Sunday, December 21
Shadow

Yawan fitsari ga mai ciki

Gwajin Ciki
Yawan fitsari ga mace me ciki ba matsala bane, alamace ta daukar ciki saidai idan yayi yawa, yakan iya zama cuta. Yawan fitsari na faruwa ne ga mace me ciki saboda yanda jikinta yake canjawa saboda shigar ciki da kuma shirin haihuwa. Yawan fitsari na daga cikin alamun farko na daukar ciki. Yawanci yawan fitsari na farawane a mako na 10 zuwa 13 bayan mace ta dauki ciki. Yawanci mata masu ciki kan yi fitsari sau 6 zuwa 10 a rana. Saidai idan ya wuce haka, yana iya zama na ciwo. Kalan fisarin mace me ciki yakan kara duhu, daga ruwan dorawa, watau Yellow zuwa me ruwan dorawa sosai ko kuma Dark Yellow. Idan mace me ciki ta ji fitsari, yana da kyau, kada ta rikeshi, ta je ta yi, saboda rike fitsari yana da illa ga mace me ciki da danta.
Hukumar dake shirya gasar Euro wato (UEFA), ta bayyana wasu sabbabin dokoki guda uku da za a fara amfani da su a gasar ta bana wadda zata gudana a ƙasar Germany

Hukumar dake shirya gasar Euro wato (UEFA), ta bayyana wasu sabbabin dokoki guda uku da za a fara amfani da su a gasar ta bana wadda zata gudana a ƙasar Germany

Kwallon Kafa
Hukumar dake shirya gasar Euro wato (UEFA), ta bayyana wasu sabbabin dokoki guda uku da za a fara amfani da su a gasar ta bana wadda zata gudana a ƙasar Germany. Alƙalin wasa zai bayyana hukuncin da ya yanke kuma zaiyi bayanin hakan ga magoya baya ta hanyar sadarwar kunne kai tsaye (Headphones) Za a dinga bayar da bayanai kai tsaye zuwa ga masu sharhin wasa (Commentators) akan hukuncin alƙalin wasa bayan dawowar sa cikin fili daga ganin VAR domin a yiwa masu bibiyar wasan bayanin abun da ya faru kai tsaye. A kowacce ƙwallo za a saka na'ura wadda zata dinga fayyace wa alƙalin wasa satar gida da kuma batun taɓa ƙwallo da hannu a yadi na 18. Fagen Wasanni

Addu’a ga mai ciki: Addu’ar saukin haihuwa

Addu'a, Gwajin Ciki
Wannan addu'a da zamu baku anan manyan malamai sunce sadidan ce, an gwada akan mata dake nakuda kuma an yi nasara: Saidai kamin mu baku wannan addu'a, ga bayani kamar haka: A binciken masana malamai na sunnah sun ce babu wata addu'a da aka ware wadda aka ce mace me ciki zata rika yi. Malamai sunce akwai dai hadisan karya da ake dangantawa da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) akan addu'a ga mai ciki. Misali Akwai hadisin da aka ce, A lokacin da fatima(A.S) ta zo haihuwa, Ma'aikin Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yasa Umm Salamah da Zaynab bint Jahsh su zo su karanta mata Ayatul Kursiyyu, da kuma al-A‘raaf 7:54, Yoonus 10:3, da kuma falaki da Nasi, Saidai wannan hadisin karyane, domin karin bayani ana iya duba al-Kalim at-Tayyib (p. 161) na Ibn Taymiy...
Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass, sun yi kira ga Muhammadu Sanusi II yayi koyi da sawun Kakan sa Muhammad Sanusi l da aka cire ya hakura

Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass, sun yi kira ga Muhammadu Sanusi II yayi koyi da sawun Kakan sa Muhammad Sanusi l da aka cire ya hakura

