Sunday, December 21
Shadow

G7 ta amince a yi amfani da kadarorin Rasha da aka ƙwace a ƙasashen duniya

Siyasa
Ƙungiyar Ƙasashen G7 masu ƙarfin masana'atu sun amince a yi amfani da ribar kadarorin Rasha da aka ƙwace, domin bai wa Ukraine ta yi amfani da su. Biden ya ce yarjejeniyar za ta hada da tura bayanan sirri, da bai wa sojoji horo da bin dokokin NATO da zuba kuɗi a masana'antu da ke Ukraine domin ci gaba da samar da makamai. Biden ya ce burinsu shi ne samar wa Ukraine tsaro ''na gaske'', da kuma turmusa hancin Rasha da ƙawayenta a ƙasa. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wannan ba abu ne da Shugaba Putin zai kawar da kai ya kyale ba.
Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara

Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara

Duk Labarai
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na rashin yin sulhu da 'yan bindiga. Yayin da yake gabatar da jawabi bayan ya shiga wani tattaki da ƙungiyoyin matasan jihar suka shirya a wani ɓangare na bikin ranar Dimokradiyya, Gwamnan Dauda ya ce zai yi duk abin da ya dace domin maido da jihar kan turbar zaman lafiya. ''Jiharmu na da tarihin zaman lafiya, amma sannu a hankali abubuwa suka fara taɓarɓarewa, sakamakon ayyukan ɓata-gari'', inji gwamnan. Gwamnan ya ce matsalar tsaro matsala ce da ta shafi kowa da kowa, don haka ya yi kira ga al'ummar jihar su haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiyar jihar. "A koyaushe ina faɗa ina maimaitawa bai kamata ka yi sulhu da kasasshe ba, mun ga yadda gwamnatocin da suka gabata suka yi yunƙurin sulhu da 'yan bindig...
Hoto: An daure wannan mutumin saboda ya cire kwaroron roba yayin da yake jima’i da wata mata da suka amince cewa zai yi amfani da kwaroron roba amma ya yaudareta ya cire bata sani ba

Hoto: An daure wannan mutumin saboda ya cire kwaroron roba yayin da yake jima’i da wata mata da suka amince cewa zai yi amfani da kwaroron roba amma ya yaudareta ya cire bata sani ba

Abin Mamaki, Jima'i
An daure Guy Mukendi me shekaru 39 tsawon shekaru 4 da wata 3 saboda cire kwaroron roba yayin jima'i ba tare sa sanin matar da yake jima'i da ita ba. Shi da matar dai sun amince su yi jima'i amma da sharadin zai saka kwaroron roba. Saidai ya yaudareta ya cire, anan ne ita kuma ta kaishi kara. A dokar kasar Ingila, idan mutum ya cire kwaroron roba ba tare da amincewar matar da yake jima'i da ita ba to kamar ya mata fyade ne. Mutumin dai ya bata hakuri inda yace dalilinsa shine ya dade bai yi jima'i ba amma duk da haka taki hakura inda ta yi amfani ma da sakon hakurin da ya aika mata a matsayin shedar cewa ya cire kwaroron robar. Mutumin dai ya ki amsa laifinsa amma hujjojin da aka samu akansa sun tabbatar da ya aikata abinda ake zarginsa da aikatawa dan haka aka yanke masa hu...

Cikin wata biyar

Gwajin Ciki, Haihuwa, Nakuda
Duk da yake cewa kowace mace da irin yanda ta ke daukar cikinta amma a wata 5 da daukar ciki, za'a ga girman cikinki ya bayyana. Jikinki zai fara canjawa yana daidaituwa da yanda cikinki ke kara girma. Ga wasu alamu da ke nuna cewa cikinki ya kai wata 5: Kafafunki zasu Kumbura: saboda nauyin da kika kara saboda cikin dake jikinki, kafafunki zasu iya kumbura, kwanciya a daga kafa sama yana taimakawa wajan magance wannan matsala. Ciwon kwankwaso: Saboda yanda cikinki ke fitowa, bayanki zai rika shigewa ciki wanda hakan zai iya kawo miko ciwon kwankwaso. Juwa: A yayin da jaririnki ya ke girma, yawan jinin dake gudana musamman zuwa kanki zai iya raguwa wanda zai sa ki ji juwa. Mura: Zaki iya fuskantar Mura, hancinki ya toshe ko kuma yayi ta yoyo, kai yana ma iya fitar da jini...

