Tuesday, December 16
Shadow
Za’a rage farashin kiran waya dana data daga kaso 50 zuwa kaso 35

Za’a rage farashin kiran waya dana data daga kaso 50 zuwa kaso 35

Duk Labarai
Rahotannin da kafar hutudole ta samu na cewa, za'a rage farashin kudin kiran waya dana data daga kaso 50 da aka kara zuwa kaso 35. Hakan ya bayyanane a cikin jawabin da shugaban kungiyar NLC ya fitar inda suke barazanar shiga yajin aiki idan ba'a yi wannan ragi ba. Hutudole ya faimci cewa, an yi zama tsakanin Gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro inda aka cimma matsaya gane da karin kudin kiran waya dana data, maimakon kaso 50 cikin 100 da aka yi, yanzu zai koma kaso 35 cikin 100. Kungiyar NLC tace idan ba'a tabbatar da wannan kari ba, zata tafi yajin aiki.
Ba zamu yadda da karin kudin wutar lantarki ba>>NLC

Ba zamu yadda da karin kudin wutar lantarki ba>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC ta yi gargadin cewa idan aka ce za'a kara kudin wutar lantarki ba zasu amince da hakan ba, zasu tafi yajin aiki. Kungiyar tace ba zata amince da duk wata dabara ta kokarin kara kudin wutar lantarkin ba. Tace idan aka yi hakan zata jagoranci gagarumar zanga-zanga. Kungiyar ta NLC tace tana sane da shirin da ake yi na mayar da kowa da kowa kan tsarin Band A na wuta da sunan wai inganta samar da wutar, kungiyar tace ba zata amince da hakan ba dan yunkuri ne na kara kudin wutar lantarkin.
Ana ci gaba da kiraye-kirayen cewa Jihohin Arewa da suka bada hutun Ramadan a makarantu basu kyauta ba, inda Kungiyar Kiristocin CAN tace ko Saudi Arabia da UAE basu bayar da hutu a makarantu ba saboda Ramadan

Ana ci gaba da kiraye-kirayen cewa Jihohin Arewa da suka bada hutun Ramadan a makarantu basu kyauta ba, inda Kungiyar Kiristocin CAN tace ko Saudi Arabia da UAE basu bayar da hutu a makarantu ba saboda Ramadan

Duk Labarai
Masu sharhi a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta musamman daga kudancin Najeriya kuma mafi yawanci Kiristoci na ci gaba da yin Allah wadai da hutun da wasu jihohin Arewa suka bayar a makarantu saboda zuwan watan ramadana. Ko da a jiya, saida kungiyar Kiristocin CAN ta fitar da sanarwar cewa, bata goyon bayan bayar da wannan hutu i da tace babban abin takaici ma shine ba'a tuntubeta ba kamin bayar da wannan hutu. Jihohin da suka bayar da irin wannan hutu sun hada da Katsina, Kano, Kebbi da Bauchi. A maganar da Kungiyar kiristoci ta CAN tayi tace akwai kasashen da suka fi 'yan Najeriya yawan musulmai amma duk da haka basu bayar da hutun Azumin watan Ramadana a makarantun su ba maimakon hakan sun rage yawan awannin da ake zuwa makarantunne. Da safiyar yau, Litinin ma Kaf...
Kungiyar Kwadago ta NLc na barazanar shiga yajin aiki saboda karin kudin kiran waya dana data

Kungiyar Kwadago ta NLc na barazanar shiga yajin aiki saboda karin kudin kiran waya dana data

Duk Labarai
Kungiyar Kwadago ta NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki muddin gwamnati bata mutunta alkawarin da suma cimmawa ba. Kungiyar ta bayyana cewa sun cimma matsayar cewa za'a rage karin kudin kiran waya dana data da aka yi da kaso 50 zuwa 35. Kungiyar tace idan Gwamnatin ta kasa mutunta wannan yarjejeniyar sun sanar da wakilansu na fadin Najeriya cewa su shirya yin zanga-zanga.
Sanata Barau ya ce zai goyi bayan ƙirƙiro jihar Karaɗuwa

