In ka cika Kwallon Shege ka fito mu yi dambe a bainar jama’a a ga wanene gwani ni da kai>>Oshiomhole ya gayawa Reuben Abati
Tsohon shugaban APC, kuma tsohon gwamnan jihar Edo wanda kuma tsohon shugaban kungiyar Kwadago ta NLC ne, watau Adams Oshiomhole ya nemi tsohon kakakin shugaban kasa, Reuben Abati da ya fito su daku idan ya isa.
Ya bayyana hakanne a ganawarsa da gidan Talabijin na Channels TV.
Yace hakane bayan da Abati a wata hira da aka yi dashi a Arise TV ya ce shin ko Ifeanyi Okowa ya tambayi Oshiomhole an yafe masa zunubansa kamin komawa APC?
A baya dai lokacin yana shugaban APC, Adams Oshiomhole ya taba cewa, duk laifin mutum idan ya shiga APC an yafe masa.
Saidai yanzu yace wannan magana da Abati yayi bata dace ba, shi a matsayinsa na Sanata menene hadinsa da binciken me laifi?
Sannan yace shin ko Abati yana jin haushin kamun da EFCC suka masa ne bayan saukar Jonathan daga Mulki, yac...








