Saturday, December 13
Shadow
Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Duk Labarai
Wani yaro dan shekara 11 mai suna Joshua Samson ya mutu bayan ya fado daga bishiyar mangwaro a kauyen Bugakwo da ke karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin Bugakwo mai suna Danjuma, ya shaidawa DAILY TRUST cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, a lokacin da marigayin ya hau bishiyar mangwaro don ya tsinka. Ya ce yaron ya hau bishiyar mangwaron ne domin ya tsinko mangwaro, amma sai ya zame daga kan reshen ya fado kasa. Ya ce daya daga cikin yaran da suka je diban mangwaron ne ya ruga gida yana kuka ya kai rahoto ga iyayen marigayin, inda suka garzaya da shi asibiti. Ya ce yaron ya mutu ne bayan kansa ya bugu a kan dutse a karkashin bishiyar mangwaron, inda ya ce an binne yaron. “Ma’aikatan lafiya a cibiyar lafiya ta Kwaku sun tabbatar da mutuwarsa s...
Kada ku bai wa ƴansanda bashin da ba za su iya biya ba, IG ya shawarci ƴan Nijeriya

Kada ku bai wa ƴansanda bashin da ba za su iya biya ba, IG ya shawarci ƴan Nijeriya

Duk Labarai
Sufeto Janar na Ƴansanda, Dr. Kayode Egbetokun, ya shawarci al’ummomin da jami’an tsaro ke aiki a yankunan su da su daina ba su rancen manyan kudade waɗanda za su wahala wajen biya. IG ɗin, wanda Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kogi, Miller Dantawaye, ya wakilta, ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin bikin ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ‘yansanda a gundumar Imane, karamar hukumar Olamaboro ta jihar. “Bari in ja kunnen al’ummar yankin cewa yayin da suke mu’amala da jami’an da za a turo musu, wasu daga cikinsu za su nemi taimakon kuɗi da rance, amma kada ku ba su rance mai yawa da za su gagara biya,” in ji Dantawaye. Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su kula da sabon ofishin ‘yan sanda, wanda shine irinsa na farko a yankin, wanda wani ɗan asalin yankin, Dr. Peter Ali, ya gina kum...
‘Yan Bindiga sun shiga uku, An kai jami’an ‘yansanda na musamman da suka kware da yaki da ‘yan Bìndìgà a kowace jiha a kasarnan>>IGP

‘Yan Bindiga sun shiga uku, An kai jami’an ‘yansanda na musamman da suka kware da yaki da ‘yan Bìndìgà a kowace jiha a kasarnan>>IGP

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya kai 'yansanda na musamman duka jihohin Najeriya dan su yaki 'yan Bindigar da ake fama dasu. Ya bayar da umarnin cewa kwamandojin 'yansanda na Squadron da su shirya runduna ta musamman ta 'yansanda na karta kwana wanda da an bukacesu a kowane lokaci zasu iya kai dauki. Ya bayar da umarnin ne a zaman ganawa da kwamandojin ranar Talata biyo bayan hare-haren da 'yan Bindiga suka kai jihohin Kwara, Benue da Sokoto suka kashe mutane 21. Hakanan an samu kazaman hare-hare a jihohin Borno, Enugu da Filato.
Ya kamata ‘yan Najeriya su rima godewa kokarin da muke domin ita matsalar tsaro ba’a magance ta a rana daya>>Inji Me baiwa shugaban kasa shawara kan matsalar tsaro, Nuhu Ribadu

Ya kamata ‘yan Najeriya su rima godewa kokarin da muke domin ita matsalar tsaro ba’a magance ta a rana daya>>Inji Me baiwa shugaban kasa shawara kan matsalar tsaro, Nuhu Ribadu

Duk Labarai
Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu yayi kira ga 'yan Najeriya da su rika godewa gwamnati kan kokarin da take dan magance matsalar. Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakanne a wata ganawa da yayi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Benue a ziyarar da ya kai jihar. Yace idana aka kalli kasashe irin su Sudan zaka ga basu da gwamnati, hakanan kasashe irin su Afghanistan inda yace ya taba yin aiki a can suma wadanda Duniya ta taru dan ta yakesu sune a yanzu suke mulkar kasar. Yace kasashe Irin su Burkina Faso da Nijar da Mali yanzu sojoji ne ke mulki yace dan haka matsalar tsaro ba matsala bace da za'a ce a magance ta a rana daya. Yace ya kamata 'yan Najeriya su rika godiya su san cewa akwai wadanda ke aiki tukuru dan samar da tsaro a kasarna...
Innalillahi Wa inna Ilaihi Raji’un: Kalli Yanda shafin Ma’aikatar Harkokin cikin Gida ta Najeriya suka wallafa Bidiyon bàtsà, watau Blù fìm

Innalillahi Wa inna Ilaihi Raji’un: Kalli Yanda shafin Ma’aikatar Harkokin cikin Gida ta Najeriya suka wallafa Bidiyon bàtsà, watau Blù fìm