Sanata Barau ya ce zai goyi bayan ƙirƙiro jihar Karaɗuwa

Duk Labarai
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya ce zai yi aiki tare da Sanata Muntari Dan-Dutse mai wakiltar yankin Funtua na jihar Katsina domin tabbatar da ƙirƙiro jihar Karaɗuwa daga jihar Katsina ta arewa maso yamma, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito a shafinta na intanet. Ya ce ƙirƙiro sabuwar jiha zai taimaka wajen ci gaba da haɓaka tattalin arzikin yankin da mutanenta. "Zan yi aiki tare da ɗan'uwana, Sanata Muntari Dan-Dutse domin ganin an ƙirƙiri jihar ta Karaɗuwa daga jihar Katsina. Yankin Karaɗuwa na da duk abin da ake buƙata domin zama jiha. Ina goyon bayan buƙatar nan ta mutanen yankin duk da cewa lamari ne mai wahala," in ji shi. Barau ya bayyana haka ne a lokacin da yake jagorantar rabon tallafin kayan abinci na azumi ga dubban ...
Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio – Mijin Natasha

Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio – Mijin Natasha

Duk Labarai
Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan ya magantu game da rikicin da ke tsakanin matarsa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio. Mijin, wanda basarake ne a yankin Neja Delta ya ce matarsa ta faɗa masa lokacin da Akpabio ya ci zarafinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. "Da kaina na je na same shi na buƙaci ya ba matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotan da ke tsakaninmu. Bayan mun tattauna sai muka amince da a warware maganar cikin mutunci. "Amma bayan maganar da muka yi, sai matata ta cigaba da bayyana damuwa game da irin cin zarafin da take fuskanta daga shugaban majalisar dattawar. "Ni dai na yarda da matata, kuma aure muka yi na soyayya da ƙauna. Babu abin da ya fiye min ita a yanzu domin ita ce...
Ramadan: Coci ya raba wa musulmi kayan abinci a Kaduna

Ramadan: Coci ya raba wa musulmi kayan abinci a Kaduna

Duk Labarai
Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry da ke unguwar Sabon Tasha a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ya raba wa musulmi masu ƙananan ƙarfi da makarantun addinin musulunci kayan abinci domin su samu abin sakawa a bakin salati a lokacin azumi. Shugaban coci, Fasto Yohanna Buru ne ya jagoranci raba kayan abincin, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin musulmi da kirista. "Muna mayar da biki ne kan yadda Hajiya Ramatu Tijjani take yawan ba kirista kayan abinci a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara," in ji shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Fasto Buru ya ce suna da burin tallafa wa aƙalla mutum 1,000 ne a azumin na bana, sannan ya ce ya jagoranci haɗa malamai da fastoci aƙalla guda 30 domin...
In kana da kudi, zaka iya siye kowa a kasarnan ka ci zabe>>Inji Tsohon Gwamnan Imo

In kana da kudi, zaka iya siye kowa a kasarnan ka ci zabe>>Inji Tsohon Gwamnan Imo

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Imo, Achike Udenwa ya bayyana cewa lamarin siyasa da mulki a kasarnan ya tabarbare inda komai ya koma maganar kudi. Yace idan kana da kudi, zaka iya saye Sojoji, 'yansansa, Hukumar zabe dama masu zaben. Ya bayyana hakane a wajan wata hira da aka yi dashi. Yace yanzu idan mutum ya fito neman zabe babu maganar me zaiwa mutane ko menene halinsa, kudi kawai ake dubawa, kowa yana duba me zai samu.
Ina da addu’ar da zan yi in gama da ‘yan Bìndìgà>>Pastor Adegboye Gabriel Olabisi 

Ina da addu’ar da zan yi in gama da ‘yan Bìndìgà>>Pastor Adegboye Gabriel Olabisi 

Duk Labarai
Pastor Adegboye Gabriel Olabisi na cocin Worksword of God Church ya bayyana cewa ta hanyar karfin da Allah ya bashi, yana da addu'ar da zai yi wadda zata gama da 'yan Bindiga. Worksword of God Church dai a baya ya hakaito cewa, Bola Ahmad Tinubu zai zama shugaban Najeriya tun kamin ya zama. Kuma yakan bayyana abubuwa da yake tunanin zasu faru nan gaba