Gwamnonin APC Da Jiga-Jiganta Sun Amince Tinubu Ya Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2027
Sun bayyana hakan ne a yayin da taron da suka gudanar a Abuja a yau Alhamis.
Me za ku ce?
Wannan matashiyar ta bayyana cewa, bayan ta kammala karatu na tsawon shekaru 5 yanzu tana bukatar aure.
https://twitter.com/mariyaalqibty/status/1925151480564039902?t=rgC1OREd5-EsZfyIh2U0EQ&s=19
Da yawa sun tayata Murna.
Rahotannin da muke samu na cewa, matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashin man fetur dinta.
Matatar tace a yanzu a Legas za'a rika sayar da man fetur din akan Naira N875 kan kowace lita sai kuma a kudu maso yamma za'a rika sayar da man nasu akan Naira N885 kowace lita.
A Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya kuwa za'a rika sayar da man fetur din ne akan Naira N895 duk lita.
Hakanan tace a jihohin Kudu maso gabas da kudu maso kudu kuma za'a rika sayen man fetur din akan Naira N905 kowace lita.
Matatar tace za'a samu man fetur din a wannan farashin a gidajen mai abokan hildarsu, wanda suka hada da MRS, AP, Heyden, Optima, TechnOil, da Hyde.
Wannan Bidiyon wata matace da take kuka tana nuna yanda aka wulakantata a gidan haya aka jefo mata kayanta waje.
https://www.tiktok.com/@diornuelqueen3thiftbags/video/7506431667964251398?_t=ZM-8wZ4WHzs6C6&_r=1
Lamarin dai ya baiwa da yawa tausai inda aka rika mata fatan Alheri.
Wannan matar ta dauki hankula sosai a kafafen sadarwa bayan da ta yi zargin cewa, mijinta ya gallaza mata.
Tace abinda ba zata taba mantawa dashi ba shine mahaifinta ya rasu amma ya hanata ta je jana'iza.
Kalli Cikakkiyar hirar da aka yi dashi:
https://www.tiktok.com/@bcrw.social.spotlight/video/7506277106347822392?_t=ZM-8wYy46Fya0c&_r=1
Labarin nata dai ya zowa mutane kamar Almara inda akai ta mamaki.
Gwamnatin tarayya ta koka da cewa, Kaso 85 na daliban Najeriya da take daukar nauyinsu dan zuwa kasashen waje su karo ilimi da zummar su dawo dan ciyar da Najeriya gaba, basa dawowa.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da ya wakana a Legas.
Yace dalilin haka yasa suka canja lissafi domin sun gano cewa yawanci karatun da ake daukar nauyin daliban su je su yi a kasashen da suka ci gaba, za'a iya yinsa a Najeriya.
Yace dan hakane suka mayar da hankali wajan karfafa harkar ilimin a Najeriya inda yace sun bude cibiyoyin bincike da zurfafa ilimi a jami'o'i daban-daban na kasarnan.
Bayan tserewar masu laifi daga gidan yarin Ilesa na jihar Osun su 7 ranar Talata, an gano cewa akwai masu laifi 2000 da suka tsere daga gidajen yari daban-daban na Najeriya da ake nema ruwa a jallo.
Haka na zuwane wata daya kacal bayan da masu laifi 12 daga gidan yari me suna Katon Karfe suka tsere daga jihar Kogi.
A shekarar 2024 ma dai an samu tserewar masu laifi daga gidan yarin MCC dake Suleja jihar Naija inda masu laifi 118 suka tsere amma guda 23 ne kawai aka samu damar sake kamowa.
Hakan na zuwane yayin da laifuka da kashe-kashen da ayyukan ta'addanci suka yi yawa a Najeriya.
Rahoton yace zuwa yanzu akwai jimullar masu laifi 2000 da suka tsere daga gidajen yarin Najeriya daban-daban.
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta JAMB zata sake shiryawa daliban da suka yi fashi basu samu damar rubuta jarabawar ba.
Shugaban hukumar, ta JAMB Prof. Is-haq Oloyede ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Yace hukumar zata shiryawa kaso 5.6 na daliban da basu samu damar rubuta jarabawar ba.
An dai zargi JAMB din da saka lokaci wanda yayiwa dalibai wahalar iya zuwa wajan jarabawar akan kari.
Rahotanni na kara bayyana dake tabbatar da alaka me karfi tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi ta kullu.
Rahotannin sun ce, duka bangarorin sun saka hannu a wata yarjejeniya da suka akince da ita.
A tafiyar dai akwai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da sauransu.
Hakanan rahoton yace sun kuma amince da komawa jam'iyyar ADC da kuma saka kudi dan gyara jam'iyyar.
Saidai duk da El-Rufai shi yana SDP ne, rahoton yace da zarar an kammala shirya komai, za'a sanar da kulla alaka tsakanin SDP da ADC din.
A bangaren APC kuwa, sakataren jam'iyyar Ajibola Basiru ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu shine uban hada kan al'umma kuma suna da yakinin shi zai lashe zaben shekarar 2027.
Rahotanni daga babban birnin kasar Amurka, Washington DC na cewa an kashe ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Israela 2.
An bayyana lamarin da cewa Kiyayya ce ga Yahudawa.
Wani rahoto yace maharbin yayi ihun cewa a kyale Falasdinawa kamij ya kashe mutanen.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana Allah wadai da lamarin inda yace irin wannan lamari bashi da mazauni a kasarsu.