Monday, December 15
Shadow
Kalli Bidiyo: Dan Siyasar APC ya sha Ihun bama so sannan aka koreshi a jihar Katsina bayan da ya je yakin neman Zabe

Kalli Bidiyo: Dan Siyasar APC ya sha Ihun bama so sannan aka koreshi a jihar Katsina bayan da ya je yakin neman Zabe

Duk Labarai
Shugaban kungiyar shuwagabannin kananan hukumomi ta Najeriya kuma shugaban karamar hukumar Kaita, Bello Lawal 'Yandaki wanda dan Jam'iyyar APC ne ya sha ehon bama so sannan aka koreshi daga kauyen 'Yanhoho bayan da ya je yakin neman zabe. Bello ya je yakin neman zabe ne a karo na biyu kauyen saidai ya gamu da fushin jama'ar yankin inda suka taru suka fasa masa gilasan mota sannan suka koreshi suna yi masa ihu. A bidiyon da ya watsu sosai a kafafen sadarwa, an ga matasan 'yanhoho da itace suna ihun basa so da sauransu. Kalli bidiyon anan
Fina-Finan da ‘yan Najeriya ke kallone yasa mutane da yawa ke son yin kudi dare daya>>Inji Matar Shugaban kasa, Remi Tinubu

Fina-Finan da ‘yan Najeriya ke kallone yasa mutane da yawa ke son yin kudi dare daya>>Inji Matar Shugaban kasa, Remi Tinubu

Duk Labarai
Matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta bayyana cewa, fina-finan Nollywood da kafafen sada zumunta da 'yan Najeriya ke ta'ammuli dasu ne ke zuga da wa wajan son yin kudi dare daya. A cikin abubuwan da take suna zuga mutane dan neman kudin dare daya hadda Addini. Tace Hakan ne ma yake sa ake safarar mutane inda tace tana baiwa hukumar hana safarar mutane gwarin gwiwa akan aikin da take. Ta bayyana hakane yayin da shugabar NAPTIP Binta Bello ta kai mata ziyara a ofishinta dake fadar shugaban kasa a Abuja. Me taimakawa matar shugaban kasar ta bangaren yada labarai, Busola Kukoyi ce ta bayyana haka a wata sanarwa data fitar inda tace Matar shugaban kasar ta bada shawarar a rika karfafa mutane dan su rika yin aiki tukuru da kuma hakuri da rayuwa.
Wanda suka yi Gàrkùwà da janar Tsiga a Katsina sun nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan dari biyu da hamsin(250m)

Wanda suka yi Gàrkùwà da janar Tsiga a Katsina sun nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan dari biyu da hamsin(250m)

Duk Labarai
' Yan Bindigar da suka yi garkuwa da tsohon janar din soja kuma tsohon shugaban hukumar bautar kasa(NYSC) Janar Maharazu Tsiga rtd sun nemi a biya Naira Miliyan 250M a matsayin kudin fansarsa. Wata majiya dake kusa da iyalan janar dinne suka bayyana hakan inda suka ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan janar din suka sanar da hakan. An yi garkuwa da janar tsiga ne tare da wasu mutane 9. Lamarin ya faru ranar Laraba da dare inda 'yan Bindiga su kusan 100 suka zagaye gidansa suka tsafi dashi. Dan majalisar tarayya dake wakiltar Bakori da Danja ya tabbatar da faruwar lamarin saidai zuwa yanzu hukumomin soji dana 'yansanda basu bayar da ba'a si ba kan lamarin.
An gurfanar da tsohon Minista kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Kabiru Turaki a kotu bisa zargin yin lalata da wata mata har ta kai ga ya dirka mata ciki

An gurfanar da tsohon Minista kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Kabiru Turaki a kotu bisa zargin yin lalata da wata mata har ta kai ga ya dirka mata ciki

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an gurfanar da tsohon Ministan ayyukan na musamman Kabiru Turaki (SAN) a kotun magistre dake Abuja bisa zargin yin lalata da wata mata. Saidai Turaki ya musanta zargin da ake masa bayan da aka karanto masa zarge-zargen a gaban me shari'a, Abubakar Jega. An zargi ministan da cewa a tsakanin watan Disamba na shekarar 2014 zuwa watan August na shekarar 2016 ya kai wata me suna  Ms. Hadiza Musa wani otal me suna Hans Palace inda yayi lalata da ita. Ya kuma sake yin lalata da matar a otal din Ideal Home Holiday dake Asokoro tsakanin watan August 2016 zuwa watan November 2021. Daga baya ma sai ya kama mata gida dake da adireshin at No. 12 Clement Akpagbo Close, Gauzape inda ya ci gaba da lalata da ita da sunan cewa ya aureta. A ...
Maganar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ba gaskiya bane>>Inji Gwamnatin Tarayya

