Shin matakan tsuke bakin aljihun CBN na tasiri wajen rage hauhawar farashin kaya a Najeriya?
Bankin duniya ya bayyana damuwa tare da kokwanto game da irin matakan tsuke bakin aljihu da babban bankin Najeriya yake dauka, domin shawo kan matsalar hauhawar tashin farashin kayayyaki da kasar ke fama da shi.
Cikin wani rahoto da bankin ya fitar, ya ce duk da irin matakan da Babban Bankin Najeriya CBN ke dauka kamar kara kudin ruwa a bankuna, har yanzu bata sauya zani ba.
Tuni dai masana tattalin arziki a Najeriya suka fara tsokaci kan rahoton Bankin Duniyar.
Dakta Murtala Abdullahi Kwara, masanin tattalin arziki ne, ya shaida wa BBC cewa, Bankin Duniya ya san da ma duk wasu tsare tsare da matakai da CBN ke dauka ba lallai su yi tasiri wajen magance hauhawar farashin kayayyaki ba.
Ya ce,”Dalilin da ya janyo haka kuwa shi ne kusan rabin tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne ...



