Friday, December 19
Shadow
Gwamnatin Tarayya ta dauki manyan Lauyoyi dan karawa da Gwamnonin PDP a kotu game da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers

Gwamnatin Tarayya ta dauki manyan Lauyoyi dan karawa da Gwamnonin PDP a kotu game da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta dauki manyan lauyoyi ciki hadda tsohon ministan shari'a kuma babban lauyan Gwamnati, Chief Akin Olujinmi (SAN) dan su kareta game da karar da Gwamnonin PDP 11 suka shigar da ita suna kalubalantar dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Sauran lauyiyin da gwamnatin tarayya ta dauka sun hada da Prof Kanyinsola Ajayi, Jelili Owonikoko, Kehinde Ogunwumiju, Tijani Gazali, Babatunde Obama , Olawale Fapohunda, Olumide Olujinmi, Akinyemi Olujinmi da Ademola Abimbola. Sauran sune, Akinsola Olujinmi, Oluwole Ilori, Abdulwahab Abayomi, Mojeed Balogun, Jideuche Ezi sai Ramat Tijani. Gwamnonin jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa ne suka shigar da gwamnatin kara s...
Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da ‘yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da ‘yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Duk Labarai
Matatar fetur ta Dangote ta nanata cewa, tana samar da isashshen man fetur din dake iya wadatar da Najeriya. Hakan na zuwane bayan da 'yan kasuwa masu Depot din sayar da man fetur din suka ce sune ke wadatar da sauran sassan Najeriya dan har yanzu Matatar man ta Dangote bata iya wadatar da dukan Najeriya da man fetur din da take da dashi. Shugaban 'yan kasuwar, Olufemi Adewole ne ya bayyana hakan inda yace duk da yawan man fetur din da 'yan Najeriya ke sha ya ragu, har a haka ma Matatar ta Dangote bata iya wadatar da Dukan Najeriya da mai. Yace sune ke kokarin yin hakan. A bangare guda kuma, Wata majiya daga matatar man fetur din ta Dangote ta bayyanawa kafar Punchng cewa, Matatar tasu na wadatar da Najeriya har ma ta fitar da Man fetur din zuwa kasashen waje.
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na PDP dan shawo kan matsalar masu ficewa daga jam’iyyar zuwa APC, kuma Wike ma ya halarci wajan

An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na PDP dan shawo kan matsalar masu ficewa daga jam’iyyar zuwa APC, kuma Wike ma ya halarci wajan

Duk Labarai
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Abuja. An gudanar da taronne a gidan Gwamnatin jihar Bauchi dake Asokoro A Abuja. Manyan 'yan jam'iyyar da yawa da suka hada da Ahmad Makarfi, Seriake Dickson, Gwamna Bala Muhammad, Gwamna Agbu Kefas, Gwamna Ahmadu Fintiri, Gwamna Dauda Lawal Dare, Gwamna Ademola Adeleke, Gwamna Caleb Muftwang, Da Dai Sauransu. Wani abin ba zata shine, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ma ya halarci taron
Ban damu sai na koma Kujerar Gwamna ko ta halin kaka ba>>Gwamnan Jihar Rivers Simi Fubara

Ban damu sai na koma Kujerar Gwamna ko ta halin kaka ba>>Gwamnan Jihar Rivers Simi Fubara

Duk Labarai
Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya bayyana cewa, bai damu sai ya koma mukaminsa na gwamna ba ko ta halin kaka. Ya bayyana hakanne a wajan wani taron tunawa da dattijon jihar, Marigayi, Edwin Clark, inda masu jawabi da yawa da auka tashi suka soki dakatar dashi da aka yi da neman a mayar dashi kujerar Gwamna. Fubara da ya hau wajan jawabi ya nesanta kansa da kalaman mutanen inda yace bai kamata a yi fito na fito kan lamarin ba. Ya kara da cewa, suka san ko yana son komawa Kujerar gwamnan? Yace shi a yanzu ma ruhinsa ya bar gidan Gwamnatin jihar.
Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya bùgà masa a ka Ya ràsù a Kano

Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya bùgà masa a ka Ya ràsù a Kano

Duk Labarai
Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya buga masa a ka Ya rasu. Cikin wani sako da mai magana da yawun randunar SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa yace “Matashi yaje zance wajen budurwa, yayanta ya fito da gora ya buga masa a ka. Ya rasu, shi kuma yana hannun Yan Sanda. Daga karshe Kiyawa yace nan gaba kadan zasu fitar da cikakken bayani.
Zan halarci taro kan tsaro da majalisa ta Shirya>>Ministan Tsaro Badaru

Zan halarci taro kan tsaro da majalisa ta Shirya>>Ministan Tsaro Badaru

Duk Labarai
Ministan tsaro, Muhammadu Badaru ya bayyana cewa, zai halarci taron tsaro da majalisa ta shirya. Ya bayyana hakane a ranar Lahadi ga manema labarai. Badaru a baya yace canja tsarin tsaro ne zai fi kawo ci gaban matsalar tsaro a taron ba. Saidai a yanzu yace shawarwarin da za'a bayar a wajan taron zasu taimaka wajan aiwatar dasu a aikata dan kawar da matsalar tsaron.