dai a baya, Vladimir Smerkis ya ce ya ajiye aiki da manhajar ta Blum. Manhajar ta Blum dai ta dade ana tsammanin zata shiga kasuwa amma shiru kake ji.
Da Duminsa: Dangantaka tsakanin Amurka da Israyla na kara tsami, yanzu haka mataimakin shugaban kasar Amurka, JD. Vance ya soke ziyarar da yake shirin kaiwa kasar saboda rashin jin dadin fadada hàrè-hàrèn da Israyla ke kaiwa Gàzà

Da Duminsa: Dangantaka tsakanin Amurka da Israyla na kara tsami, yanzu haka mataimakin shugaban kasar Amurka, JD. Vance ya soke ziyarar da yake shirin kaiwa kasar saboda rashin jin dadin fadada hàrè-hàrèn da Israyla ke kaiwa Gàzà

Duk Labarai
Rahotannin dake fitowa daga kasar Amurka na cewa, Mataimakin shugaban kasar, JD. Vance ya fasa kai ziyarar da yayi niyya zuwa kasar Israela. An bayyana cewa rashin jin dadin fadada hare-haren Israyla a Gaza ne yasa JD. Vance daukar wannan mataki. Dama dai a baya hutudole.com ya kawo muku rahoton cewa, Amurka na shirin amincewa da kafuwar kasar Palasdinu saboda an samu rashin jituwa tsakanin kasashen Biyu. Trump dai bai san ana juyashi yayin da rahotanni ke cewa, shi kuma shugaban Israela Benjamin Netanyahu yana son ya rika juya shuwagabannin Amurka.
Da Duminsa: Peter Obi yayi magana me dadi game da Rahoton dake cewa ya yadda ya zama mataimakin Atiku a 2027

Da Duminsa: Peter Obi yayi magana me dadi game da Rahoton dake cewa ya yadda ya zama mataimakin Atiku a 2027

Duk Labarai
A yayin rahoto yayi nisa cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Labour party a shekarar 2023, Peter Obi ya yadda yawa Atiku Abubakar mataimakin shugaban kasa a zaben shekarar 2027, Peter Obi din yayi martani kan wannan rahoton. Peter obi dai bai karyata wannan rahoto ba amma yace Koma me za'a fada aje ai ta fada amma shi yayi hadaka dan kawar da matsalar rashin tsaro da yunwa a Najeriya. Ya bayyana hakane a Kubawa Abuja wajan wani taro inda ya bayar da tallafi ga wata Makaranta. Dama dai a shekarar 2019, Peter Obi da Atiku ne suka tsaya takarar shugabancin Najeriya amma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kadasu.
Ji Yadda Gwamna Abba Gida-gida ya taimaki dalibar da ke fama da lalura bayan ta tura masa sako na neman taimako

Ji Yadda Gwamna Abba Gida-gida ya taimaki dalibar da ke fama da lalura bayan ta tura masa sako na neman taimako

Duk Labarai
Yadda Gwamna Abba Gida-gida ya taimaki dalibar da ke fama da lalura bayan ta tura masa sako na neman taimako. A cikin wani lamari mai ratsa zuciya , wata mata mai karfin gwiwa da buri, Mai suna Ummi mai shekaru 31, ta samu kulawar da ta daɗe tana mafarki daga gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf. Ummi ta shafe kusan shekaru 18 tana fama da wata cuta mai suna Proximal Myopathy, wadda ke sa raunin tsokokin jiki. Duk da wannan ƙalubale, ta kammala karatunta a fannin shari'a, amma rashin lafiya ya hana ta zuwa makarantar koyon aikin lauya (Law School). Duk da rashin tabbacin amsa, Ummi ta aike da saƙon neman agaji ga Gwamna Abba Kabir Yusuf. Cikin abin mamaki da tausayawa, Gwamna ya karanta saƙon kuma ya ɗauki matakin gaggawa. Wani faifan bidiyo da ya...
NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

Duk Labarai
Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu da kuma jam’iyya mai mulki ta APC dangane da wasu kalaman suka da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi a kwanakin baya. Jam’iyyar ta gargadi Kwankwaso da kada ya kara amfani da sunanta wajen sukar Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Kano an kore shi daga NNPP tuni. A wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na NNPP, Dakta Oginni Olaposi, ya fitar a ranar Lahadi a Legas, jam’iyyar ta nesanta kanta daga kalaman Kwankwaso, inda ta bayyana cewa an katse duk wata alaka tsakaninta da Kwankwaso da kuma kungiyar Kwankwasiyya da yake jagoranta. “Muna neman afuwa ga Shugaban kasa Bola Tinubu da dukan iyalan jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Dakta Abdulla...