Saturday, December 13
Shadow
Babu Dan Arewa da ya isa ya zama shugaban kasa a 2027 sai 2031 bayan Tinubu ya gama saboda Buhari ma sau biyu yayi mulki>>Inji Wike

Babu Dan Arewa da ya isa ya zama shugaban kasa a 2027 sai 2031 bayan Tinubu ya gama saboda Buhari ma sau biyu yayi mulki>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa babu dan Arewar da ya isa ya zama shugaban kasa sai a shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gama wa'adinsa karo na biyu. Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja. Wike yace dan Arewa ya yi mulki har sau biyu dan haka Shima Tinubu sai yayi sau biyu daga kudu kamin wani dan Arewa ya sake mulka. Yace babu wani yanki da zaice shi kadai zai ta yin mulkin Najeriya, tsarin karba-karba za'a ci gaba da yi.
Jam’iyyar NNPP ta yi bayani dalla-dalla kan komawar Kwankwaso APC

Jam’iyyar NNPP ta yi bayani dalla-dalla kan komawar Kwankwaso APC

Duk Labarai
NNPP ta karyata jita-jitar sauyin sheka na Kwankwaso Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta karyata jita-jitar da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC. Shugaban jam’iyyar a jihar, Hashimu Dungurawa, ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Kano. Dungurawa ya ce Kwankwaso ba ya bukatar shawarar kowa wajen yanke shawarar siyasa, amma ya jaddada cewa babu wani shiri na sauya sheka. “Ba mu da wata alaka da APC, kuma ba mu da niyyar sauya sheka,” in ji Dungurawa, yana karyata jita-jitar da cewa wani makirci ne kawai. Ya nuna tabbaci cewa gwamnatin NNPP a Jihar Kano tana samun nasara kuma tana maido da doka da oda a yankin. An rawaito shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano yana cewa kofar jam’iyyar a bude take ga Kwankwaso da sa...
Kashim Shettima yayi magana bayan rahoton cewa an hanashi shiga fadar shugaban kasa ya yadu

Kashim Shettima yayi magana bayan rahoton cewa an hanashi shiga fadar shugaban kasa ya yadu

Duk Labarai
Ba wanda ya hana ni shiga fadar shugaban kasa - Kashim Shettima Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana rahotannin da ke yawo cewa an hana shi shiga fadar shugaban kasa a matsayin karya maras tushe. Daily Trust ta rawaito cewa a daren jiya Juma’a ne wasu rahotanni su ka fito daga wata kafar labarai ta yanar gizo suna cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa shiga fadar shugaban kasa ta hannun wasu jami’an tsaro, tare da cewa an killace shi a gidansa har sai shugaban kasa ya dawo daga tafiyarsa ta kasashen waje. Amma cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Mista Stanley Nkwocha, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, ya ce: “A 'yan kwanakin nan, an shirya kuma an tsara yada labaran karya da gangan akan...
Miji ya kàshè mutumin dake shirin auren tsohuwar matarsa da yawa saki 3 a jihar Naija

Miji ya kàshè mutumin dake shirin auren tsohuwar matarsa da yawa saki 3 a jihar Naija

Duk Labarai
Wani mutum me suna Alhaji Yikangi daga kauyen Chikan na karamar hukumar Gbako jihar Naija ya kashe bazawarin tsohuwar matarsa me suna Muhammad Ma’aba. Alhaji Yinka yawa matarsa me suna Fatima Suleiman saki 3 wanda bisa tsarin addinin Musulunci ba zai iya sake aurenta ba sai bayan ta sake yin wani auren ta fito. Saidai Alhaji Yinka ya sha Alwashin matar tasa saidai ta dawwama ba aure dan kuwa ba zai barta ta yi auren ba. Rahoton yace ya jagoranci mutane inda sukawa Muhammad Ma'aba Kwantan Bauna suka ta dukansa har sai da ya mutu. Kakakin 'yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna bincike dan kama duka masu hannu a lamarin.
Ku cire rai: Tinubu ba zai cika muku Alkawuran da ya dauka ba>>Inji Datti Baba Ahmad

Ku cire rai: Tinubu ba zai cika muku Alkawuran da ya dauka ba>>Inji Datti Baba Ahmad

