Saturday, May 2
Shadow
Tinubu ne ke daukar nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar mu ta Labour party>>Peter Obi

Tinubu ne ke daukar nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar mu ta Labour party>>Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ke da alhakin rikicin dake faruwa a cikin jam'iyyar su. Obi ya bayyana hakane a yayin da ake masa tambayoyi a gidan Talabijin na Arise TV inda yace yana da tabbacin Gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin rikicin dake faruwa a jam'iyyar. Ya bayyana cewa, suna son yada rikici a cikin jam'iyyar ta Labour Party.
Jigo a Jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam’iyyar

Jigo a Jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam’iyyar

Duk Labarai
Jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi ya bayyana cewa, a Shirye yake ya koma jam'iyyar APC duk da a baya ya soki jam'iyyar da salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace lallai a baya ya soki Gwamnatin Tinubu amma a yanzu idan dai ya samu dama, zai iya komawa jam'iyyar APC. Yace kuma a shirye yake dan yin aiki tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu din domin ko da a baya dama yayi aiki tare dashi.
Ji yanda Bòm ya kàshè masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Ji yanda Bòm ya kàshè masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Duk Labarai
Kimanin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya bayan tarwatsewar wani abun fashewa da ake zargi mayaƙan Lakurawa sun dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato. Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan babura na hanyarsu ta dawowa daga yawon bikin sallah a ƙauyen Gwabro. Bayanai sun ce an dasa abun fashewar ne a ƙarƙashin wata itaciya da ke zaman wurin hutawar dakarun sojoji a lokacin da suka fito sintiri a yankin. Majiyiyo sun ce mutum shida sun mutu nan take yayin da ɗaya daga cikin wasu mata biyu yara da suka jikkata ta rasu washegari. Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Tangaza, Alhaji Ghazzali Rakah ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa waɗanda abin ya shafa mazauna ƙauyen Zurmuku ne. Wannan dai ba shi na farau ba, domin kuwa a watan...
Ji bayani Dalla-Dalla: DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA

Ji bayani Dalla-Dalla: DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA

Duk Labarai
DA KYAR JAMI'AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA. Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana bayyana cewar sai dai aka hada da jami'an tsaro aka ceci Dan wasan barkwanco Ali Art-work Wanda aka fi sani da Madagwal. Madagwal ya fada komar Yan Kwankwasiyya ne jiya Lahadi lokacin daya sake zuwa karbar darikar Kwankwasiyyar, a hannun Ubanta Injiniya Rabiu Musa, a wani taro da suka gudanar na bikin Sallah a Jihar. Kafin Yanzu bayan ficewar sa a shekararun baya Madagwal ya koma suka da jefa kalaman batanci ga Rabiu Musa Kwankwaso da sauran Magoya bayan sa. Haka Kuma ya sha chachchakar salon Mulkin Abba Kabir Yusuf, tare da bukatar cewar Kwankwaso ya yiwa Gwamnatin Jihar Kano kakagida shi yasa baa tabuka abun a zo a gani. Wannan ya Saka ...
Tsohon soja ya mùtù a hannun ‘Yàn Bìndìgà duk da biyan Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fansa

Tsohon soja ya mùtù a hannun ‘Yàn Bìndìgà duk da biyan Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fansa

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kogi na cewa, wani tsohon soja me suna Major Joe Ajayi ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane duk da danginsa sun biya kudin fansarsa Naira Miliyan 10. An yi garkuwa dashine a gidansa dake Odo-Ape na karamar hukumar Kabba-Bunu ranar May 21, 2025 da misalin karfe 11:30pm. Da farko dai wanda suka yi garkuwa dashi sun nemi Naira Miliyan 50 inda daga baya da suka ga bashi da lafiya zai rasu. Sai suka ce a kai musu Naira Miliyan 10, bayan da aka kai musu, suka bayyana inda za'a je a daukeshi, sai gawarsa aka tarar. Tuni aka kai gawar tasa zuwa mutuware dake Asibitin Kabba Specialist Hospital. Masu garkuwa da mutane sun matsawa jihar Kogi a 'yan kwanakinnan.
Ya Zama Wajibi Ga Ƴan Nijeriya Mu Tashi Tsaye Wajen Ganin An Kawar Da Gwamnatin APC 2027 A Kowane Matakai, Saboda Mawuyacin Halin Da Ta Jefa Mu, Ta Hanyar Haɗaka Da Muke Shirin Kafawa Nan Gaba Kaɗan, Cewar Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa

