Zargin Biliyan biyu ga Kwankwaso: Babu hankali da lissafi a maganar Baffa Bichi – Abba Gida-Gida
Zargin Biliyan biyu ga Kwankwaso: Babu hankali da lissafi a maganar Baffa Bichi - Abba Gida-Gida.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Baffa Bichi martani bisa zarge-zargen da ya fada akan gwamnatin.
A wata hira da manema labarai da ta karade kafafen watsa labarai, an jiyo Baffa Bichi, wanda aka cire shi daga muƙamin sakataren gwamnatin, na cewa an ɗauki matakin ne don ya ki amincewa da ya sahale a rika diban Naira biliyan 2 duk wata ana saka wa a asusun Rabi'u Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya.
A wani taro da kansilolin mazaɓu 484 na jihar a yau Lahadi, gwamna Abba ya ce maganganun da Bichi ya yi "babu hankali da lissafi da aiki da ƙwaƙwalwa a wannan maganar."
A cewar gwamna Abba, babu hankali a ce gwamnatin sa da ko shekaru bi...








