Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa duk inda ga tafi zamu bishi – Abba Gida Gida
Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa - Abba Gida Gida
Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya sake jaddada kudurinsa na mara wa Sanata Rabiu Kwankwaso baya a dukkan harkokin siyasa.
Gwamna Yusuf ya sha alwashin bin tafarkin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa, "duk inda ya dosa a siyasa, magoya bayansa za su bishi."
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga kansiloli 484 daga kananan hukumomi 44 a fadar gwamnati ranar Lahadi.
Abba ya kuma karyata zarge-zargen da tsohon sakataren gwamnatin jiha, Baffa Bichi, ya yi masa, inda ya kira shi da "makaryaci marar kunya," yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin karya kuma abin dariya.
Gwamnan ya fi mayar da hankali kan zargin cewa Kwankwaso na karɓar Naira biliyan biyu duk wata daga gwamnatin jihar Kano, yana mai cewa wannan zar...








