Atiku da Peter Obi zasu hada kai domin kayar da Tinubu a zabe mai zuwa-Makusancin Atiku.
Dama dai akwai Rahotannin dake ta yawo cewa ana ta kokarin hada kai tsakanin 'yan Adawa.
Ana zargin Seyi Tinubu, shugaban NTA da kuma ministan matasa ne suka yi garkuwa da shugaban daliban Najeriya na NANS suka sa aka bashi kashi saboda yaki karbar cin hancin miliyan 100 ya koma APC, yace APC bata yi abin azo a gani ba da zai sa ya mara mata baya.
Duka dai akan Wannan Labarin:
Tsohon gwamnan Kaduna, El Rufa'i ya bukaci kungiyar kare hakkin bil'adama dasu biwa shuhaban daliban Najeriya na NANs hakkinsa, domin ana zargin su Seyi Tinubu nada sa hannu a dukan da aka masa.
A yau ne ake sa ran hukumomin kasar Amurka na FBI zasu saki bayanai akan zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da safarar miyagun kwayoyi a Birnin Chicago na kasar.
Ana zargin Tinubu da asu mutane 3 Lee Andrew Edwards, Mueez Akande, da Abiodun Agbele a shekarun 1990 sun yi safarar miyagun Kwayoyi wanda shari'ar take kan Gudana.
Lauyoyi da musamman 'yan Adawar shugaban kasar na neman a saki bayanai game da wannan binciken dan a san wanene shugaban kasar.
A baya ba'a samu hadin kan hukumomin kasar Amurkar ba game da sakin bayanan, amma a yanzu sun amince kuma a yau, Juma'a ne ake sa ran sakin wadannan bayanan.
Saidai fadar shugaban kasa ta bakin me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga tace tabbas lauyoyi na kan binciken wannan magana.
Saidai fadar tace bayanan ko da ...
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya ƙaryata rade-radin da ake cewa su na zaman doya da manja da mataimakin sa, Yakubu Garba.
Bago ya tabbatar da cewa lafiya lau ya ke zaune da mataimakin na sa.
"Ba wanda zai iya raba ni da mataimaki na. Mu na zaman lafiya kuma mu na aiki tare lafiya. Dukkan mu kuma mu na kokarin wanzar da zaman lafiya a tsakanin mu," in ji Bago.
'Yan Bindiga dake garkuwa da mutane dan neman kudin fansa sun fito da wata sabuwar azabtar da mutanen sa suka yi garkuwa dasu.
A yanzu an fara ganin 'yan Bindigar na yankewa mutane hannu su sakosu idan ba'a kai musu kudin fansa ba.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Yagba West dake jihar Kogi.
Mutane 3 suka yiwa wannan azaba.
Gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa Najeriya ce ta hudu a bayan kasashen India, China da Saudi Arabia wajan saurin habakar tattalin Arziki.
Saidai an gano wannan ikirarin ba gaskiya bane.
Gwamnatin Ta yi ikirarin cewa wannan bayanai sun fito ne daga hukumar bayar da lamuni ta Duniya IMF.
Saidai bincike ya bayyana cewa Najeriya ta 37 ce ba ta 4 ba a jerin kasashen masu saurin habakar tattalin arziki.
Kungiyar Tuntuba ta Arewa me suna ACF ta bayyana cewa, abin takaici ne ya da 'yan Arewa a kudancin Najeriya ba'a sayar musu da gidaje da Filaye.
Amma nan a Arewa 'yan kudu na ta mallakar gidaje da filaye.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu ne yayi wannan kirafi inda yace ya kamata a jihohi 19 na Arewa a fito da sabon tsarin mallakar fili da gida dan magance wannan matsala.
Yace musamman a jihohin Inyamurai basa sayarwa da 'yan Arewa fili.
Yace idan ba'a tashi tsaye aka magance wannan matsala ba, muna ji muna gani zamu sama bamu da fili ko gida a garuruwan mu duk baki sun saye.
Shugaban Kungiyoyin gwagwarmaya da suka hada kai suka kai bukatar a binciki tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya je ya janye bukatar binciken.
Kungiyoyin sun ce basa tare da shugaban nasu me suna Kabir Matazu.
A wata sanarwa da sakataren kungiyoyin me suna Moses Okino ya fitar, yace Matazu ya yaudaresu da cin amanarsu.
Kungiyar tace dama can akwai wasu na hannun damar Mele Kolo Kyari dake ta son su hana binciken me gidan nasu.
Yace dan haka abinda Matazu yayi ba da yawun kungiya yayi ba yayi ne shi kadai bisa radin kansa.
Yace Matazu bai tuntubesu ba dan haka suna kyautata zaton kudi aka bashi.
Babban Malamin Darika dake daukar hankula a kafafen sada zumunta, Attalili Attagazuti ya bayyana sunayen Annabawa da ba'a taba jinsu ba.
https://twitter.com/northern_blog/status/1917708087135264816?t=f7ssui8vGrqUErhMI6dhMA&s=19
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya yadu sosai inda mutane sukai ta mamakin lamarin.
A ranar Litinin ɗin nan ne gwamnonin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya suke taro a birnin Damaturu babban birnin Jihar Yobe kan matsalolin da yankin ke fama da su.
Taron na zuwa a daidai lokacin da yankin ke fama da sabin hare-haren mayakan Boko Haram.
Masana da al'ummar yankin na cewa dama ce gwamnonin suka samu domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
A ranar Talata ne dai ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai wani harin bam da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 26 a Rann a jihar Borno.