TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama’a ne kawai game da zargin Akpabio?
TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama'a ne kawai game da zargin Akpabio?
Daga Ibrahim Jamiu Adamu, Abuja
Da so samu ne ba zan ce uffan game da abin da ke faruwa tsakanin Sanatar da aka tura ta wakilci al’ummar Kogi ta tsakiya Natasha da Shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ba. Amma bayan dogon nazari sai na gane cewa tabbas wannan turka-turka ta jefa al’ummar da suka tura wannan baiwar Allah ta wakilce su tauye musu hakki.
Ga mai bibiyar lamuran da ke faruwa ya san yadda aka kawo inda muke a wanan batu na zarge-zargen Natasha. A waje na ina ganin ƙarara tana nuna ba ta san darajar abin da aka damƙa mata ba.
Mu fara da yadda ta watsar da haƙƙin wakilcin da miliyoyin mutane suka damka mata, kowa ya ga yadda take ta kalaman ɓatanci don neman tausayar al’u...








