DA DUMIDUMINSA: Muna Tare Da Tinubu Dari-Bisa Dari, Inji Tsoffin Membobin Tsohuwar Jam’iyyar CPC Magoya Bayan Buhari
DA DUMIDUMINSA: Muna Tare Da Tinubu Dari-Bisa Dari, Inji Tsoffin Membobin Tsohuwar Jam'iyyar CPC Magoya Bayan Buhari
Magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karkashin kungiyar tsohuwar jam’iyyar CPC dake cikin jam’iyyar mai mulki ta APC, wanda Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya jagoranci hira da manema labarai a yau Alhamis sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis.
Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar ba sa jin dadin yadda Tinubu ke tafiyar da al’amura, kuma suna shirin ficewa daga jam’iyyar APC gaba ɗaya.
Cikin wadanda suka halarci taron a Abuja ranar Alhamis, wadanda kuma suka nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Tinubu, akwai Gwamnan jihar Katsina, D...








