Thursday, December 18
Shadow
Gwamnatin Kasar Saudiyya Ta Kama Matar Rìkàķķen Ďàn Bìndiģa Ado Aliero Da Mahaifiyarsa A Yayin Da Suka Je Aikin Hajjì

Gwamnatin Kasar Saudiyya Ta Kama Matar Rìkàķķen Ďàn Bìndiģa Ado Aliero Da Mahaifiyarsa A Yayin Da Suka Je Aikin Hajjì

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin Kasar Saudiyya Ta Kama Matar Rìkàķķen Ďàn Bìndiģa Ado Aliero Da Mahaifiyarsa A Yayin Da Suka Je Aikin Hajjì
Shekara daya bayan da Gwamnatin Tinubu tace an gyarasu ‘Har yanzu matatun man fetur na Fatakwal da Wari basu fara fitar da man fetur ba’

Shekara daya bayan da Gwamnatin Tinubu tace an gyarasu ‘Har yanzu matatun man fetur na Fatakwal da Wari basu fara fitar da man fetur ba’

Duk Labarai
Masu hada-hadar man fetur a Najeriya na kokawa kan yadda suke samun matsala wajen samun fetur daga matatun gwamnati guda biyu da aka gyara kwanan nan—matatar Fatakwal da na Warri—shekara daya bayan da aka bayyana cewa sun fara aiki. Najeriya, wadda ta shafe shekaru tana fama da ƙarancin man fetur, ta kashe kimanin dala biliyan 2.4 tun daga shekara 2021 domin farfaɗo da waɗannan matatun da ke yankin Niger Delta, da nufin dakatar da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje. Sai dai har yanzu, ba su fara fitar da man fetur ba. Kungiyar 'yan kasuwa masu gidajen mai ta Najeriya, PETROAN, ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sama da mambobinta 6,700 har yanzu na dogaro da shigo da mai daga waje da kuma matatar Dangote. Bisa bayanan ƙungiyar, har zuwa watan Maris ...
Dokar tilastawa ‘yan Najeriya su rika yin zabe ba zata yi aiki ba>>Inji Femi Falana SAN

Dokar tilastawa ‘yan Najeriya su rika yin zabe ba zata yi aiki ba>>Inji Femi Falana SAN

Duk Labarai
Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, SAN ya bayyana cewa, dokar tilastawa 'yan Najeriya sai sun yi zabe ba zata yi aiki ba. Majalisar wakilai ta fara tattaunawa akan wani kudirin doka da kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ya gabatar da ya bukaci kowace dan Najeriya me hankali dole ya rika yin zabe. Dokar dai har ta tsallake karatu na 2. Saidai a nasa jawabin, Femi Falana yace wannan doka ba zata yi aiki ba. Yace dokar Najeriya ta tanadi a baiwa dan Najeriya damar ya yi tunani akan wanda zai zaba sannan doka ta bashi damar ya boye wanda ya kadawa kuri'ar. Yace dan haka wannan doka ba zata yi aiki ba duk da yasan cewa ana kokarin zartas da itane dan karfafawa mutane yin zabe.
Daliba ‘Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar

Daliba ‘Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar

Duk Labarai
Daliba 'Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar Daga Comr Nura Siniya Shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Nasiru Yahaya Daura, ya miƙa ragamar shugabancin majalisa na minti 5 ga wata ɗaliba mai hazaƙa Marwa Nasir Yahaya, a lokacin da daliban makarantar suka kawo ziyarar duba ayyukan majalisar, domin sanin makamar aiki, a ranar Litinin 19 ga watan Mayu 2025. Katsina Reporters ta samu cewa, daliban makarantar “Little Angel ne suka zaɓi Marwa Nasir Yahaya, saboda kwazonta ga harkar ilimin addini da na zamani. Ɗalibar dai ta kasance ɗiya ga shugaban majalisar dokokin na jihar Katsina.
PDP ta bayyana yanda za’a yi a kayar da Tinubu karfe dayan rana a zaben 2027