Ya Zama Wajibi Ga Ƴan Nijeriya Mu Tashi Tsaye Wajen Ganin An Kawar Da Gwamnatin APC 2027 A Kowane Matakai, Saboda Mawuyacin Halin Da Ta Jefa Mu, Ta Hanyar Haɗaka Da Muke Shirin Kafawa Nan Gaba Kaɗan, Cewar Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa

Duk Labarai
Ya Zama Wajibi Ga Ƴan Nijeriya Mu Tashi Tsaye Wajen Ganin An Kawar Da Gwamnatin APC 2027 A Kowane Matakai, Saboda Mawuyacin Halin Da Ta Jefa Mu, Ta Hanyar Haɗaka Da Muke Shirin Kafawa Nan Gaba Kaɗan, Cewar Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Kalli Bidiyo: Ya yi hàdàrì da motarsa jim kadan bayan da ya sayota daga wajan sayar da mota

Kalli Bidiyo: Ya yi hàdàrì da motarsa jim kadan bayan da ya sayota daga wajan sayar da mota

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false,"used_sources":{"version":1,"sources":[{"id":"336487999083211","type":"ugc"}]}} Wannan wani matashi ne da ya sayo sabuwar mota, saboda doki ya rika gudun wuce sa'a da ita har daga karshe ya je ya fada cikin wani gini. https://twitter.com/General_Somto/status/1932040367978795216?t=YNBNkpoFUVPDxlF7qYnYNQ&s=19 Wasu dai sun jajanta masa inda wasu suka mai Allah kara.
Kalli Hotuna yanda aka gano Kòkòn kàn mùtùm a cocin wani fasto da ake zargi da yin tsàfì da sàssàn jìkìn mutane

Kalli Hotuna yanda aka gano Kòkòn kàn mùtùm a cocin wani fasto da ake zargi da yin tsàfì da sàssàn jìkìn mutane

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Enugu sun sanar da gano kokon kan mutum a wani kango inda aka ginin wata coci. Ana zargin faston cocin da ake kira da Chinedu Solomon Ezedike yana amfani da sassan jikin dan Adam wajan gudanar da tsafi. An gano hakan ne bayan binciken hadaka wanda aka yi da DPO din 'yansanda na karamar hukumar Igbo-Eze dake jihar. A baya dai an zargi faston da kashe wasu mutane 4 'yan uwan juna wanda ake zargin yayi amfani dasu ne wajan aikata tsafi. Shugaban karamar hukumar, Barrister Ferdinand Ukwueze ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami'an tsaro sun kai samame wajanne bayan samun bayanan sirri. Rahoton yace ana kan ci gaba da binciken lamarin.
Gwamnatin Tarayya zata farfado da kamfanin Karafa na Ajakuta

Gwamnatin Tarayya zata farfado da kamfanin Karafa na Ajakuta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata korkiro da kamfanin Karafa na Ajakuta. Ministan karafa, Shuaibu Abubakar Audu, ne ya bayyana hakan inda yace Gwamnatin tuni ta shiga mataki na gaba wajan farfado da kamfanin. Ministan ya bayyana hakane a yayin da yake ganawa da wasu 'yan jam'iyyar APC yayin da suka kai masa ziyara a gidansa dake jihar Kogi. Yace tuni Gwamnatin ta shiga yarjejeniya dan farfado da kamfanin sannan tana kokarin jawo hankalin masu zuba hannun Jari musamman daga kasar China dan su zo su zuba jari a kamfanin dan farfado dashi. Yace suna aiki me kyau kan lamarin kuma zasu tabbatar sun bayar da sakamako me kyau.