Ana haihuwa a wata takwas

Haihuwa
Eh, Ana haihuwa a wata takwas amma mafi yawanci dan sai an bashi kulawa ta musamman. Saidai kada ki tayar da hankalinki mafi yawanci duk wanda aka haifa a wata 8 sukan rayu kuma su yi rayuwa irin ta kowa. Kai har wanda ma aka haifa a wata bakwai sukan rayu su kuma yi rayuwa irin ta sauran mutane bayan an basu kulawa ta musamman bayan haihuwarsu. Dan haka idan kika haihu a wata 8 kada hankalinki ya tashi, kiwa abinda kika haifa fatan Alheri. Dalilin da yasa ake haihuwa a wata 8 ko wata 7 wanda ake cewa bakwaini: Idan kofar mahaifarki bata da kwari, ya kai cewa bata iya rike dan da zaki haifa, hakan na iya faruwa, za ta bude ki haihu a wata na 7 ko 8. Idan ya zamana kin taba haihuwa a wata na 7 ko 8, hakan zai iya sake faruwa. Idan 'yan Biyune suma ana iya haihuwarsu lok...

Alamun ciki yakai haihuwa

Haihuwa, Nakuda
Akwai alamu da yada dake nuna ciki ya jai haihuwa: Zaki iya jin zafi sosai kamar na lokacin al'ada. Zaki ji mahaifar ta matse sannan zata saki. Hakan zai iya ci gaba da faruwa, yana zuwa yana tafiya duk bayan mintuna 5, kuma lokaci na tafiya hakan na kara tsananta. Da kinji haka to a kira ungozoma ko kuma a kaiki asibiti, Haihuwa ta zo. Zaki iya jin ciwon baya sosai. A yayin da kike da ciki, wani ruwa me yauki yana taruwa ya kulle kofar mahaifarki, to a yayin da kika zo haihuwa, wannan ruwan zai fito waje, idan kika ganshi, me yauki ne kuma Pink to haihuwa ta zo, saidai wasu na haihuwa ba tare da ganin ruwan ba. Amma masana kiwon lafiya sun ce rashin ganin ruwan ka iya zama alamar cewa akwai matsala tare da ke ko abinda zaki haifa. Dan haka ya kamata a nemi ungozoma ko...
Hamas ta soki Blinken kan kalamansa game da batun tsagaita wuta

Hamas ta soki Blinken kan kalamansa game da batun tsagaita wuta

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Hamas ta mayar da martani ga suka daga sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dangane da jan ƙafa wajen amincewa da ƙudurin tsagaita buɗe wuta, inda ta ce ta yi abin da ya kamata game da tattaunawar zaman lafiya. Hamas ta bayyana cewa ta yi abin da ya kamata dangane da sabuwar shawarar tsagaita buɗe wuta da kuma duk shawarwarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta," inda ta banbanta matsayinta da Isra'ila, wanda ta ce ba ta fito fili ta bayyana amincewa da shirin tsagaita buɗe wuta ba. Blinken ya sha ambata cewa Isra'ila ta amince da shawarar tsagaita wuta, kodayake gwamnatin Isra'ila ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba. Da yake magana a Qatar a ranar Laraba, Blinken ya bayyana taƙaicin yadda Hamas ta mayar da martani, yana mai cewa Hamas ta gabatar da sauye-sauyen da ...
Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake fuskanta da ke janyo fushin jama'a. Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na jiya a yayin bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya. “Na fahimci matsalolin tattalin arziki da muke fuskanta a matsayinmu na kasa. Tattalin arzikinmu yana cikin tsananin bukatar gyara shekaru da yawa. Ba a daidaita shi ba saboda an gina shi a kan kura-kurai na dogaro da kudaden shigar da ake samu daga hako man fetur,” inji Tinubu. Tun bayan hawansa ƙaragar mulki a bara, Tinubu ya cire da tallafin man fetur wanda ya haddasa tashin gwauron zabin sufuri da farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin kasar. Dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan t...
Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Siyasa
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma'aikata mafi karanci a ƙasar. Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000. A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago. Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi. Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeya...