Saturday, December 13
Shadow
Kalli Hoto: Yanda aka kama sojan Najeriya, Yahya Yunusa na safarar makamai a Kaduna

Kalli Hoto: Yanda aka kama sojan Najeriya, Yahya Yunusa na safarar makamai a Kaduna

Duk Labarai
An kama karamin sojan Najeriya me suna Private Yahaya Yunusa a Jaji dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna saboda zargin safarar makamai. Sojan dake aiki a bataliya ta 197 dake jihar Zamfara an kamashine ranar Juma'a da misalin karfe 11:55 a.m. inda aka samu albarusai 214 a wajensa. An kuma kamashi da ATM da yawa. Ya amsa laifinsa inda yace ya saci albarusanne daga wajen aikinsa dan shine ke kula da bindigar A.A da ake kafewa a bayan motar yakin sojoji.
Kalli Yanda aka kama Hòdàr Iblis Boye a cikin litattafan Addini za’a kaita kasar Saudiyya daga Najeriya

Kalli Yanda aka kama Hòdàr Iblis Boye a cikin litattafan Addini za’a kaita kasar Saudiyya daga Najeriya

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama kulli 20 na hodar iblis da aka boye a tsakanin litattafan addini da za'a yi safararta zuwa kasar Saudiyya. Shugaban hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. Yace an yi kamenne ranar 15 ga watan Afrilunnan da muke ciki, saidai bai bayar da karin haske kan ko an kama wadanda suka yi yunkurin aikata wannan laifi ba.
Kalli yanda aka kama sojan Najeriya da fashi da makami da satar mota

Kalli yanda aka kama sojan Najeriya da fashi da makami da satar mota

Duk Labarai
Hukumomin 'yansanda sun kama Sojan Najeriya da ake zargi da satar mota. Sojan ya hada kai da wani farar hula ne dan satar mota kirar Toyota Hilux a garin Legas. An kama su biyunne a yayin da suke kokarin kai motar da suka sata zuwa kudancin Najeriya. Sojan dake aiki a rundunar Operation Delta Safe dake jihar Bayelsa, ya bi dayan farar hular ne dan ya rika nuna ID card dinsa na aikin sojane ana barinsu suna wuce shingen jami'an tsaro. Saidai 'yansanda sun bi sahunsu suka kamasu a yayin da suke kokarin kai motar inda zasu sayar
Buhari ne ya gina ramin da Tinubu ya jefa mu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa Hakeem Baba Ahmad

Buhari ne ya gina ramin da Tinubu ya jefa mu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa Hakeem Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya haka ramin da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jefa 'yan Najeriya ciki. Ya bayyana hakane a wata ganawa ta musamman da aka yi dashi tun bayan da ya ajiye aikin nasa. Yace Shugaba Buhari ya taba cewa jiki Magayi yace a yanzu ne ma ya kamata a fadi wannan kalma. Yace nan da watanni 6 za'a kafa wata tafiya wadda zata jagoranci inda Arewa zata fuskanta.
A bayyane yake Gwamnati kadai ba zata iya bayar da tsaro ba, sai mun tashi tsaye mun baiwa kan mu kariya>>Inji T.Y Danjuma

A bayyane yake Gwamnati kadai ba zata iya bayar da tsaro ba, sai mun tashi tsaye mun baiwa kan mu kariya>>Inji T.Y Danjuma

Duk Labarai
Tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma ya bayyana cewa, Gwamnati ita kadai ba zata iya baiwa mutane kariyar da ya kamata ba. Yace dan kawo karshen matsalar tsaro da garkuwa da mutane dole sai mutane sun tashi tsaye sun kare kansu. Ya bayyana hakane a wajan wani taro a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba. Yace a bayama ya taba fadar haka a Wukari, kuma gashi ya sake nanatawa.
Atiku bashi da Alkawari>>Inji Wike

Atiku bashi da Alkawari>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar bashi da Alkawari. Wike yace bai taba bibiyar Atiku ba. Yace a shekarar 2019, Saraki, da Atiku da Secondus sun sameshi inda suka ce masa zasu bashi babban lauyan Gwamnati idan aka kafa Gwamnati. Yace amma da aka fadi zabe bai san sanda aka kafa Kungiyar lauyoyin da zasu kai kara ba, yace shi da aka ce za'a baiwa babban lauyan Gwamnati ta yaya za'w masa haka. Saidai yace dama hakan bai zo masa da mamaki ba dan yasan cewa Atiku dama bashi da Alkawari. Dan haka Wike yace PDP bata shirya karbar mulki ba a kasarnan. Yace shiyasa ya goyi bayan Tinubu kuma bai yi nadamar yin hakan ba.
Ko Tinubu mutumin kirki ne ko Mugune sai ya sake zama shugaban kasa a shekarar 2027 yayi 8 kamin ya sauka>>Inji Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule

