Wednesday, July 1
Shadow
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci

Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci

Duk Labarai
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci. Shahararriyar Manhajar haƙo sulalla ta Tapswap ta hanyar TON Blockchain ta ce ta jinkirta ranar bajakolin kasafin sulalla ga masu amfani da shi zuwa wani lokaci da ba su sanar ba, yayin da ma'aikantan su ke kokarin neman karin hanyoyin da za su inganta shi domin amfanar mutane da yawa. Shugaban sashen sadarwa na Tapswap John Robbin ne ya bayyana hakan a dandalin sadarwarsa na X ranar Laraba. Dandalin wanda ke buƙatar masu amfani da shi da su rika danna alamar da ke tsakiyar manhajar Tapswap a Telegram don hakar sulalla a kwanan nan ya samu karbuwa a tsakanin 'yan Najeriya inda suke duƙufa wajen latsa fuskar wayarsu don neman kudi, kuma ya tara mutane sama da Miliyan 50 tun bayan da aka kaddamar da shi a ranar 15 g...
Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Siyasa
Lauyoyin jagoran ƙungiyar Ipob mai rajin kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu sun bayyana cewa akwai yiwuwar su tuntuɓi gwamnati domin neman sasanci a wajen kotu game da shari'ar da ake yi masa. Ana tuhumar Nnamdi Kanu ne da laifukan da suka jiɓanci ta'addanci a matsayinsa na jagoran ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta Ipob. Ƙungiyar na ƙoƙarin ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya ɓalle ne tare da kafa ƙasa mai zaman kanta. Tuntuni gwamnatin Najeriya ta ayyana ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda. Aloy Ajimakor, wanda shi ne jagoran lauyoyin da ke kare Kanu, ya shaida wa kotu cewa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar da ta kafa Babbar kotun tarayya sun bayar da damar sasantawa a wajen kotu kan duk wani rikici tsakanin mutum da mutum ko kuma wani mutum da gwamnati. Sai ...

Allah Sarki: Ji yanda auren wata mata ya mutu saboda kissar kishiya

Abin Mamaki, Auratayya
Wata baiwa Allah da labarinta ke cike da ban tausai ta bayyana yanda aurenta ya mutu saboda kissar Kishiya. Ta bayyana hakane a zauren yanar gizo na Arewa up. Ga dai yanda labarin yake kamar yanda ta badashi: Ta fara shimfida kamar haka: "yadda aure na ya mutu assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh yadda aure na na biyu ya mutu a silar kissar kishiya a gaskiya maza idan kunsan Baku Isa da matanku na gida ba kudaina yinkurin Kara aure sbd ku kanku Baku Isa kuce ba bare Kuma mu da aka aura" Ta ci gaba da bayar da labarin kamar haka: "wallahi na fada Miki bansan me ya faru ba Kinga an kaini gidansa ranar Friday to Kuma Daman gaskiya kamar Yana tsoron matar tasa to kwana na uku muka fara rabon kwana to yaje yayi mata kwana 2 ya dawo yayimun kwana 2 ya koma gidanta to wa...

Ana warkewa daga ciwon hanta

Ciwon hanta
Ana warkewa daga mafi yawan cutar hanta da aka saba da ita a tsakanin al'umma saidai akwai kalar wadda ba' warkewa daga ita saidai ai ta kokarin shan magani. Yawanci ba'a cika ganin alamun cutar hanta ba, fara maganin cutar da wuri na da matukar amfani saboda idan hantar ta riga ta tabu, magani bai cika yin tasiri ba. Akwai matakai 3 na ciwon hanta kamar haka: Hepatitis: Wannan shine matakin farko da hanta ke fara kumbura saboda wata cuta data sameta ko kuma ta kasa yakar wata cuta data shigeta. Daga wannan matakine cutar ke tsallakawa zuwa matakin Fibrosis. Fibrosis: A wannan matakine hanta zata fara tsotsewa tana kankancewa, jini zai daina zuwarwa hantar, sannan kuma iska ma zai daina zuwar mata yanda ya kamata kuma zata rasa sauran sinadarai masu amfani. A wannan matakine h...

Kalli Bidiyo yanda maza ke shiga bayin mata har aka kama wasu suna Ziynaa a kasar Saudiyya

Abin Mamaki
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Abdallah Gadon kaya ya bayyana cewa abinda wasu alhazai suke yi basa kyautawa. Ya bayyana hakane a wajan wata lacca da yakewa Alhazai. Yace akwai shekarar da aka kama wata Hajiya da Alhaji suna Zina a ban daki. https://twitter.com/northern_blog/status/1802852561243763053?t=ljzVQvW8WdUKMMb5XTo0Mg&s=19 Hakanan yace yanzu haka ana samun maza suna shiga ban dakin mata sa sunan wai sun matsu, musamman da dare.