Thursday, December 18
Shadow
Anata ta cece-kuce saboda babu mace ko daya data halarci wajan sakawa kasafin kudin 2025 hannu da shugaba Tinubu yayi

Anata ta cece-kuce saboda babu mace ko daya data halarci wajan sakawa kasafin kudin 2025 hannu da shugaba Tinubu yayi

Duk Labarai
An fara cece-kuce saboda ba'a ga mace ko daya ba a wajan sakawa kasafin kudin shekarar 2025 hannu da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi. A jiya Juma'a ne dai shugaban kasar ya sakawa kasafin kudin na shekarar 2025 hannu. Hakan na zuwane yayin da ake ikirarin samar da daidaito ko Adalci tsakanin maza da mata wajan rike mukaman gwamnati da wakiltar jama'a. Shugaban ya sakawa kudirin dokar hannu ne a fadarsa dake Abuja, kuma bikin ya samu halartar Ministan Kudi, Wale Edun, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio, da takwaransa na Wakilai, Tajudeen Abbas da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila. A ciki kuma akwai Nuhu Ribadu wanda shine me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro da Ministan babban birnin tarayya, Nyesome Wike da sauransu. ...
Ina da kwararan shaidu cewa mijin ki mijin ki ɗan neman mata ne – Sanata Natasha ga matar Akpabio

Ina da kwararan shaidu cewa mijin ki mijin ki ɗan neman mata ne – Sanata Natasha ga matar Akpabio

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci Ekaette Akpabio, matar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ta send tsoma baki a batun zargin da ta ke yi wa mijin na ta na neman mata. A wata hira da aka yi da ita a tashar Arise a ranar Juma’a, Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta bayyana cewa Akpabio ya yi mata tayin lalata a ofishinsa da kuma gidansa da ke Akwa Ibom. Hakan ne ya sanya matar Shugaban Majalisar Dattawan, Ekaette, ta mayar da martani inda ta ce mijinta mutum ne mai kamun kai, kuma ta ce ikirarin sanatar “karya ne.” Ekaette ta kuma shigar da kara a kotu kan take hakki ta da ɓata suna da Akpoti-Uduaghan ke yi. A cikin wata wasika mai kwanan wata 1 ga Maris, da aka aikawa matar Shugaban Majalisar, sanatar, ta hannun lauyanta, Vict...
Sanata Natasha ta taba bani labari game da haduwarta da Sanata Akpabio a dakin Otal, saidai na mata gyara inda nace mata a ofis ake haduwa a yi aiki ba a otal ba>>Sanata Kingibe

Sanata Natasha ta taba bani labari game da haduwarta da Sanata Akpabio a dakin Otal, saidai na mata gyara inda nace mata a ofis ake haduwa a yi aiki ba a otal ba>>Sanata Kingibe

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Sanata me wakiltar babban birnin tarayya, Abuja, Ireti Kingibe ta bayyana cewa, sanata Natasha Akpoti kamar diya take a wajenta saboda tazarar shekarun dake tsakaninsu. Ta bayyana cewa a baya kamin dangantaka ta yi tsami tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Natasha, tafi kowace mace a majalisar samun damarmaki na ci gaba. Tace kuma ba Sanata Natasha Akpoti kadai aka canjawa wajan zama ba. Game da maganar zargin lalata da tawa Sanata Akpabio, sana Kingibe tace ita bata sa...
Dalla-Dalla: Sanata Natasha Akpoti ta fitar da kalaman batsa da Sanata Godswill Akpabio ya gaya mata bayan da ta je ofishinsa

Dalla-Dalla: Sanata Natasha Akpoti ta fitar da kalaman batsa da Sanata Godswill Akpabio ya gaya mata bayan da ta je ofishinsa

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ta bayyana kalaman batsa da Sanata Godswill Akpabio ya gaya mata bayan da ta je ofishinsa. Tace ta je ofishinsa ne dan jin ba'asin abinda yasa ba'a amincewa da kudirorin dokar da take kawowa majalisar inda ta bayyana cewa, kudirorin na da matukar muhimmanci a wajan jama'ar mazabarta. Tace tana mai magana kawai sai yace mata idan tana son kudirorin data kawo su wuce to sai ta yadda ta jiya masa dadi. Tace sai ta yi kamar bata ji ahinda yace ba ta ci gaba da maganarta, tace amma ya sake gaya mata cewa, zabi ya rage nata. Sanata Akpoti ta bayyana hakane a hirar da aka yi da ita a gidan talabijin na Arise TV inda ta zargi Sanata Akpabio da neman yin lalata da ita.
Duk da Alkawarin fara biyan matasa masu bautar kasa Naira 77,000, gwamnatin Tinubu ta saba Alkawarin

Duk da Alkawarin fara biyan matasa masu bautar kasa Naira 77,000, gwamnatin Tinubu ta saba Alkawarin