Ko Tinubu mutumin kirki ne ko Mugune sai ya sake zama shugaban kasa a shekarar 2027 yayi 8 kamin ya sauka>>Inji Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya baiwa 'yan Arewa baki inda yace su yi hakuri da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad su koma goyi bayanshi ya sake zama shugaban kasa a shekarar 2027. Ya bayyana hakane jiya a wajan wani taro da aka yi a Akwanga dake jihar inda yace ko Tinubu mutumin kirkine ko Mugune sai ya kammala mulkin shekara 8 kamin ya sauka. Yace Arewa ta yi mulki na shekaru 8 dan haka suma kudu sai sun yi mulkin shekaru 8 kamin mulkin ya dawo Arewa. Yace 'yan siyasane kawai suke kawo rudani saboda basu samu abinda suke so ba. Yace a baya wasu gwamnoni sun rika gaya musu cewa Tinubu ne zabin shugaban kasa dan zai gyara Najeriya kamar yanda ya gyara Legas. Yace amma yanzu sai a canja magana?Yace maganar gaskiya sai Tinubu yayi Takwas.
Dan Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar yayi magana kan Rahoton dake cewa Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya zabgawa babansa mari

Dan Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar yayi magana kan Rahoton dake cewa Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya zabgawa babansa mari

Duk Labarai
A jiyane dai muka samu rahoton dake cewa Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi,Auwal Jatau ya zabgawa ministan harkokin kasashen waje Mari. Saidai Kakakin mataimakin gwamnan, Muslim Lawal ya fito ya musanta wannan zargi inda yake cewa ko gwamna ba zai mari Ministan ba ballantana mataimakin gwamna. Daga baya dai hutudole ya kawo muku rahoton yanda lamarin ya faru dalla-dalla A yau kuma Dan minista Tugga ne me suna Adam ya fito yake karin haske kan lamarin. Adam yace rahoton dake cewa an mari babansa ba gaskiya bane. Inda ya soki dan gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed da rashin da'a na yada wannan magana wadda yace karyace. Yace babansa bai ce yana neman gwamnan jihar Bauchi ba amma an sakashi gaba da suka.
Insha Allahu Daga Yau Ma Bar Darika Kuma Ina Mai Neman Afuwar Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi Da Iyalansa Da Dalibansa, Kuma Daga Yau Da Ni Za A Ďìnga Yada Sùññah, Kuma Na Yi Mafarki Na Ga Sheik Idris Dutsen Tanshi A Aljànnah, Inji Umar Ambato

Insha Allahu Daga Yau Ma Bar Darika Kuma Ina Mai Neman Afuwar Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi Da Iyalansa Da Dalibansa, Kuma Daga Yau Da Ni Za A Ďìnga Yada Sùññah, Kuma Na Yi Mafarki Na Ga Sheik Idris Dutsen Tanshi A Aljànnah, Inji Umar Ambato

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} "Daga Yau Na Bar Dariqa Kuma Ina Neman Afuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi da Iyalansa" Umar Ambato "Nabar Darika daga yau ina kuma neman afuwar Dr Idris Dutsen tanshi da iyalansa da masoyansa musamman wadanda su ke a wannan kafa ta Facebook, sakamakon abin da ya faru dani a cikin baccin da na yi daren jiya, nayi mafalki Dr Idris Dutsen Tanshi yana cikin aljanna, mu yan Dariku an tara mu za'a kai mu wutar Jahannama". "Tunda na tashi daga bacci bana jin karfin jikina, hankalina ya t...
Ina mamaki idan naga ‘yan Siyasa na turuwa zuwa gidan Buhari, Buhari yawa ‘yan Najeriya yaudarara da ba’a taba musu irinta ba>>Inji Buba Galadima

Ina mamaki idan naga ‘yan Siyasa na turuwa zuwa gidan Buhari, Buhari yawa ‘yan Najeriya yaudarara da ba’a taba musu irinta ba>>Inji Buba Galadima

Duk Labarai
Tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana Buhari a matsayin wanda yawa 'yan Najeriya yaudarar da ba'a taba musu irin ta ba. Ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi. Yace ya yiwa Buhari yakin neman zabe a baya kuma dashi aka kafa jam'iyyar APC amma maganar gaskiya Buhari ya boye bakar aniyarsa ce a zuciya inda ya rika nuna yana tare da talakawa, sai daya hau mulki ya fito da ainahin kalarsa. Yace amma ba zai yi magana sosai akan lamarin ba 'yan Najeriya ne zasuwa kansu alkalanci game da wanene Buhari. Ya kara da cewa Buhari kamata yayi ya koma ya ci gaba da neman gafarar Allah biyo bayan zaluncin da yawa mutane.