Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyon: Mu bamu da gata ne, su kuma kirista suna da gata shiyasa maganar har ta kai kunnen Trump yayi magana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Kalli Bidiyon: Mu bamu da gata ne, su kuma kirista suna da gata shiyasa maganar har ta kai kunnen Trump yayi magana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Kirista na da gata da Jagoranci na gari ne shiyasa suka kai kara aka sauraresu. Yace ku kuma matsalar mu ko an kashe mutane karyatawa muke. Malam yace amma mafita itace ace duka 'yan Najeriya ne ake kashewa babu wata maganar addini kawai a kawo mana dauki. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7567884525938806034?_t=ZS-913r5SflRoX&_r=1
Zanje in gana da Trump in warware masa zare da abawa>>Shagaba Tinubu bayan da Trump yayi bharhazanar kawo khari Najeriya

Zanje in gana da Trump in warware masa zare da abawa>>Shagaba Tinubu bayan da Trump yayi bharhazanar kawo khari Najeriya

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa nan gaba kadan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan. Yace a kwai kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da Amurka inda yace a baya Amurkar ta sayarwa Najeriya da makamai Wanda ta yi amfani dasu wajan yakar matsalar tsaro. Hakan na zuwane kwana daya bayan da shugaban Amurkar, Donald Trump yayi barzanar kawo hari Najeriya idan gwamnati bata dauki mataki kan harkar tsaro ba.
Kalli Bidiyo: Na yi kuskure dana ce Kuskurene Halittar Talauci>>Inji Gfresh Al-amin

Kalli Bidiyo: Na yi kuskure dana ce Kuskurene Halittar Talauci>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya fito ya bayyana cewa, yayi kuskure a kalaman da yayi cewa halittar Talauci kuskurene. Ya bayyana cewa, yana so ya cene an kirkirarwa Najeriya Talauci da gangan. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7567900923209583880?_t=ZS-913iASUAwlt&_r=1 Gfresh a baya yayi Bidiyon inda ya fadi cewa halittar Talauci kuskurene a yayin da yake magana akan fadan Baana da A'ishatulhumaira.
Kalli Bidiyo: Bazan iya barin waka in koma makaranta ba saboda, masu digiri da yawa basu da abinda nake dashi irin su waya, mota>>Inji Bilal Villa

Kalli Bidiyo: Bazan iya barin waka in koma makaranta ba saboda, masu digiri da yawa basu da abinda nake dashi irin su waya, mota>>Inji Bilal Villa

Duk Labarai
Mawaki Vilal Billa ya bayyana cewa, ba zai iya barin wasannin barkwanci da yake ba ko kuma waka ya koma makaranta ba. Yace akwai masu digirin da sune ke basu kudi hakanan wayar da yake rikewa da motar da yake hawa, masu digiri da yawa ba su da ita. Saidai yace a yanzu zai iya komawa makaranta saboda ya kawo karfi zai iya rike kansa. https://www.tiktok.com/@cuteboy_backup/video/7567688724436602119?_t=ZS-913fbhsQo1B&_r=1
Qhasar Amurka ta zhargi Sarkin Musulmi da hannu wajan Muzhghunawa Kirista

Qhasar Amurka ta zhargi Sarkin Musulmi da hannu wajan Muzhghunawa Kirista

Duk Labarai
Tsohon Magajin garin Blanco City dake jihar Texas a kasar Amurka, Mike Arnold ya zargi me alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III da hannu wajan kisan kiyashi da aikata Jihadiy akan Kiristoci. Ya bukaci sarkin da ya fito ya kawo hujja wadda ke nuna cewa bashi da hannu a khiysan da akewa Kiristoci a Arewa. Saidai fadar sarkin ta bayyana cewa wannan zargi ne da bashi da tushe ballantana makama. Sannan tace ba zata ma bayar da amsa ba game da zargin. Sakataren fadar, Alhaji Saidu Maccido, yace Gwamnatin tarayya da Majalisar tarayya sun bayar da amsa kan wannan lamari dan haka hankalin sarki akan karfafa zaman lafiya yake ba irin wadannan maganganun ba.
An gano Naira Biliyan 11 a asusun bankin daya daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

