Dole Ne Mu Magance Matsalar Rashin Abinci Mai Gina Jiki, Inji Kashim Shettima
Dole Ne Mu Magance Matsalar Rashin Abinci Mai Gina Jiki, Inji Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira wajen kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Kungiyar Tarayyar Turai domin yaki da Matsalar karancin Abinci mai gina jiki da sauran kalubalen jin kai a kasar.
Kashim Shettima ya furta hakan ne a yayin da yake karbar bakuncin tawagar jakadan EU mai barin gado Samuela Isopi a wata ziyarar bankwana da ya kai fadar shugaban kasa.
Mataimakin ya kuma yaba da irin gudunmawar da kungiyar ta EU ke bai wa Najeriya Musamman a fannin Ayyukan jin kai da kasuwanci.Shettima ya yaba da ayyukan Isopi a Najeriya, ciki har da rawar da ta taka wajen karfafa huldar EU da Najeriya, wajen samar da zaman lafiya da tsaro.
A nata bangaren ita ma Isopi ta yi tsokaci k...