Maganar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ba gaskiya bane>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Ma'aikatar ilimi ta tarayya, ta bayyana cewa, Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya bada shawarar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ne amma bai ce an canja ba. Sanarwar tace maganar canja tsarin kai tsaye ba gaskiya bane. Me magana da yawun ma'aikatar Ilimin, Folasade Boriowo ta bayyana cewa, kwamitin Ilimi na kasa zai duba wannan shawara kamin sanin matakin da ya kamata a dauka na gaba. Ministan ya bayar da wannan shawara ne a Abuja ranar 6 ga watan Fabrairu a wajan wani taro kan Ilimi da aka yi a Abuja.
DA DUMI DUMINSA: fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al’ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu

DA DUMI DUMINSA: fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al’ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu

Duk Labarai
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al'ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu. Fadar shugaban ƙasa tace Sama da Mutanen Arewa Miliyan 60 Sun nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu, da Wasu da Kungiyoyi ga tuntuba ta matasan Arewa ta wakilta, sun bayyana Goyon bayansu ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Sun jaddada cewa "goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Akpabio suna mai cewa "shugabannin biyu daga Kudu sun goyi bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban ƙasa da Shugaban majalisar Dattawa, kuma hakan ya dace a gare mu. don rama wannan gudummawar da suka ba...
Ministar da Tinubu ya sauke ta koma yin Fim

Ministar da Tinubu ya sauke ta koma yin Fim

Duk Labarai
Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta dawo masana’antar Nollywood tare da sabon fim dinta mai suna “Hatred”. Fim ɗin, wanda ita ce ta shirya, ya kasance alamar dawowarta a hukumance cikin masana'antar bayan tsawon lokacin da ta yi a harkar siyasa. An naɗa Kennedy-Ohanenye a matsayin ministan Shugaba Bola Tinubu a ranar 21 ga Agusta, 2023, amma aka tsige ta daga mukaminta a ranar 23 ga Oktoba, 2024, tare da wasu ministoci hudu. VANGUARD ta rawaito tun bayan barin ta ofis, matar mai shekaru 51 ta koma mayar da hankali kan harkar shirya fina-finai da fasaha.
Da Duminsa: Kamfanin Wutar Lantarki sun janye yajin aikin da suke a Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi

Da Duminsa: Kamfanin Wutar Lantarki sun janye yajin aikin da suke a Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin wutar lantarkin dake kula da wutar lantarki ta Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto dake yajin aiki sun janye yajin aikin nasu da ya kwashe kwanaki biyar suna yi. Ma'aikatan kamfanin wutar sun janye yajin aikinne bayan da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya shiga tsakani. Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda ya tabbatar da cewa, an janye yajin aikin.
Komai ya tafi daidai a Gwamnatina>>Tsohon Shugaban kasa Buhari ya bugi kirji

Komai ya tafi daidai a Gwamnatina>>Tsohon Shugaban kasa Buhari ya bugi kirji

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya bayyana cewa a zamanin mulkinsa abubuwa sun tafi yanda ya kamata. Ya bayyana hakane a gawarsa da wasu 'yan jarida da suka kai masa ziyara a Daura. Yace abubuwan ci gaba da ya kawo a zamanin mulkinsa za'a dade ana amfana dasu a Najeriya. Shugaban ya bayyana cewa, a shekarar 2015 da ya karbi mulki, ya gaji matsaloli da yawa daga gwamnatin Jam'iyyar APC wanda suka hada dana rashin tsaro, matsalar tattalin arziki da sauransu.
Amurkawa na zuwa Asibitocin Najeriya neman magani>>Inji Gwammatin Tarayya

Amurkawa na zuwa Asibitocin Najeriya neman magani>>Inji Gwammatin Tarayya

Duk Labarai
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, an samu ci gaba sosai a Najeriya musamman ta fannin lafiya inda yace 'yan kasar Amurka na zuwa Najeriya neman magani. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da wata kungiyar Likitocin da suka kai masa ziyara a Abuja fadar shugaban kasa. Yace kwanannan wasu marasa lafiya daga kasar Amurka su 13 suka zo Asibitin Zenith Medical and Kidney Centre aka musu dashen koda kuma an samu nasarar yin aikin. Yace kuma sun samu aikin a farashi me sauki kasa da yanda ake yinsa a kasar ta Amurka. Mataimakin shugaban kasar ya kuma jinjinawa shugaban Asibitin me suna Dr. Olalekan Olatise inda yace gwarzo ne wajan kula da lafiya. Saidai ya koka game da yanda 'yan Najeriya da yawa ke fama wajan aikin Koda saboda tsadarsa inda yace wasu na dog...