Za mu koma aikin haƙo ɗanyen mai a arewacin Najeriya – NNPCL
Shekara biyu bayan ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a iyakar jihohin Bauchi da Gombe - wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba - a yanzu sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya Bayo Ojulari ya fada wa BBC cewa za a koma kan aikin.
Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al’ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren.
Tun a jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan shan rantsuwar kama mulki ne ...








