Saturday, December 13
Shadow
Ba’a isa a hanamu yin hukunci da shari’ar musukunci ba>>Musulman Yarbawa suka mayarwa da Gwamnoninsu Martani

Ba’a isa a hanamu yin hukunci da shari’ar musukunci ba>>Musulman Yarbawa suka mayarwa da Gwamnoninsu Martani

Duk Labarai
Shugaban kotun shari'ar Musulunci dake jihar Kwara, Justice Abdurraheem Sayi ya bayyana cew basa bukatar amincewar hukumin Gwamnati ko na sarakunan gargajiya kamin su kafa kotun shari'ar Musulunci. Yace duk masu adawa da kafa kotunan shari'ar musulunci a jihohin Yarbawa kiyayyar addinin ce kawai ta sasu hakan ba wani abuba. Ya bayyana hakane a yayin da yake gabatar da yawabi a jami'ar Legas akan maganar shari'ar Musulunci a jihohin Yarbawa. Ya bayyana cewa ko shugaban kasa, doka bata bashi damar hana samar da kotun shari'ar Musulunci ba. Yayi kira ga mahukunta a yankin dasu bayar da dama ga musulman dake so su aiwatar da shari'ar Musulunci domin dokokin jihohinsu basu baiwa musulmai irin wannan dama ba.
Kuma Dai: Bidiyon Tsiraici na wata ‘yar TikTok ya kara bayyana

Kuma Dai: Bidiyon Tsiraici na wata ‘yar TikTok ya kara bayyana

Duk Labarai
A yayin da a baya aka yi fama da bayyana bidiyoyin tsiraici na 'yan TikTok irin su Babiana da Hafsat baby, an yi tsammanin abin ya wuce. Saidai a yanzu ma an sake kumawa inda bidiyon tsiraici na wata shahararriyar 'yar TikTok ya sake bayyana. Saidai a wannan karin lamarin yayi Muni. Matashiyar me suna Aisha dake da dubban mabiya a kafar ta sada zumunta an gantane wani namiji wanda bai nuna fuskarsa ba yana lalata da ita. A yayin da Su Babiana da Hafsat baby daukar kansu suka yi su kadai tsirara, ita kuwa A'isha wanda ke lalata da itace ya dauketa hoton bidiyon a yayin da yake aikata lalatar da ita. Munin bidiyon yasa ba zamu iya wallafashi anan ba.
Kalli Bidiyo: Maganar Gaskiya Yawancin Masu Kallon Mu Ba Su Da Cikaķķen Ilmi, Inji Jarumar Finafinan Hausa, Zahra Diamond

Kalli Bidiyo: Maganar Gaskiya Yawancin Masu Kallon Mu Ba Su Da Cikaķķen Ilmi, Inji Jarumar Finafinan Hausa, Zahra Diamond

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Zahara Diamond ta shiga bakin 'yan kafafen sada zumunta inda aka ganta a wani faifan bidiyo tana fadar cewa, yawanci masu kallonsu basu da ilimi. Bidiyon dai gajerene wanda ba'a sami cikakken shi ba. Saidai duk da haka mutane sau mata zafafan raddi suke. https://www.tiktok.com/@kannywoobackup/video/7474399386768854327?_t=ZM-8uB3tqfyU0T&_r=1 Me za ku ce?
Kalli Bidiyon Kwallon da Neymar yaci daga Corner data dauki hankula sosai

Kalli Bidiyon Kwallon da Neymar yaci daga Corner data dauki hankula sosai

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Santos, Neymar Jr. Ya ciwa kungiyarsa kwallo daga Corner wadda ta dauki hankula 'yan kallo sosai. Neymar ya ciwa Santos kwallon ne a wasanninsa na farko-farko da ya bugawa kungiyar. https://www.tiktok.com/@cfc.zx0/video/7474739218237967638?_t=ZM-8uB0E9qwmxh&_r=1 Kamin ya ci kwallon, Abokan hamayya sun rika wa Neymar Ehon bama so wanda yace su ci gaba inda ya buga Kwallon ya basu mamaki.
Sai mun hada kai da ‘yan kudu dan ceto Najeriya daga halin da take ciki>>El-Rufai