PDP ta bayyana yanda za’a yi a kayar da Tinubu karfe dayan rana a zaben 2027

Duk Labarai
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa hadakata tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai zai baiwa 'yan adawa nasara akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027. Mataimakin shugaban matasa na jam'iyyar na kasa, Hon. Timothy Osadolor ne ya bayyanawa jaridar Vanguard hakan a wata ganawa da ta yi dashi. Yace Musamman Atiku Abubakar da Peter Obi idan suka hade kaga ana da jimullar kuri'u Miliyan 13 kenan inda shi kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke da kuri'u Miliyan 8. Yace a haka tun karfe dayan rana zasu kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ranar zabe.
Zamu daina baka makamai da yanke duk wata hulda da kai idan ka ci gaba da Kàshè Palasdiynawa>>Shugaba Trump ya gargadi Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu

Zamu daina baka makamai da yanke duk wata hulda da kai idan ka ci gaba da Kàshè Palasdiynawa>>Shugaba Trump ya gargadi Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu

Duk Labarai
Rahotanni daga fadar White House ta kasar Amurka na cewa, shugaban kasa, Donald Trump na ci gaba da matsawa Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu akan ya dakata da yakar Falasdinawa. Rahotan yace Shugaba Trump har ta kai ga ya gayawa Benjamin Netanyahu cewa ko dai ya daina wannan yaki ko su yanke duk wata hulda dashi. Benjamin Netanyahu dai ba zai so hakan ba saboda mafi yawa kasar Amurka ce ke sayar musu da makamai. Saidai a wata majiyar an ji cewa, Benjamin Netanyahu na fadar zasu ci gaba da yakin kuma zasu samu nasara ba tare da taimakon kasar Amurka ba. Hakanan a wani Rahoto me kama da wannan, kasashen Ingila, Faransa da Canada sun yi barazanar daukar kwakkwaran mataki muddin Israela bata dakata da sabbin munanan hare-haren da take kaiwa a Gaza ba da kuma janye hana ka...
Zamu ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya >>Matatar Dangote ta sha Alkawari

Zamu ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya >>Matatar Dangote ta sha Alkawari

Duk Labarai
Matatar man Dangin ta sha Alwashin ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya. Matatar tace tana ci gaba da rage farashin man ne saboda amincewa da ta rika sayen danyen man fetur din da kudin Naira. Tace tana godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya amince da yin hakan, kamar yanda wakilin matatar me suna Anthony Chiejina ya tabbatar. Matatar tace zata ci gaba da goyon bayan karfafa ci gaban tattalin arziki Najeriya da kuma tabbatar da saukin man fetur.
PDP ta koka da cewa, APC na ta mata kwacen mutanenta inda a yanzu haka Gwamnonin da suka rage ana musu Alkawari me gwabi idan suka shiga APC

PDP ta koka da cewa, APC na ta mata kwacen mutanenta inda a yanzu haka Gwamnonin da suka rage ana musu Alkawari me gwabi idan suka shiga APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar APC me mulki nawa gwamnonin PDP da tsaffin Gwamnonin jam'iyyar Alkawura masu gwabi idan suka yadda suka koma jam'iyyar. Rahotanni daga Punchng sun ce APC nawa Gwamnoni masu ci alkawarin za'a basu tikitin sake tsayawa takara idan suka yadda suka koma jam'iyyar ba tare da abokin takara ba, sannan kuma za'a basu dama su zabi wanda zai gajesu da wadanda zasu tsaya takarar 'yan majalisa. Sannan tsaffin Gwamnonin dake cikin PDP ana musu Alkawarin za'a basu mukaman Minitoci. Saidai Rahotan yace Atiku Abubakar yana jan hankalin su da cewa goyon bayan Tinubu kamar goyon bayan Rashin Nasara ne da Gwamnatin data gaza, inda yake jan hankalinsa da su goyi bayansa. Kakakin PDP, Debo Ologunagba ya koka da cewa, ana Amfani da Mulki wajan matsawa 'yan jam'...
An kara kama wani kasurgumin me Gàrkùwà da mutane a Filin jirgin Sokoto yana shirin zuwa Hajji

An kara kama wani kasurgumin me Gàrkùwà da mutane a Filin jirgin Sokoto yana shirin zuwa Hajji

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa, an kama wani Kasurgumin me Garkuwa da mutane a filin Jirgin jihar yana shirin zuwa aikin Hajji. Wanda aka kama din shine Sani Galadima a yayin fa yake daf da hawa Jirgi. An kamashi ne daidai wajan da ake tantance mutane. Rahoton yace hukumar 'yansandan farin kaya ce ta kamashi kuma za'a gurfanar dashi a kotu, da zarar an kammala bincike.