Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci.
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage ranar yanke hukunci kan shahararriyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, har zuwa ranar 20 ga watan Mayu, bayan da masu gabatar da kara su ka nemi izini don gyara tuhumar da a ke yi mata.
Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Murja da tuhuma daya tak kan zargin cin zarafin Naira.
An ga Murja a wani faifen bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta tana watsar da kudi har Naira 400,000 tare da rawa a lokacin wani biki da aka gudanar a otal din Tahir Guest Palace a watan Disamba na shekarar 2024.
Tuni dai wanda ake tuhumar ta amsa laifin da ake zarginta da shi.
A zaman kotun na ranar Talata da aka tsara domin yanke hukunci, lauyan EFCC...
Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na'ura.
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta amince da kuskuren na'ura da ya kawo cikas ga sahihancin sakamakon jarabawar da aka yi ta bana a cibiyoyi 157 a fadin kasar nan.
Shugaban hukumar ta JAMB, Ishaq Oloyede, yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Laraba, ya ce sakamakon ɗalibai 379,997 abin ya shafa.
Ya ce hukumar ta gano matsalolin a cibiyar a Legas da Owerri, wanda hakan ya sa aka kasa dora amsoshin ɗaliban da abin ya shafa a kwanaki ukun farko na jarabawar.
Oloyede ya ce ba gano matsalar da daya daga cikin kamfanonin da ke bada na'urar yin jarrabawar ya haifar ba kafin a fitar da sakamakon.
Ya ce cibiyoyi 65 a Legas ɗalibai...
Gwamnatin Birtaniya ta ce matakan da shugaban Najeriya bola Ahmed Tinubu ke ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar kwalliya na biyan kuɗin sabulu.
Birtaniyan ta ce matakan da aka ɗauka musamman wajen farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, da na kuɗin shiga na daga cikin dalilan da suka aka samu ƙaruwar damar zuba jari a ƙasar.
Jakadan Birtaniya a Najeriya Dr. Richard Montgomery ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin Najeirya da Birtaniya, ta fuskar kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, da ya gudana a Abuja babban birnin na Najeriya.
Gwamnatin Birtaniyar ta ce la’akari da rahoton da Bankin Duniya a baya-bayan nan kan harkokin zuba jari a Najeriya ya nuna cewar darajar kuɗin ƙasar naira na farfaɗowa.
Haka kuma rahoton ya ce ana sam...
Sanatocin Najeriya uku da suka fito daga jihar Kebbi, waɗanda suka sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki sun ce sun fita daga jam'iyyar ce sanadiyyar rikice-rikice na cikin gida.
A jiya Talata ne shugabancin majalisar dattajai ya tabbatar da sauya shekar sanatocin wato Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya da Yahaya Abdullahi mai wakilartar Kebbi arewa da kuma Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta kudu.
Sanatocin sun ce sun fice daga jam'iyyar ne saboda rikice rikicen cikin gida da suka yi wa jam'iyyar PDP katutu.
Daya daga cikinsu, Sanata Yahaya Abdullahi ya shaida wa BBC cewa a bayyane take tun bayan zaɓen 2023, jam'iyyar PDP ta shiga ruɗani da rikici kala-kala, kuma har kawo yanzu babu alamun jam'iyyar tana ɗaukar matakin gyara matsalolin n...
Wata kungiya me saka ido kan ayyukan masu ikirarin Jìhàdì me suna Nextier SPD ta bayyana cewa sojojin Najeriya 100 ne da farar hula 200 aka kashe a hare-haren masu ikirarin Jìhàdì cikin makonni 5 da suka gabata.
Kungiyar a sabon rahoton data wallafa tace akwai bukatar a sake duba ga tsarin yakar ta'addanci a Najeriya da ake dashi a yanzu.
Rahoton kungiyar yace an kai hare-hare 252 na ta'addanci a cikin watanni 6 da suka gabata sannan kungiyoyin B0K0 Hàràm da ÌŚWÀP sun kwace kananan hukumomi 3 a jihar Borno.
Kungiyar ta yi gargadin cewa ana samun karin sanyin gwiwa a tsakanin sojoji hakanan alaka tsakanin jama'ar gari da sojoji na kara yin tsami, sannan kuma hakan na nufin lamarin na iya kara kazancewa nan gaba.
Kungiyar tace rashin samun ilimi da rashin aikin yi tsakanin matas...
Mayaƙan IS sun ƙara kai wa sojojin Najeriya hari, karo na biyu a cikin kwanaki biyu.
Rundunar sojin Najeriya ta ce maharan sun kashe dakarunta huɗu a wani sansanin su da ke kusa da garin Rann da ke kan iyakar ƙasar da Kamaru a ihar Borno.
A ranar Litinin ma IS ta kai hari a wani sansanin soji da ke yammacin Borno, a garin Marte, inda aka bayar da rahoton kisan sojojin Najeriya da dama.
Masu sharhi sun ce a baya bayan nan mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun canza salon kai hare-hare, ciki harda amfani da jirgin sama marar matuƙi.
Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka mai neman tabbatar da tsarin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya.
Wannan na daga cikin aikin da majalisar ke yi na gyaran wasu sassa shida na kundin mulkin ƙasar, waɗanda a baya suka gaza tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.
Zaman majalisar na ranar Talata wanda shugabanta Abbas Tajudeen ya jagoranta ya yi muhawara a kan ƙudirin sannan ya cimma matsayar yin watsi dashi kamar yadda ya yi wa sauran ƙudirorin da aka gabatar da su tare.
Sai dai ana sa ran batun zai ƙara tasowa a zaman majalisar wakilan na yau Laraba domin sake tafka muhawa da ɗaukar matsaya a kai.
Wasu daga cikin ƴan majalisar da suka yi muhawara a kan ƙudirin sun ce a yanzu haka jam'iyyun siyasar Najeriya suna da irin nasu tanadi na tantance karɓa-karɓan shu...
Rundunar soji ta Operation Hadin Kai ta koka da yanda tace masu ikirarin Jihadi na Kungiyar B0k0 Hàràm na amfani da jirage marasa matuka dan kai musu hari.
Rundunar tace irin wannan hare-haren na da wahalar ganowa da dakilewa musamman ta hanyar amfani da hanyoyin da aka saba wadanda ba na zamani ba.
Shugaban Rundunar, Major General Abdulsalam Abubakar ne ya bayyana hakan a wajan wani taro a Maiduguri.
Yace wasu daga cikin jiragen marasa matuka da kungiyar ke amfani dasu na kama da irin wadanda ake amfani dasu a kasashen Israela da Ukraine.
Dan haka ya jawo hankalin sauran 'yan kungiyar dasu tuba su mika kansu ga jami'an tsaro kamar yanda 'yan uwansu ke yi kuma ana karbar su tare da cin zarafi ba.
Saidai yayi gargadin wadanda suka ki amincewa su mika kansu, zasu fuskanci ki...
Hukumar 'yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Bidiyon da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga jirgin samansu yana sauka da tashi a tsakanin wasu masu rike da makamai.
An yi zargin cewa jirgin ya je kaiwa 'yan Bindiga kayan abinci da sauran kayan aiki ne.
Saidai a sanarwar da ta fitar ta shafinta na sada zumunta, Hukumar 'yansandan tace ba 'yan Bindiga bane aka gani a cikin Bidiyon ba. 'Yansanda ne dake aikin samar da tsaro a dajin Obajana na jihar Kogi.
Hukumar tace a daina dogaro da bayanan da basu fito daga bakin hukumomin tsaro ba dan gujema labarin karya.