Sai mun hada kai da ‘yan kudu dan ceto Najeriya daga halin da take ciki>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, sai Arewa ta hada kai da 'yan kudu dan ceto Najeriya daga halin data tsinci kanta. El-Rufai ya bayyana hakane a yayin ziyarar gaisuwar da ya kai Jihar Delta ta gaisuwar mutuwar Edwin Clark. El-Rufai wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yawa jagora zuwa jihar Delta yace Arewa ta sha hada kai da kudu dan cimma burikanta na siyasa.
Mahara sun shiga coci suka yankewa Fasto yatsu suka kuma harbeshi sannan suka sace mutane 6

Mahara sun shiga coci suka yankewa Fasto yatsu suka kuma harbeshi sannan suka sace mutane 6

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Delta sun bayyana cewa, wasu mahara sun shiga coci a garin Asagba Ogwashi dake karamar hukumar, Aniocha South ta jihar ina suka harbi fasto suka sace mutane 6. Kakakin 'yansandan jihar, Mr. Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace tuni jami'ansu suka bazama daji dan bin sahun masu garkuwa da mutanen. Zuwa yanzu dai maharan basu kira 'yan uwan wadanda suka sace din ba. Tuni aka garzaya da faston zuwa Asibiti dan duba lafiyarsa.
Hattara: An gano masu gasa kaji na gefen hanya suna amfani da lalatatun Kaji

Hattara: An gano masu gasa kaji na gefen hanya suna amfani da lalatatun Kaji

Duk Labarai
Wani Rahoto na musamman da Jaridar Vanguard ta yi ya gano cewa wasu masu gasa kaji na gefen hanya na amfani da kajin da suka lalace suna sayarwa mutane. Rahoton yace matsin tattalin arziki da rashin kasuwa yasa dole wasu masu gasa kajin da nama na bakin titi suka daina kasuwancin. Inda wasu kuma a kokarin rage Asara da ci gaba da kasuwancin kamar yanda hausawa ke cewa da babu gara ba dadi ke siyo kajin da suka dade a ajiye suka fara lalacewa. Rahoton yace masu sayarwa da masu gasa kajin naman sukan ajiyesu a firjin ne, to dalilin rashin kasuwa, idan kajin suka dade ba'a siya ba sai su fara lalacewa har dandanonsu ya fara canjawa. Amma maimakon a yaddasu, saboda gudun Asara, sai a rika sayarwa da masu gasa naman irin wadannan kaji da suka fara lalacewa a farashi me sauki. Su ...
Ku daina baiwa Azzaluman shuwagabannin mu bashi>>NLC ta roki Bankin Duniya da IMF

Ku daina baiwa Azzaluman shuwagabannin mu bashi>>NLC ta roki Bankin Duniya da IMF

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta roki bankin Duniya da kungiyar bada lamuni ta Duniya, IMF da su daina baiwa mugayen shuwagabanni bashi. Kungiyar tace baiwa irin wadannan shuwagabannin bashi bashi da amfani dan kuwa tana kara rikita harkar mulki ne da kara jefa gwamnatocin wadannan kasashe cikin bashi da rashin ci gaba. Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ne ya bayyanawa hukumomin kudin na Duniya haka inda ya kuma gaya musu cewa shawarwari da suke baiwa Najeriya game da tattalin arzikinta na kara jefa kasar ne cikin talauci da rashin ci gaba. Joe Ajaero ya baiwa IMF da Bankin Duniyar shawarar cewa su daina bayar da shawarar tattalin arziki ga kasashe a dunkule, su rika bada shawarar da zata rika kawowa kowace kasa ci gaba.
Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata a Asibitin dake Kano

Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata a Asibitin dake Kano

Duk Labarai
Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata me shekaru 60 da haihuwa a Asibitin mahaukata dake Dawanau, Karamar hukumar Dawakin Tofa Kano. Matar me suna Talatu Ali an yi garkuwa da itane a yayin da take jiran ganin Likita. Dan matar da dan uwanta ne suka kai ta Asibitin, saidai a yayin da suma suke jiran layi ya zo kanta taga likita, sai suka nemeta sama da kasa suka rasa. Lamarin ya farune ranar February 19, 2025 da misalin karfe 8 na safe, saidai ranar February 21 da misalin karfe 7 na safe an kira danginta inda aka tabbatar musu da cewa an yi garkuwa da itane. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.