Saturday, May 2
Shadow
Katsinawa sun nishadantar dani sosai, ji na yi kamar a garin mu nake>>Shugaban kasa, Bola Ahmad

Katsinawa sun nishadantar dani sosai, ji na yi kamar a garin mu nake>>Shugaban kasa, Bola Ahmad

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Katsinawa sun Nishadantar dashi sosai a ziyarar da ya kai jihar. Tinubu ya bayyana hakane bayan da mawaka ciki hadda Rarara suka wakeshi da yaren Yarbanci. https://twitter.com/NTANewsNow/status/1918607611420660172?t=hq3bHIKxYRmmRMKg7N5mYw&s=19 Ya jinjinawa mawakan inda a wasu lokutan aka hangoshi yana rausayawa.
An gano motoci 150 da aka sato daga kasar Canada a Najeriya, Gambia, Mauritania da sauran kasashen Afrika

An gano motoci 150 da aka sato daga kasar Canada a Najeriya, Gambia, Mauritania da sauran kasashen Afrika

Duk Labarai
'Yansandan kasa da kasa, Interpol sun gano motoci 150 da aka sato daga kasar Canada a kasashe daban-daban na Afrika. An yi bincikenne a tsakanin kasashen Afrika 12 a tsakanin ranekun March 17 to 30, 2025. Interpol sun ce sun hada kai da 'yansandan wadannan kasashe na Afrika wanda suka hada da Najeriya da Ghana. Hakanan sun ce an binciki motoci 12,600 inda aka gano wasu motoci an satosu ne daga kasashen Faransa, Jamus, Netherlands Yawanci motocin da aka kama Toyota ne, Honda da Peugeot. Mot9da yawa ne ake sacewa a Duniya duk shekara
Ƴànbìndìgà sun yi gàrkùwà da mata 25 a hanyar zuwa biki a Zamfara

Ƴànbìndìgà sun yi gàrkùwà da mata 25 a hanyar zuwa biki a Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mata 25 a garin Kurmi na ƙaramar hukumar Maru An ce dai an yi garkuwa da matan ne suna kan hanyar zuwa gidan bikin. Haka ma wasu ƴan bindigar sun yi garkuwa da aƙalla mutum 19 yayin da suka raunata ƙarin wasu da dama, a garin Galadi da ke ƙaramar hukumar Tsafe, duk dai a jihar ta Zamfara.
Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai matarsa ta gaishe da shugaban kasa, Tinubu

Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai matarsa ta gaishe da shugaban kasa, Tinubu

Duk Labarai
A yayin ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a daren ranar Juma'a, Tauraron mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara ya gabatarwa da shugaba Tinubu da matarsa, A'isha Humaira inda ta gaishe da shugaban kasar. https://twitter.com/abdullahayofel/status/1918552250688975253?t=ujjnjfaaHXn-GJEWleawMw&s=19 Shugaba Tinubu dai ya ji dadin wakar da Rarara ya masa sosai.
Kudin da ake zargin tsohon shugaban NNPCL da ma’aikatan sa da sacewa zasu iya fin wanda ake zargin tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Emefiele da sacewa>>EFCC

Kudin da ake zargin tsohon shugaban NNPCL da ma’aikatan sa da sacewa zasu iya fin wanda ake zargin tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Emefiele da sacewa>>EFCC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC zata fara binciken tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL watau Mele Kolo Kyari. Tare da kyari, akwai mutane 13 da suma za'a bincikesu wanda suka yi aiki tare dashi. Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa, Tuni aka kama wasu daga cikin tsaffin ma'aikatan sannan ana kan bin sahun sauran dan suma a kamasu. Majiyar tace sauran wadanda ake bincike tare da kyari sune: Abubakar Yar’Adua, Mele Kyari, Isiaka Abdulrazak, Umar Ajiya, Dikko Ahmed, Ibrahim Onoja, Ademoye Jelili, da Mustapha Sugungun. Sauran sune Kayode Adetokunbo, Efiok Akpan, Babatunde Bakare, Jimoh Olasunkanmi, Bello Kankaya da Desmond Inyama. Ana zargin dai Kolo Kyari da ma'aikatansa sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man ...