An gano Naira Biliyan 11 a asusun bankin daya daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce an gano Naira Biliyan 11 a asusun daya daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Juyin mulki. Rahotan yace sojan me mukamin Colonel ne kuma yana aiki ne a karkashin wani soja me mukamin Brigadier General. Dda aka tambayeshi, yace kudin na wani tsohon Gwamna ne kuma kasuwanci suke shi da gwamnan. Rahoton ya kara da cewa a baya an taba kai sojan aiki a yankin Naija Delta.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi gwamnatin Tinubu ta dauki mataki kan matsalar tsaro ko ya aiko sojojin kasarsa zuwa Najeriya

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi gwamnatin Tinubu ta dauki mataki kan matsalar tsaro ko ya aiko sojojin kasarsa zuwa Najeriya

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi Gwamnatin Najeriya da cewa, ta dauki mataki na magance matsalar tsaro musamman wadda ta shafi khisan Khiyashi da ake zargin yiwa Kiristoci. Yace ya baiwa Ma'aikatar yaki ta kasarsa umarnin daukar mataki akan Najeriya muddin lamarin bai canja salo ba. Ya bayyana hakane a shafinsa na yanar gizo.
Na yi dana sanin Shiga Harkar Fim>>Inji Anfara

Na yi dana sanin Shiga Harkar Fim>>Inji Anfara

Duk Labarai
Tauraron Fina-finan Hausa da ake kira da Anfara ya bayyana cewa yayi dana sanin shiga harkar Fim. Ya bayyana hakane a hirar da Hadiza Gabon ta yi dashi inda ta tambayeshi wane abune yayi wanda yake dana saninsa. Yace shiga harkar fim itace a ko da yaushe idan ya tuna abin na damunsa sosai. Yace dalilin da yasa ba zai fita daga harkar fim ba shine idan ya fita zai fara daga farko ne a rayuwarsa.
Kalli Bidiyon sojan da ya Tona Asirin sojojin da suka yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, kuma ya dakilesu, har An kara masa mukami zuwa Lt-Gen

Kalli Bidiyon sojan da ya Tona Asirin sojojin da suka yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, kuma ya dakilesu, har An kara masa mukami zuwa Lt-Gen

Duk Labarai
Bidiyon wani babban sojan Najeriya na ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa, shine ya dakile Yunkurin juyin mulkin da aka yi zargin an shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. An ga sojan na ta rawa a wajan wani biki. Da yawa dai sun rika jinjinawa sojan da cewa dan kishin kasane duk dai labarin a kafafen sda zumunta kawai yake ta yawo. https://twitter.com/dipoaina1/status/1984030400373829780?t=Mm3D8FdcmS1FcTkIAOCPkQ&s=19 Sojoji sama da 40 ne dai rahotanni suka ce aka kama bisa zargin yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki. Saidai Hukumomin gidan soja da Gwamnatin tarayya basu bayyana cewa yunkurin juyin mulkin ne akawa shugaban kasar ba. Hakanan shugaban kasa Tinubu ya canjawa sojojin Najeriya da yawa wajan aiki.
Kalli Bidiyon: Na bar Kiristanci na koma Musulmi>>Inji Tauraron mawakin Najeriya, Burna Boy

Kalli Bidiyon: Na bar Kiristanci na koma Musulmi>>Inji Tauraron mawakin Najeriya, Burna Boy

Duk Labarai
Tauraron mawakin Najeriya, Burna Boy ya bayyana cewa ya bar Kiristanci ya koma musulmi. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi wadda Bidiyon ke ta yawo a kafafen sada zumunta. Da yawa dai sun yi ta mamakin cewa Burna Boy Musulmi ne ko kuma ya musulunta. https://www.tiktok.com/@clippedbyaloha/video/7567223741340454162?_t=ZS-912AxbSJ6yf&_r=1