Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle yace Sojan Ruwa da ya tare Nyesom Wike bai aikata laifin komai ba
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, sojan ruwa, A. Yerima da ya tare Ministan babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike bai aikata laifin komai ba.
Minista Bello Matawalle ya bayyana cewa sojan na bakin aikinshi ne kuma yana bin umarnin me gidansa ne.
Bello Matawalle ya bayyana hakane a hirar da aka gudanar dashi a gidan Talabijin na DCL Hausa.
Ya kuma kara da cewa, Wike yayi hattara dan kuwa wulakanta sojan da yayi kamar ya wulakanta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne.