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2023 karkashin jam'iyyar Labour Party, Datti Babba Ahmad ya bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai cika Alkawuran da ya daukarwa 'yan Najeriya ba. Yace dalili kuwa an tabbatar cewa jam'iyyar APC ta shugaban kasar, makaryaciyace. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Arise TV. Datti Baba Ahmad ya kara da cewa, Ya hango kamin zaben 2027, 'yan Najeriya zasu hada kai kuma jam'iyyar APC zata fad...
Wani Bincike ya gano Kaso 70 na ‘yan Najeriya na jin haushin Gwamnati da masu kudi

Wani Bincike ya gano Kaso 70 na ‘yan Najeriya na jin haushin Gwamnati da masu kudi

Duk Labarai
Binciken da wata kungiya me suna Edelman Trust Barometer dake bincike akan yanda mutane ke kallon Gwamnati, Kasuwanci, Kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen yada labarai ta yi ya nuna cewa kaso na mutane da yawa a Najeriya na jin haushin Gwamnati da masu kudi. Kungiyar ta gudanar da wannan bincikene ta hanyar tambayar mutane ra'ayoyinsu kan ayyukan gwamnati da yanda ake gudanar da kasuwanci da sauransu. Kaso 70 sun bayyana mata cewa suna ganin abinda masu kudi ke yi na taimakawa wajan kara jefa 'yan Najeriya cikin halin kaka nikayi, hakanan da yawa sun zargi masu kudin da rashin biyan haraji. Kungiyar ta bayyana cewa, mutane da yawa kuma sun nuna rashin amincewa da gwamnati, da kafafen yada labarai da kuma Kungiyoyi masu zaman kansu.
Na yiwa Atiku Makarkashiya a zaben shekarar 2023 duk na ni dan PDP ne hakanan idan ya sake tsayawa takara a shekarar 2027 zan sake yi masa makarkashiya>>Inji Ayodele Fayose

Na yiwa Atiku Makarkashiya a zaben shekarar 2023 duk na ni dan PDP ne hakanan idan ya sake tsayawa takara a shekarar 2027 zan sake yi masa makarkashiya>>Inji Ayodele Fayose

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayse ya bayyana cewa, a zaben shekarar 2023 ya yiwa Atiku Abubakar makarkashiya. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels. Yace babbar matsalar da aka samu a PDP shine da aka baiwa dan Arewa damar tsayawa takarar shugaban kasa bayan da dan Arewa ya kammala shekaru 8 yana mulki. Yace Najeriya tafi PDP muhimmanci. Yace kuma idan Atiku ya sake cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027, zai sake yi masa makarkashiya. Hakan ya zowa mutane da yawa da bazata musamman ganin cewa, shi Fayose dan PDP ne.
Babu irin muguntar da Buhari bai shiryawa Tinubu ba dan ya fadi zaben 2023 amma da yake Allah na sonshi, ya tsallake>>Inji Ministan Abuja Wike

Babu irin muguntar da Buhari bai shiryawa Tinubu ba dan ya fadi zaben 2023 amma da yake Allah na sonshi, ya tsallake>>Inji Ministan Abuja Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa, babu irin muguntar da tsohuwar gwamnatin APC batawa Tinubu ba dan kada ya zama shugaban kasa ba amma Allah ya tsallakar dashi. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma'a. Yace An kawo sabbin tsare-tsare na wahalar man fetur da canjin kudi da sauransu duk dan a hana Tinubu zama shugaban kasa amma Allah ya tsallakar dashi. Yace haka ne ke faruwa dama idan Allah na son mutum. Yace kuma babu maganar wani dan Arewa ya sake zama shugaban kasa a Najeriya har sai bayan shekarar 2031 bayan Tinubu ya kammala mulkinsa zango na biyu.
Ku rika Sadaka, Tana jawo Alkhairai da yawa>>Inji Tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Ku rika Sadaka, Tana jawo Alkhairai da yawa>>Inji Tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya baiwa 'yan Najeriya shawarar su rika yin sadaka inda yace tana jawo Alkhairai da yawa. Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane ranar Juma'a a wajan kaddamar da fara gyaran wani masallacin dake Kobiti, Abeokuta, jihar Ogun. An kaddamar da fara shirin gyaran masallacin a Dakin karatu na Obasanjon dake Abeokuta. A jawabin da yayi lokacin bude kaddamar da aikin, Obasanjo yace sada wadda kowane mutum na iyayi ba tare da la'akari da addini ko karfin tattalin arziki ba, tana jawo Alkhairai da yawa.