Duk Labarai
Shafin ma'aikatar harkokin cikin gida na Najeriya a dandalin X sun wallafa Bidiyon batsa wanda aka fi sani da Blùè Fìm. Abin ya zowa mutane da mamaki ganin cewa shafine na gwamnati. Saidai wasu sun ce me kula da shafinne ya manta bai canja shafinba ya ke ya wallafa wannan abin Kunya. Lamarin dai ya jawo cece-kuce da Allah wai da shagube.
Gwamnatin Tinubu ta zo ta binne ‘yan Najeriya ne bayan da Buhari ya kashe mu>>Inji Sowore

Gwamnatin Tinubu ta zo ta binne ‘yan Najeriya ne bayan da Buhari ya kashe mu>>Inji Sowore

Duk Labarai
Dan fafutuka kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya bayyana cewa Gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ta kashe 'yan Najeriya ne inda ita kuma gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta zo ta binnemu. Sowore ya bayyan hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Symfoni yacm soki gwamnatin Najeriya sabosa hanyar data dauka. Yace kuma abin takaici shine yanda wasu ke goyon bayansu. Yace irin su El-Rufai basu ne ya kamata ace suna nemarwa talaka hakkinsa ba, yace mayunwata ne, suna samun abinda suke so zasu koma inda suka fito. Yace duk a gidan yari ya kamata a sakasu a kulle saboda tsaffin ma'aikatan gwamnatin Buhari ne. Yace amma idan 'yan Najeriya suka sha wuyar da ba zasu iya jurewa ba, da kansu zasu fito su yi zanga-zangar juyin juya hali.
Da Kuke ta sukar mu dan munce za’a saka Solar a fadar shugaba Tinubu, To Fadar White House ma ta shugaban kasar Amurka da Solar take amfani>>Inji Fadar Shugaban kasa Bola Tinubu

Da Kuke ta sukar mu dan munce za’a saka Solar a fadar shugaba Tinubu, To Fadar White House ma ta shugaban kasar Amurka da Solar take amfani>>Inji Fadar Shugaban kasa Bola Tinubu

Duk Labarai
Kakakin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Bayo Onanuga ya kare maganar ware Naira Biliyan 10 dan samar da wuta ta hanyar amfani da hasken rana a fadar shugaban kasa dake Abuja. A sanarwar da ya fitar, Bayo Ya bayyana cewa ba Gwamnatin Najeriya bace ka dai ta dauki wannan mataki ba, hadda gwamnatin kasar Amurka. Yace fadar White House ta kasar Amurka ma da wutar Solar watau Hasken Rana take amfani. Ya bayyana hakanne bayan da sanarwar ware Naira Biliyan 10 dan saka Solar a fadar shugaban kasa ya jawo cece-kuce.
Shugaba Tinubu da dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara sun gana a Landan

Shugaba Tinubu da dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara sun gana a Landan

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da dakataccen Gwannan jihar Rivers, Simi Fubara sun gana a jihar Landan. Rahoton yace sun yi ganawar ne dan samo hanyar da za'a samu zaman lafiya a jihar ta Rivers. Wannan ne karon farko da aka yi ganawa tsakanin Gwamnan jihar Rivers din da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tun bayan da ya dakatar dashi ya saka dokar ta baci a jihar. Wani hadimin shugaba Tinubu ne ya bayyana hakan. Saidai ganawar an yi tane ba tare da tsohon Gwamnan jihar Rivers ba watau Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike. Ana tsammanin dai shugaba Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki na jihar Rivers nan gaba.
Kasar Amurka zata fara biyan mata dala Dubu biyar sama da Naira Miliyan 7 idan suka yadda su haihu sannan duk wadda ta yadda ta haifi ‘ya’ya 6 za’a bata lambar yabo

Kasar Amurka zata fara biyan mata dala Dubu biyar sama da Naira Miliyan 7 idan suka yadda su haihu sannan duk wadda ta yadda ta haifi ‘ya’ya 6 za’a bata lambar yabo

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasar Amurka, Donald Trump ta fito da sabon tsarin karfafa mata su rika haihuwa dan kara yawan mutane a kasar. Rahoton yace duk macen da ta yadda zata haihu za'a bata Dala dubu 5, kwatankwacin sama da Naira Miliyan 7 kenan a kudin Najeriya. Hakanan duk macen da ta yadda ta haifi 'ya'ya sama da 6 za'a bata lambar girmamawa ta musamman.
An koya min Darasi: Wasu abokaina sun daina daukar wayata idan na kirasu saboda na yi ritaya>>Muhammad Zakari ya koka

An koya min Darasi: Wasu abokaina sun daina daukar wayata idan na kirasu saboda na yi ritaya>>Muhammad Zakari ya koka

Duk Labarai
Wani tsohon Ma'aikacin Gwamnati me suna Muhammad Zakari ya koka da cewa, wasu abokai sun yadashi basu ma daukar wayarsa shekara daya bayan da ya ajiye aiki. Yace ya fuskanci kalubale da yawa bayan ajiye aikin kuma wannan na daya daga cikinsu. Saidai yace hakan ya koya masa darasin cewa Yana da kyau mutum ya kulla alaka da mutane ba na wajan aikinsa kadai ba. Muhammad Zakari ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook.