Ƴan Sa Kai 11 Sun Rasa Rayukansu a Sokoto Bayan Artabu da Ƴan Bindiga
Aƙalla ‘yan sa-kai 11 ne aka tabbatar sun mutu, wasu da dama kuma ba'a san inda suke ba, bayan wani mummunan artabu da suka yi da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Tangaza da ke Jihar Sokoto.Rikicin ya fara ne tun ranar Juma’a, inda aka samu rahoton mutuwar mutane biyu, amma daga bisani aka ƙara gano gawawwaki tara a dajin Lakurawa. Har yanzu ana ci gaba da neman wasu da ba a san inda suke ba, tare da taimakon sojoji da jami’an tsaro daga Binji da Racca.Shaidun gani da ido sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan da ‘yan sa-kai suka hana wani hari a kauyen Magonho, lamarin da ya janyo musayar wuta mai tsanani.Ƴan bindigar, wadanda yawansu ya kai 40, sun zo ne akan babura guda 20 dauke da ma...