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta saba alkawarin data wa matasa masu bautar kasa, NYSC fara biyansu Alawus din Naira 77,000 a watan Fabrairu inda har yanzu ta ci gaba da biyansu Naira 33,000. Da yawan matasa masu bautar kasa da suka karbi alawus din nasu a daren ranar Juma'a sun bayyana ganin Naira 33,000 maimakon Naira 77,000 da aka musu Alkawari. Hakan ya sabawa maganar da shugaban hukumar ta NYSC, Brigadier General Yushau Ahmed yayi a watan Janairu da ya gabata inda yace maganar karin kudin tabbatacciya ce kawai ana jiran akincewa da kasafin kudin shekarar 2025 ne. Zuwa yanzu dai babu wani karin bayani kan lamarin daga gwamnati wanda hakan ya bar matasan cikin damuwa. Lura da yanda matsin tattalin arziki yayi yawa, Naira 33,000 babu inda zata kai matasan masu bautar kasa.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NATCA tace aiki ya mata yawa tana fama da matsanancin karancin ma’aikata

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NATCA tace aiki ya mata yawa tana fama da matsanancin karancin ma’aikata

Duk Labarai
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa, NATCA ta bayyana cewa aiki yawa ma'aikatanta yawa saboda karancin ma'aikata da hukumar ke fama dashi. Hukumar tace akwai bukatar a dauki ma'aikata musamman dan saukaka aikin hukumar. Shugaban kungiyar ma'aikatan hukumar, Mr Amos Edino ne ya bayyana haka inda yace aiki yanawa ma'aikatansu yawa wanda hakan yake sa su kasa kammala aikin yanda ya kamata. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a filin jirgi na Murtala Muhammad dake Legas. Yace a ka'ida, ma'aikatansu aikin awanni 2 kawai ya kamata su rika yi suna tashi kamin wani yazo ya karbeka, yace amma yanzu ma'aikatansu har aikin awanni 4 suna yi. Yace makarantar horas da matuka jirgin sama dake Zaria, NCAT dake da alhakin horas da irin wadannan ma'aikata itama tana fama da kar...
Duk namijin da ya ganni sai ya harba, saboda na hadu>>Inji ‘Yar Fim, Lydia Usang

Duk namijin da ya ganni sai ya harba, saboda na hadu>>Inji ‘Yar Fim, Lydia Usang

Duk Labarai
'Yar Fim din kudancin Najeriya, Lydia Usang ta bayyana cewa duk namijin da ya ganta sai sha'awarsa ta tashi saboda tsabar kyan da jikinta ke dashi. Ta bayyana hakane a hirar da jaridar Vanguard ta yi da ita inda tace maganar gaskiya Allah ya mata kyau, babi namijin da zai kalleta bai sake kallo ba. Saidai tace har yanzu bata da tsayayye abinda ta mayar da hankali akai shine aikinta na yin fim.
Sanata Akpabio ya zargi Sanata Natasha Akpoti da saka kaya masu shara-shara dake nuna surar jikinta da kuma yin kwaliyar data wuce kima

Sanata Akpabio ya zargi Sanata Natasha Akpoti da saka kaya masu shara-shara dake nuna surar jikinta da kuma yin kwaliyar data wuce kima

Duk Labarai
A ci gaba da dambarwar data kunno kai tsakanin kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti inda ta zargeshi da neman yin lalata da ita, Sanata Akpabio yace Akpoti na saka kaya shara-shara. Akpabio ya bayyana hakane ta bakin babban hadiminsa, Mfon Patrick wanda ya rubuta a shafin Facebook cewa, Sanata Natasha Akpoti ta sha aikin sanata shine yin kwalliya a koda yaushe da kuma saka kaya masu shara-shara dake nuna tsiraici. saidai lauyan Sanata Natasha Akpoti, Victor Giwa ya shigar da kara kotu akan lamarin inda yake karar hadimin na Akpabio Patrick da shi Akpabio din da kansa inda yace wadannan kalamai sun zubarwa da wadda yake wakilta mutunci a idon jama'a.
Da Duminsa: ‘Yan Bìndìgà sun sako janar Maharazu Tsiga

Da Duminsa: ‘Yan Bìndìgà sun sako janar Maharazu Tsiga

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan Bindiga da suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar bautar kasa, Janar Maharazu Tsiga sun sakoshi. An sakoshi ne bayan shafe kwanaki 22 a hannun masu garkuwa da mutanen, Rahoton yace wata majiya tace an sakoshi kuma yana wani asibiti da ba'a bayyana sunansa ba yana jinya. A ranar 6th February 2025 ne 'yan Bindigar suka dira a gidansa suka yi garkuwa dashi tare da jikkata mutane 2 sannan daya daga cikin 'yan Bindigar ya mutu bayan da wani dan Bindigar ya harbeshi bisa kuskure. A baya dai hutudole ya jiyo cewa 'yan Bindigar sun nemi kudin fansa Naira Miliyan 250 kamin sakin tsohon sojan. Saidai zuwa yanzu hukumomin tsaro a jihar basu ce uffan ba kan lamarin.