Sunday, December 14
Shadow
Kasar Amurka zata fara biyan mata dala Dubu biyar sama da Naira Miliyan 7 idan suka yadda su haihu sannan duk wadda ta yadda ta haifi ‘ya’ya 6 za’a bata lambar yabo

Kasar Amurka zata fara biyan mata dala Dubu biyar sama da Naira Miliyan 7 idan suka yadda su haihu sannan duk wadda ta yadda ta haifi ‘ya’ya 6 za’a bata lambar yabo

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasar Amurka, Donald Trump ta fito da sabon tsarin karfafa mata su rika haihuwa dan kara yawan mutane a kasar. Rahoton yace duk macen da ta yadda zata haihu za'a bata Dala dubu 5, kwatankwacin sama da Naira Miliyan 7 kenan a kudin Najeriya. Hakanan duk macen da ta yadda ta haifi 'ya'ya sama da 6 za'a bata lambar girmamawa ta musamman.
An koya min Darasi: Wasu abokaina sun daina daukar wayata idan na kirasu saboda na yi ritaya>>Muhammad Zakari ya koka

An koya min Darasi: Wasu abokaina sun daina daukar wayata idan na kirasu saboda na yi ritaya>>Muhammad Zakari ya koka

Duk Labarai
Wani tsohon Ma'aikacin Gwamnati me suna Muhammad Zakari ya koka da cewa, wasu abokai sun yadashi basu ma daukar wayarsa shekara daya bayan da ya ajiye aiki. Yace ya fuskanci kalubale da yawa bayan ajiye aikin kuma wannan na daya daga cikinsu. Saidai yace hakan ya koya masa darasin cewa Yana da kyau mutum ya kulla alaka da mutane ba na wajan aikinsa kadai ba. Muhammad Zakari ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook.
Buhari ya bar mana gadon Mafi Munin Gwamnati>>Inji Nuhu Ribadu

Buhari ya bar mana gadon Mafi Munin Gwamnati>>Inji Nuhu Ribadu

Duk Labarai
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, sun gaji mafi munin yanayin Gwamnati daga wajan Gwamnatin Buhari. Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Benue bayan munanan hare-haren da aka kai jihar da suka yi sanadiyyar kashe mutane sama da 50. Ya bayyana cewa, suna kokarin ganin an kawo karshen lamarin matsalar tsaro a jihar Benue kuma suna jajantawa Al'ummar da lamarin ya shafa.
Najeriya ta koma ta 4 a cikin jerin kasashen Africa da suka fi karbin tattalin arziki wanda a baya itace ta 1

Najeriya ta koma ta 4 a cikin jerin kasashen Africa da suka fi karbin tattalin arziki wanda a baya itace ta 1

Duk Labarai
A shekarar 2015, Najeriya ce ta daya a jerin kasashen da suka fi karfin Tattalin arziki a Afrika. Saidai yanzu Najeriyar ta koma ta 4 kamar yanda wasu alkaluma suka nunar. 20151 Nigeria — $494.31 billion2 Egypt — $350.12 billion3 South Africa — $346.66 billion4 Algeria — $187.49 billion5 Angola — $131.66 billion20251 South Africa — $410.34 billion2 Egypt — $347.34 billion3 Algeria — $268.89 billion4 Nigeria — $188.27 billion5 Morocco — $165.84 billion*2025 is projected.#Statisense(IMF WEO Apr 2025)
Karanta Munanan Abubuwan da suka faru a Najeriya lokacin da Tinubu ke ƙasashen Turai

Karanta Munanan Abubuwan da suka faru a Najeriya lokacin da Tinubu ke ƙasashen Turai

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja daga nahiyar Turai bayan ziyarar aiki da ya kai biranen Paris da Landan. Shugaba Tinubu ya isa filin jirgi na Nnamdi Azikwe da yammacin ranar Litinin, inda wasu manyan jami'an gwamnati suka tarbe shi. A cewar fadar shugaban kasa, dalilan da suka sanya shugaban ya gudanar da wannan ziyarar sun haɗa da yin nazari kan wasu muhimman cigaban da gwamnatinsa ta samu. ''Zai yi amfani da wannan ziyarar domin yin nazari kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke gudanarwa da kuma tsara yadda za a ɓullo da wasu sabbin shirye-shirye gabanin cikarsa shekara biyu kan karagar mulki," a cewar fadar shugaban ƙasa. A wani ɓangare kuma yayin da ake murnar samun ƙaruwa a asusun gwamnatin Najeriya na ƙasashen waje a babban bankin ƙasar, abubuwa da dama sun ...
Hukumar alhazan Najeriya ta saka ranar fara kai maniyyata Saudiyya

