Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai – Kocin Arsenal
Mun fi kowacce ƙungiya ƙoƙari a gasar zakarun turai - Kocin Arsenal.
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ƙungiyar tasa ce ta fi kowacce ƙoƙari a gasar zakarun Turai ta Champions League ta bana duk da kashin da suka sha a hannun Paris St-Germain.
BBC Hausa ta rawaito cewa Arsenal ɗin ta je filin wasa na Parc des Princes ne da zimmar rama ƙwallo ɗaya da aka zira mata a gidanta a wasan farko domin kaiwa wasan ƙarshe na gasar.
Sai dai duk da damarmakin da suka ƙirƙira, 'yanwasan Arsenal ɗin ba su iya yin nasara ba.
Ƙwallayen da Fabian Ruiz da Achraf Hakimi suka ci ne suka taimaka wa PSG din, inda har sai a minti na 76 Bukayo Saka ya farke wa Arsenal ɗaya, inda wasa ya tashi 3-1 gida da waje.
"Saura ƙiris, ƙiris ya rage mu sauya sakamakon wasan, amma kuma aka fitar da mu," a cew...








