Thursday, December 18
Shadow
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Duk Labarai
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da Honorable Salisu Yusuf Majigiri na mazaɓar Mashi/Dutsi, Honorable Aliyu Iliyasu na mazaɓar Batsari/Safana/Danmusa, Honorable Abdullahi Balarabe Dabai na mazaɓar Bakori/Danja. Dukkan su sun bayyana rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a matsayin dalilin sauya shekar ta su.
Akpabio ya kai Sanata Natasha Akpoti kara kotu kan takardar Hakuri da shagube data yi masa, Yace yana son Kotu ta sa Natasha ta goge Wasikar a shafinta na sada zumunta sannan ta bashi Hakuri

Akpabio ya kai Sanata Natasha Akpoti kara kotu kan takardar Hakuri da shagube data yi masa, Yace yana son Kotu ta sa Natasha ta goge Wasikar a shafinta na sada zumunta sannan ta bashi Hakuri

Duk Labarai
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu, yana zargin ta da wallafa kalaman ɓatanci a cikin wata wasikar bada haƙuri da aka danganta da ita — Wasikar da ke ɗauke da wata magana mai cin mutunci da ke cewa “ta yi kuskuren tunanin cewa kujerarta a Majalisa ta samu ta hanyar zaɓe, ba ta hanyar jima’i ba.” Rahotanni sun bayyana cewa wannan ƙara ta samo asali ne daga wata wallafa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da Sanata Natasha, inda ta nemi gafara daga Shugaban Majalisar bisa wasu maganganu da ake cewa ta furta a baya. A cikin wannan wasikar, an ambaci cewa ta “yi kuskuren ɗauka cewa ta samu kujera ne ta hanyar sahihin zaɓe.” Lauyoyin Akpabio sun ce wannan magana ta wallafa ra’ayi mai matuƙar cin mutunci da b...
Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye. Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba. Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin. Ambasada Nuhu ya ce "hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al'umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma", in ji shi. "...
An sami rashin fahimta tsakanin ƴan majalisa da ministan tsaron Najeriya kan tsaro

An sami rashin fahimta tsakanin ƴan majalisa da ministan tsaron Najeriya kan tsaro

Duk Labarai
Ministan tsaron Najeriya, Mohamamd Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba, da majalsair dattawwan ƙasar ta nemi a yi ba. Haka kuma ya musanta zargin da majalisar wakilan ƙasar ta yi na cewar ƴan bindigar na amfani da makaman da suka fi na jam'an tsaron ƙasar. A ranar Talata ne dai majalisar dattawan Najeriya suka buƙaci da a shirya wani taro kan harkokin tsaro, don samar da hanyoyin magance matsalar. Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na ministoci da ya gudana a jihar Laraba ministan tsaron na Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya ce sakae dabarun yaƙi da mastaalr tsaro ya kamata a yi ba wai taro ba a halin da ake ciki a ƙasar. "Idan ka yi taron ƙasa kan tsaro, mutane za su zo, su fadi abin da suke so, mu ...
Mayar da Najeriya tsarin Jam’iyya daya na da hadari>>Goodluck Jonathan

Mayar da Najeriya tsarin Jam’iyya daya na da hadari>>Goodluck Jonathan

Duk Labarai
Bayan tsawon lokaci ba a ji ta bakinsa ba dangane da faruwar al'amuran siyasa, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ɓara inda ya yi gargaɗin cewa "abu ne mai haɗari ɗora Najeriya a kan turbar jam'iyya guda ɗaya". Ba kasafai dai ake jin bakin Goodluck Jonathan ba a al'amura kasancewarsa mutum mai kawaici da rashin son yawan magana. To sai dai a ranar Larabar nan, tsohon shugaban na Najeriya yayin wata lacca da aka shirya a Abuja domin tuna wa da marigayi Edwin Clerk, dattijo ɗan ƙabilar Ijaw wanda ya rasu yana da shekara 97, Jonathan ya ja hankalin gwamnati da jam'iyya mai mulki ta APC da ake zargi da mayar da ƙasar ƙarƙashin tsarin jam'iyya guda. Kalaman Goodluck Jonathan Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ce duk wnai yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam'i...
Gwamnatin Kano ta dakatar da watsa shirye shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai dake jihar. Hakan na zuwa ne domin tantance da kuma tsabtace kalamai da yan siyasa ke yi a kafar sadarwa na radiyo da talabijin

Gwamnatin Kano ta dakatar da watsa shirye shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai dake jihar. Hakan na zuwa ne domin tantance da kuma tsabtace kalamai da yan siyasa ke yi a kafar sadarwa na radiyo da talabijin

Duk Labarai
Gwamnatin Kano Ta Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye a Kafafen Watsa Labarai Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dakatarwa nan take ga dukkan shirye-shiryen siyasa da ake yadawa kai tsaye a kafafen watsa labarai na jihar. An bayyana wannan mataki ne yayin taron tattaunawa na kowane lokaci da ake gudanarwa a Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, wanda Kwamishinan Yada Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranta tare da shugabannin kafafen yada labarai. A cewar wata sanarwa da Daraktan Harkokin Musamman na ma’aikatar, Sani Abba Yola, ya sanyawa hannu, an dauki wannan mataki ne don dakile yada kalaman da za su iya haifar da fitina da barazana ga zaman lafiya da daidaiton al’adu da addini a jihar. “Ba mu dauki wannan mataki don murkushe ‘yan adawa ba,” in ji ...
Matata tace Na burgeta kuma zan yi kyau da Fafaroma shiyasa na watsawa Duniya ta gani>>Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi karin bayanin dalilin da yasa ya wallafa hotonsa da kayan Fafaroma

Matata tace Na burgeta kuma zan yi kyau da Fafaroma shiyasa na watsawa Duniya ta gani>>Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi karin bayanin dalilin da yasa ya wallafa hotonsa da kayan Fafaroma

Duk Labarai
Bayan da cece-kuce yayi yawa akan hoton da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya wallafa yana sanye da kayn Fafaroma, ya fito yayi karin bayani. Shugaba Trump yace Kamin ya dora hoton a shafinsa na Sada zumunta sai daya nunawa matarsa kuma ta amince dashi cewa yayi kya. Yace dan haka yayi amannar kasancewar matarsa 'yar Darikar Katolika, to yasa sauran ma 'yan darikar zasu so hoton. A baya dai da aka Tambayeshi wa yafi cancanta ya zama Fafaroma, sai yace shine.
Bayan da ta zargeni da nemanta da lalata Har Hotunan Selfie Sanata Natasha Akpoti ke daukar mu ni da ita idan mun tafi aiki, saboda tsabar jin dadin aiki dani kuma nace ta kawo hujjar zargin da take min amma taki

Bayan da ta zargeni da nemanta da lalata Har Hotunan Selfie Sanata Natasha Akpoti ke daukar mu ni da ita idan mun tafi aiki, saboda tsabar jin dadin aiki dani kuma nace ta kawo hujjar zargin da take min amma taki

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Abin mamaki bayan da sanata Natasha Akpoti ta zargeshi da cewa ya nemeta da lalata, sun yi tafiye-tafiye tare har zuwa kasashen waje aiki. Yace kuma har hotuna Selfie take daukarsu idan suna aiki saboda jin dadin aiki dashi. Yace amma kuma ya nemi ta gabatar da hujjar zargin da take masa amma taki. Sanata Natasha Akpoti dai tace ba zata bayar da hujjojin zargin da takewa, Sanata Godswill Akpabio ba sai an je kotu.