Tuesday, December 16
Shadow
Kalli bidiyo inda Shiekh Adam Muhammad Dokoro yace Idan akwai wanda ya taba yin Zina ya tashi tsaye a wajen wa’azinsa

Kalli bidiyo inda Shiekh Adam Muhammad Dokoro yace Idan akwai wanda ya taba yin Zina ya tashi tsaye a wajen wa’azinsa

Duk Labarai
Babban malamin Islama, Shiekh Adam Muhammad Dokoro ya nemi idan akwai wanda ya taba yin zina ya mike tsaye. Sai dai babu wanda aka samu ya mike. https://www.tiktok.com/@mhaliru92/video/7477552048578284806?_t=ZM-8uNPYcIktPh&_r=1 Dan haka yace idan mutum yana yi ya daina ya tuba dan idan bai daina ba sai ya mike a gaban Allah. Kalli Bidiyon anan
Ana shirin sasanta Kwankwaso da Ganduje da Shekarau 

Ana shirin sasanta Kwankwaso da Ganduje da Shekarau 

Duk Labarai
Tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kano ta Tsakiya, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun sulhunta tsakanin jagororin siyasar jihar: Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Shekarau. Zaura ya ce haɗin kan manyan jagororin zai taimaka wajen gyara siyasar jihar, tare da samar da cigaba ta yadda jihar za ta yi gogayya da jihar Legas da wasu jihohin da suka ci gaba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Zaura ya ce, "irin adawar siyasa da ake yi a Kano ba ta da amfani. A shirye nake in shige gaba wajen samar da maslaha tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Shekarau. Ya kamata mu fifita ci gaban Kano sama da son ranmu. Da zarar an samu wannan nasarar, Legas da sauran jihohi sai sun yi koyi da Kano wajen siyasa ta hank...
Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Duk Labarai
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, wato Arewa Consultative Forum ko kuma ACF a taƙaice ta nuna damuwarta kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi wanda kakakin ƙungiyar, Muhammad-Baba ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce akwai buƙatar a gudanar da bincike mai kyau domin tantance sahihancin zargin, kamar yadda tashar Channels a shafinta na intanet. "A yanzu dai yadda abubuwa suke shi ne zargin nan zai iya ɓata sunan Najeriya a idon duniya," in ji ƙungiyar, wadda ta nuna damuwa kan yadda a cewarta har zuwa yanzu, sanatocin arewa ne kaɗai suka fuskanci takunkumi kamar dakatarwa a majalisar ta 10. "Wannan ya sa ACF ke fargabar ko dai abin ɓoye ne ya fara fitowa fili na...
Mun kusa fara biyan alawus ɗin naira 77,000 – NYSC

Mun kusa fara biyan alawus ɗin naira 77,000 – NYSC

Duk Labarai
Hukumar NYSC ta ce ta kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus ɗin naira 77,000. Hukumar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rashin fara biyan sabon alawus ɗin bayan an sanar da ƙari daga naira 33,000 da ake biya biyo bayan ƙara mafi ƙanƙantar albashi. A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin fara biyan sabon alawus ɗin, amma har yanzu ba a fara biya ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga masu bautar ƙasar. A watan Janairu, darakta-janar na NYSC, Birgediya-janar Yushau Ahmed ya sanar da cewa daga watan Fabrairu za a fara biyan sabon alawus ɗin, amma kuma ba a biya ba a watan na Fabrairu da ya gabata. Daraktan riƙo na hulɗa da jama'a na hukumar, Caroline Embu, ta ce suna jiran kuɗi ne da umarni kafin fara biyan sa...
Darajar wasu kuɗaɗen kirifto ta tashi bayan sanarwar Donald Trump

Darajar wasu kuɗaɗen kirifto ta tashi bayan sanarwar Donald Trump

Duk Labarai
Darajar wasu kuɗaɗen kirifto sun tashi bayan shugaba Donald Trump ya sanar da cewa za a kafa wani rumbun adana kuɗaɗen kirifto na ƙasar Amurka. Ya ambaci kuɗin kirifto na Bitcoin da Ethereum da XRP, da ADA SOL a cikin wani jawabi da ya yi a kafofin sadarwa, inda ya ƙara da cewa Amurka ce za ta zama babbar cibiyar hada-hadar kirifto ta duniya. Jim kaɗan da yin jawabin ne darajar kuɗaɗen da ya ambata suka tashi, inda Bitcoin da Etherium suka ƙara daraja da kusan kashi 10 kafin suka ja baya, sannan sauran kuɗaɗen ma suka tashi. A baya dai Trump da matarsa Melania sun fitar da kuɗinsu na kirifto na matakin meme.
Hukumar EFCC tace itace ta kai samame Otal a Jihar Naija ba ‘yan Bìndìgà ba

Hukumar EFCC tace itace ta kai samame Otal a Jihar Naija ba ‘yan Bìndìgà ba

Duk Labarai
A jiyane dai muka samu rahoton cewa, 'yan Bindiga cikin shiga irin ta EFCC sun kai samame wani otal dake Chanchanga inda suka sace mutane 10. Saidai a yau, hukumar EFCC ta fito inda ta bayyana cewa, itace ta kai wannan samame ba 'yan Bindiga ba. Hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa, ta samu bayanai akan wasu 'yan damfarar yanar gizo ne dake zaune a otal din inda wakilanta na jihar Kaduna suka kai samame kan otal din me suna WhiteHill Hotel dake Chanchaga a jihar ta Naija. Sanarwar tace an kama mutane 11 daga otal din sannan hukumar tace ta gudanar da aikinta cikin kwarewa da bin doka dan haka bata san daga inda maganar 'yan Bindiga ta samo asali ba. Hakanan kuma sanarwar tace an kwace motoci 2 da wayoyin hannu 13. Sanarwar tace za'a gurfanar da wadanda ake zargin...
Kalli Bidiyo yanda aka wulakanta wani barawon Kunin Aya inda aka sashi yace shi barawo ne ya saci kunun aya

Kalli Bidiyo yanda aka wulakanta wani barawon Kunin Aya inda aka sashi yace shi barawo ne ya saci kunun aya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wani mutum ne da aka kama a wani Shago a Abuja ya saci kunin Aya. Bayan kamashi an sashi ya rike takardar da ta ce ni barawo ne na saci kunun aya. https://www.youtube.com/watch?v=EFI6pOhuVsc Daga baya dai an barshi ya tafi ba'a masa komai ba. Mutanene suka roki me shagon ya kyaleshi.
Bai kamata ka turo matarka ta rika fada da Natasha ba, kai ya kamata ka tsaya a yi da kai>>Betty Akeredolu

Bai kamata ka turo matarka ta rika fada da Natasha ba, kai ya kamata ka tsaya a yi da kai>>Betty Akeredolu

Duk Labarai
Matar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Betty Akeredolu ta bayyana cewa bai kamata kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya saka matarsa a cikin fadan da suke da Sanata Natasha Akpoti ba. Tace kamata yayi ace ya tsaya an yi fadan dashi ba ya koma gefe ya turo matarsa ba. Betty ta bayyana hakanne a kafar X. Tace kuma Sanata Natasha Akpoti ta birgeta data fito ta nuna rashin jin dadinta kan canja mata kujera ba tare da saninta ba. Tace dan an yiwa wasu sun yi shiru hakan ba yana nufin itama ta yi shiru bane. tace irin su Sanata Natasha Akpoti ne ya kamata ace mata suna sakawa a gaba dan su jagorancesu musamman a majalisa.