Hukumar alhazan Najeriya ta saka ranar fara kai maniyyata Saudiyya

Duk Labarai
Hukumar Alhazai ta Ƙasa a Najeriya ta sanar da kammala shirye-shirye domin soma jigilar maniyyata aikin Hajjin bana zuwa kasar Saudiyya ranar 9 ga watan Mayu. Hukumar ta Nahcon ta sanar da hakan ne bayan wata ganawa da shugabanta da wakilan majalisar gudanarwa suka yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima. Mataimakin shugaban kasar ne ya gayyaci shugaban hukumar Farfesa Abdullah Saleh Usman da wakilan sashen gudanarwa zuwa ganawar a ofishinsa domin sanar da shi inda aka kwana game da shirye-shiryen aikin hajjin. "Mun yi masa bayani game da shirye-shiryenmu a Makkah da Madina da Arafa kuma ya gamsu, har ma ya ba mu umarnin yadda za mu haɗa kanmu mu yi aikin har zuwa ƙarshensa," kamar yadda Farfesa Saleh ya shaida wa BBC. Kazalika, shugaban ya ce suna sa ran kammala aikin k...
Kotu a Kano ta yankewa Matashi hukuncin kìsà saboda kàshè mata da miji da diyarsu

Kotu a Kano ta yankewa Matashi hukuncin kìsà saboda kàshè mata da miji da diyarsu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Babbar Kotu a jihar Kano ta yankewa Salisu Idris mazaunin Unguwar Gayawa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta yanke hukuncin a kashe Salisu ta hanyar rataya sakamakon bankawa wata mata da mijinta tare da ɗansu ɗan shekara 2 wuta da yayi sanadiyar mutuwarsu. Al'amarin ya faru tun a shekarar 25 ga September, 2019 a unguwar Gayawa dake ƙaramar hukumar Ungoggo, a jihar Kano da misalin ƙarfe 2:00 na daren wannan rana. Mukhtar Abdullahi Shuaibu Fassara a ...
Dansandan Najeriya ya Harbi Kansa Da Bìndìgà ya mùtù

Dansandan Najeriya ya Harbi Kansa Da Bìndìgà ya mùtù

Duk Labarai
Dansandan Najeriya me suna Maxwell Zabu ya Harbi Kansa inda ya mutu har Lahira. Dansandan na aikin baiwa tsohon shugaban karamar hukumar Fatakwal ta jihar Rivers, Victor Ihunwo kariyane inda a ranar Talata ta harbi kansa ya mutu. Lamarin ya farune a Eagle Island gidan tsohon shugaban karamar hukumar. Kakakin 'yansandan jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan bincike.
YANZU-YANZU: Gwamna Bago Ya Sanya Dokar Ta Baci A Garin Minna Biyo Bayan Rikìçe-Ŕikicen Ta Ta’ďdançi

YANZU-YANZU: Gwamna Bago Ya Sanya Dokar Ta Baci A Garin Minna Biyo Bayan Rikìçe-Ŕikicen Ta Ta’ďdançi

Duk Labarai
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar taƙaita zairga-zirgar baburan haya daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar sakamakon yawaitar rikicin 'yan daba a birnin. A cewar gwamnan, yanzu haka an takaita zirga-zirgar 'yan acaɓa da babura masu ƙafa uku a wannan tsakanin. Bago ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati yau Talata. ''Babu wanda zai sake ɗaukar kowane irin nau'i makami a garin Minna. Ina bai wa jami'an tsaro umarni, duk mutumin da kuka gani da makami ku ɗauke shi a matsayin ɗanfashi da makami.'' in ji shi. Ya bayyana cewa sabon matakin na da nufin daƙile matsalolin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a babban birnin jihar. ...