Monday, December 15
Shadow
Za mu fitar da Afirka da ga talauci, in ji Tinubu

Za mu fitar da Afirka da ga talauci, in ji Tinubu

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu, a yau Talata ya ce shugabannin Afirka za su ci gaba da jajircewa wajen fitar da al’ummarsu daga kangin talauci da gina tattalin arzikinsu a matakan da su ka dace. Tinubu, wanda ya kasance babban bako na musamman, ya bayyana haka ne a wajen rantsar da shugaba John Mahama a birnin Accra na kasar Ghana. “Ba mu da wani abin da za mu tabbatar wa kowa sai kanmu. Mun sami hanya mai mahimmanci don samun nasarar mu. Za mu fitar da al'ummarmu daga kangin talauci, mu gina tattalin arziki mai dorewa a kan kan mu. "A yau, na zo nan ba kawai a matsayina na shugaban Najeriya ba, har ma a matsayina na dan Afirka mai cikakken goyon baya ga Ghana da mutanenta," in ji Tinubu
Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Najeriya – Akintoye

Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Najeriya – Akintoye

Duk Labarai
Shugaban Ƙungiyar Ƙudirin samar da 'Yancin Kai ta Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta janye daga neman kafa ƙasar Yarabawa ba. A cewar Akintoye, kimanin Yarabawa miliyan 60 ciki har da mazauna gida da 'yan ƙasashen waje, suna goyon bayan ƙudirinsa na kafa ƙasar Yarbawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Da ya ke tattaunawa da jaridar The PUNCH a jiya Litinin, Akintoye ya ce, “Ba za mu koma baya ba. Dole ne mu fice daga Najeriya, ko kuma ƙasarmu za ta shiga matsala. “Ba kwa jin muryar mu a tituna? Ƙasar Yarabawa yanzu, babu gudu ba ja da baya. “Muna nufin Yarabawa da ke Nijeriya, kusan mutane miliyan 55 zuwa 60. Muna so mu kafa ƙasa ta kanmu. Ba za a samu Najeriya ba idan muka kafa ƙasarmu. Amma idan sauran suna son ci gaba da kasancewa a matsay...
Nijeriya Ta Yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu

Nijeriya Ta Yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu

Duk Labarai
Najeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike gibin da take samu wajen hako mai wanda Kungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana. Wannan shinekaron farko cikin shekaru hudu da Najeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya suka fuskanta Wasu alkaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara. A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Najeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a kowace rana, sai dai ƙungiyar ta rage wannan adadi zuwa milyan 1.5 sakamakon gazawar Najeriya na cike giɓin da take samu wajen haƙar man ta dalilin matsalolinta na cikin gida, hakan ya janyo wa kasar koma-baya a ba...
Akan Bashin Naira Dubu 300 Da Ake Binsa, Kotu Ta Siyar Da Gidansa Na Kusan Milyan 20 A Naira Milyan Biyu A Kano

Akan Bashin Naira Dubu 300 Da Ake Binsa, Kotu Ta Siyar Da Gidansa Na Kusan Milyan 20 A Naira Milyan Biyu A Kano

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Malam Surajo Yarima ya ce a lokacin da aka kai karar kotu ya samu karaya ne inda yake jinya a jihar Adamawa, kuma ya nuna musu hotunan lokacin da yake jinya domin su zama hujja, amma duk da haka ba a karbi uzurinsa ba. Ya ce yanzu haka an watsar da kayan su waje, inda ba su wajen kwana duk da cewa yana mata da hara tara. Don haka ne Yarima ya roki gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kai masa ɗauki domin shiga lamarin.
A Titi Muke Kwana Ni Da Mahaifiyata Saboda Otal Din Da Muke Kwana Kudinmu Ya Kare Har An Kwace Mana Jakunkunanmu Saboda Suna Bin Mu Ba Shi, Inji Iyalan Marigayi Tsohon Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero

A Titi Muke Kwana Ni Da Mahaifiyata Saboda Otal Din Da Muke Kwana Kudinmu Ya Kare Har An Kwace Mana Jakunkunanmu Saboda Suna Bin Mu Ba Shi, Inji Iyalan Marigayi Tsohon Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A Titi Muke Kwana Ni Da Mahaifiyata Saboda Otal Din Da Muke Kwana Kudinmu Ya Kare Har An Kwace Mana Jakunkunanmu Saboda Suna Bin Mu Ba Shi, Inji Iyalan Marigayi Tsohon Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero Ko a kwanakin baya dai Zainab ta koka kan yadda iyalan marigayi tsohon Sarkin suka yi watsi da ita da mahaifiyarta duk da cewa mahaifina nata ya ce su kula da ita da mahaifiyarta ko bayan ransa. Me za ku ce?
Wallahi Mutuwar Aure Bàlà’ì Ne Ga Mata, Ko Da A Ce Mijìnki Dukanki Yake Gwamma Ki Yi Hakuri Ki Zauña, Inji Mansura Isah

