Saturday, December 13
Shadow
An kaiwa Tawagar Hadimar Gwamnan Kaduna hari

An kaiwa Tawagar Hadimar Gwamnan Kaduna hari

Duk Labarai
Hadimar gwamnan jihar Kaduna dake bashi shawara akan harkokin siyasa, Hon. Rachael Averik ta tsallake rijiya da baya a yunkurin kisheta da aka yi. An kaiwa tawagar Hon. Rachael Averik harin kwantan baunane ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu. Harin ya farune a tsakanin kauyukan Tsauni Majidadi da Gani dake karamar hukumar Sanga ta jihar. A ranar tana kan hanyar zuwa Gwantu ne abin ya faru. A ranar taje gaisuwane sannan ta kaddamar da Asibitin da Alhaji Muhammad Umar Numbu ya gina a masarautar Arak. Jami'an tsaron dake tare da ita sun budewa maharan wuta inda anan aka jikkata direbanta da Dansanda daya. Jami'an tsaro a jihar sun fara bincike kan lamarin. Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da harin.

Maganin hana karyewar gashi

Magunguna
Abubuwan dake haddasa Karyewar gashi sun hada da yawan damuwa, zafi, ciwo me tsanani irin su ciwon suga, hawan jini da sauransu. A wannan rubutu zamu yi cikakken bayani game da karyewar gashi da maganin hana karyewar gashi. Bushewar gashi da barinshi ba gyara ma yana sawa ya rika kakkaryewa. Ga cikakken bayani kamar haka game da abubuwan dake kawo karayar gashi: Abinci: Kalar abincin da ake ci na taimakawa matuka wajan kyawun gashi da kuma hana karyewarsa. Kalar abincin dake taimakawa wajan hana karyewar gashi sune, dafaffen kwai, gasashshiyar kaza, ganye irin su kabeji, dodon kodi, madara, da Yegot. Yawan Damuwa: Kasancewa cikin yawan damuwa na sanya karyewar gashi. Dan haka, masana sun bada shawarar a rika cire kai daga cikin damuwa dan samun gashi me kyau da baya karyewa....
Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa’ad Abubakar

Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa’ad Abubakar

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa'ad Abubakar Wace fata za ku yi mata?
Bayyana Kyautar Motar Da Yara ‘Ýan Maťàñ Nan Śuke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Źuwa Ýi Ake Ba Šu Motar

Bayyana Kyautar Motar Da Yara ‘Ýan Maťàñ Nan Śuke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Źuwa Ýi Ake Ba Šu Motar

Duk Labarai
Daga Jamila Ibrahim Ni Wallahi yaran nan da ake bawa mota fitowa da suke yi suna nunawa ya fi illa akan abinda suke zuwa ýi ake ba su. Yanzu sun yi influencing yara kanana na ťìķțok har ya kai ga burin yarinya kawai ta yi ìşķançì a ba ta kudi, yara sun fara fandarewa. In an basu suyi hakuri su daina zuwa suna posting don yadawa duniya. Ku kuma 'yan mata da kuke kallon wadanda ake bawa gida da mota as role model har suke burge ku ku sani ba haka kawai ake ba su kudin ba, wani abun ya wuce kudin da saurayi zai bawa budurwa sabida soyayya ko sabida ya yi źìñà da ita, yawanci kudin ķùñģiya ce, bayan wasu shekaru za a a nemi wadanan dukiyar a rasa ka zama abun tausayi. Zan iya misalai da 'yan fim dayawa wadnda ma suka tare kasar waje suka yi suna, suka yi kudi amma karshen su yan...
Wata cuta data bullo ta yi sanadiyyar kwantar da mutane dubu biyar a Asibiti

Wata cuta data bullo ta yi sanadiyyar kwantar da mutane dubu biyar a Asibiti

Duk Labarai
Mutane sama da dubu biyar ne aka kwantar a Asibiti a kasar Ingila biyo bayan bullar wata cutar mura. Mutanen sun kamu da cutar ne a makon karshe na shekarar 2025 inda gadaje suka yi kadan a Asibiti sai da aka samar sa sabbin gadaje na gaggawa 1,300. An dai bayyana sunan cutar da norovirus and Respiratory Syncytial Virus (RSV) kuma yawan masu kamuwa da ita din sun fara karuwane daga ranar Kirsimeti. Daraktan hukumar kula da lafiya ta kasar, Julian Redhead ya bayyana cewa, abin damuwa ne ganin cewa mutane 5000 ake kwantara kullun a Asibiti sanadiyyar cutar. Yace kuma nan gaba lamarin zai kara munana saboda ana tsammanin sanyi ya karu. Yayi kira ga mutane su dauki matakan baiwa kansu kariya.
Gwamnatin Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti

Gwamnatin Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti

Duk Labarai
Hukumar karɓar haraji ta jihar Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti da nufin inganta harkokin tsaro. Hukuma ta ce za a yi hakan ne kuma don ƙara yawan kuɗaɗen shiga da ake samu. Yanzu dai za a sauya wa motocin haya da keke-NAPEP launi domin a bambance tsakanin ababen hawa na haya da kuma waɗanda ba na haya ba. Launin ja ko tsanwa. Hon Moses Abeh wanda ya wakilci gwamnatin jihar a taron kaddamar da tsarin, ya ce an ɗauki aniyar yin tsarin ne domin samar da lambobin tsaro da kume fentin ga direbobi domin kare kai daga ɓata-gari da ake kira 'One Chance'. "Lambar tsaron zai kunshi bayanan direba da suka haɗa da wajen da mutum ya fito da kuma inda yake zama," in ji Moses. Ya kuma ce dole sai an san ƙungiya da direba ke ciki domin kaucewa sajewa da ɓata-g...
Rikicin kabilanci ya janyo mùtùwàr mutum tara a Jigawa

Rikicin kabilanci ya janyo mùtùwàr mutum tara a Jigawa

Duk Labarai
Wani rikici da aka danganta da kabilanci wanda ya barke tsakanin kauyukan Gululu da 'Yan-Kunama a jihar Jigawa, ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla tara. Rikicin ya samo asali ne sakamakon zargin da aka yi wa wasu matasan Fulani da ɓalle wani shagon kayan masarufi, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki. Sai dai zuwa yanzu, an samu nasarar shawo kan rikicin wanda kuma ya janyo asarar gidaje da dama. Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ta Jigawa, DSP Lawan Shi'isu Adam, ya shaida wa BBC cewa tuni aka aika jami'an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar zuwa yankin domin kwantar da hankali. "Za mu gudanar da bincike don ganin an kama waɗanda suka aikata wannan laifi da kuma hukunta su," in ji DSP Lawan. Ya ce hankali ya fara kwanciya a garuruwan kuma jami'an ...
Yanzu-Yanzu: Yanzu muke samun Labarin Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya karbi Katin jam iyyar PDP a mazabarsa dake unguwar Sarki Kaduna

Yanzu-Yanzu: Yanzu muke samun Labarin Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya karbi Katin jam iyyar PDP a mazabarsa dake unguwar Sarki Kaduna

Duk Labarai
Rahotanni na yawo a kafafen sada zumunta cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya koma Jam'iyyar PDP. Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da muka samu daga PDP ko kuma shi El-Rufai data tabbatar da hakan amma maganar nata kara yaduwa a kafafen sada zumunta. Da zarar mun samun karin bayani akan hakan, zamu sanar daku..... Yanzu muke samun Labarin Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya karbi Katin jam iyyar PDP a mazabarsa dake unguwar Sarki Kaduna! Ku biyomu don kawo cikakken labarin.