Wallahi Mutuwar Aure Bàlà’ì Ne Ga Mata, Ko Da A Ce Mijìnki Dukanki Yake Gwamma Ki Yi Hakuri Ki Zauña, Inji Mansura Isah

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, wadda tsohuwar matar Sani Musa Danja ce, ta bayyana hakan cikin wani bidiyo da ta wallafa. A cikin bidiyon ta bayyana yadda mata ke shiga mawuyacin hali bayan mutuwar aurensu. Ta shawarci mata da su kasance masu haƙuri a gidajensu na aure tare da gujewa duk wani abu da ka iya kawo musu ɓaraka da mazajensu. Ta yi gargaɗin cewa babu komai a rayuwar zawarci sai tarin baƙin ciki da da-na-sani. Me za ku ce?
Tsaffin sojoji da suka yi ritaya sun yi zanga-zangar rashin biyansu albashi

Tsaffin sojoji da suka yi ritaya sun yi zanga-zangar rashin biyansu albashi

Duk Labarai
Tsaffin sojoji da suka yi ritaya ranar Talata sun kai kujeru da rumfa a kofar fishin ma'ikatar kudi dake Abuja inda suka yi zaman dirshan suka bukaci a biyasu hakkokinsu. Dama dai a watan Disamba daya gabata, sojojin sun yi irin wannan zanga-zanga ta neman hakkinsu. Watanni da yawa sun shude inda ake gayawa tsaffin sojojin cewa, babu kudin da za'a biyasu hakkokin nasu. Bayan zanga-zangar da suka yi a watan Disamba, an biyasu kaso 50 cikin 100 na hakkokin nasu inda aka musu alkawarin biyan suran amma sunce har yanzu shiru.
Ana barazana ga rayuwata – Obi

Ana barazana ga rayuwata – Obi

Duk Labarai
Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sukar gwmnatin Shugaban Ƙasa Tinubu da ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara. A saƙon nasa na sabuwar shekarar, Obi ya bayyana cewa Najeriya na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ingantaccen kiwon lafiya. A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce, "shin na wuce iyaka? na yi wannan tambayar ce saboda ana yi wa rayuwata da ta iyalina barazana saboda jawabin da na yi na sabuwar shekara. Bayan barazanar kuma, wani mai suna Mr Felix Morka ya zarge ni da wuce iyaka, sannan ya yi barazanar zan ɗanɗana kuɗata," in ji shi. Obi ya ƙara da cewa idan har da gaske ya karya doka, a nuna masa, inda ya ƙara da cewa, "amma ba zan daina faɗin ga...
Aƙalla mutum 95 sun ràsù a girgizar ƙasa a China

Aƙalla mutum 95 sun ràsù a girgizar ƙasa a China

Duk Labarai
Wata mummunar girgizar ƙasa ta afku a kusa da iyakar Tibet da Nepal. Aƙalla mutum 95 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan sama da 130 sun jikkata a girgizar, wadda ta afku a ranar Talata. Girgizar ta kuma ƙetara zuwa yankin Nepal da ke ƙasar Indiya, wanda ke maƙwabtaka da Tibet na ƙasar China. Girgizar ƙasar ta lalata gine-gine a birnin Shigatse na Tibet, lamarin da ya sa jama'a su riƙa kwararowa kan tituna domin tsira. Tuni sojojin ƙasar suka fara aikin ceto, inda suka aika jirage marasa matuƙa zuwa wani yanki mai nisa a kusa da tsaunin Everest.
An fara bincike kan harin da B0k0 Hàràm ta kai kan sojoji a Borno

An fara bincike kan harin da B0k0 Hàràm ta kai kan sojoji a Borno

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan harin da ƴan Boko Haram suka kai wa sojojin ƙasar a sansaninsu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar. Rahotanni sun ce harin na Boko Haram ya yi ajalin aƙalla sojojin Najeriya shida a sansanin sojojin da ke Damboa a ranar Lahadi, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito, inda ta ce tsagin Boko Haram na ISAWP ne suka kai harin. Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da harin, amma bai bayyana adadin waɗanda aka kashe ba. Sai dai ya ƙara da ecwa, "mun fara bincike kan lamarin. Za mu fitar da sanarwa game da harin nan kusa," kamar yadda ya bayyana wa BBC.