Kano
Shugaban Darikar Tijjaniyya Mahi Nyass ya shawarci Lamido Sanusi da ya yi koyi da kakansa ta hanyar kin amincewa da kujerar sarautar Sarkin Kano. Sarki Sanusi shi ne jagoran kungiyar Tijjaniyya a Najeriya. An mayar da shi a matsayin Sarkin Kano a karshen watan da ya gabata bayan da Gwamnatin Jihar ta yi wa dokar masarautu gyara inda ta rusa masarautu hudu daga cikin biyar da ke Jihar tare da tube Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano. Mista Ado Bayero dai yana kalubalantar tsige shi ne a gaban kotu, kuma yanzu haka yana zaune a karamar fadar Sarkin bisa kin amincewa da umarnin Gwamnatin Jihar. Sai dai kungiyar ta Islama a wata takarda mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Yuni mai dauke da sa hannun babban shugabanta Mista Nyass ta bukaci Sanusi da ya ki amincewa da mayar da shi ...
‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

Jihar Zamfara, Tsaro
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ya kasa sarrafa gine-ginen tsaro a jihar. Lawal ya ce ba shi da iko a kan shugabannin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa suna karbar umarni daga manyansu. Da yake jawabi yayin wani taron birnin tarayya na bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba, gwamnan ya yi tir da ayyukan ‘yan bindiga a jihar. A cewar Lawal: “Da sunan, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wani jami’in tsaro na soja, ko ‘yan sanda ko na Civil Defence. “Suna karbar umarninsu daga manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, ina fata muna da, da ya kasance wani labari na daban. " Ya ce matsalar tsaro ba ta gyaru a jihar ba sakamakon katsalandan da ya b...
An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

Duk Labarai
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Chibuzo Emmanuel, dan shekara 40 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin karbar baturan jirgin kasa da silinda na sata. Hukumar NSCDC, ta gurfanar da Emmanuel tare da Adamu Danbaba mai shekaru 52 da laifin sata da kuma karbar dukiyar sata. Jami'i mai shigar da kara na NSCDC, Mista Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da ke yankin Arewa ta tsakiya, Kafanchan, ta shigar da kara a ofishin hukumar a ranar 13 ga watan Mayu. Audu ya bayyana cewa Danbaba ma’aikacin layin dogo ne ya saci batir din jirgin kasa guda biyu da silinda mai nauyin kilogiram 12 a ofishin sa ya sayar wa Emmanuel akan kudi N24,000...

Cin yaji ga mai ciki

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Cin abinci me yaji ga mai ciki bashi da matsala sam ko kadan. Kuma ba zai cutar da dan cikinki ba. Saboda yanayin bakin me ciki, zaki so cin abu me yaji dan kwadayi, masana sun ce zaki iya ci ba tare da matsala ba. Mutane da yawa na da tunanin cewa, abinci me yaji yana da hadari ga mai ciki amma hakan ba gaskiya bane. Saidai a sani ko menene aka yishi ya wuce iyaka zai iya bayar da matsala. Hakanan kowace mace da irin jikinta, wata Yaji zai iya zamar mata matsala, wata kuma bata da matsala dashi. Dan haka kinfi kowa sanin kanki. Yaji zai iya sa zafin kirji ko kuma rashin narkewar abinci wanda duka basu da mummunar illa ga me ciki. Jin kwadayin cin abinci me yaji ba matsala bane ga mace me ciki, ga wasu amfanin da abincin me yaji zai yiwa mace me ciki kamar haka: Cin...

Yadda mai ciki zata kwanta

Gwajin Ciki
Masana sun yi amannar cewa, da zaran ciki ya fara girma, an fi son mace ta kwanta a bangaren jikinta na hagu tare da lankwasa gwiwowin kafarta. Wannan tsarin kwanciya a cewarsu shine mafi jin dadi sannan zai taimakawa gudanar jini a jikin uwar da danta. Hakanan a cewar masanan, wannan salon kwanciyar yana hana kumburar kafar me ciki. Masana kiwon lafiya sunce kwanciyar ruf da ciki bata da illa idan ciki be girma ba amma idan ya girma a daina yinta. Masana sun ce kwanciya a gefen dama yana da illa amma kuma me ciki zata iya kwanciya a gefen dama na dan gajeren lokaci. Hakanan masana sun yi gargadin kada a kwanta rigingine, watau akan baya musamman idan ciki yayi nisa. Kwanciya akan baya na hana jini gudana yanda ya kamata a jikin me ciki da kuma dan dake cikinta. Hakana...
Hotuna: An kama wadannan malaman makarantar mata bayan da suka yi yunkurin yin taron dangi suwa dalibinsu fya-de

Hotuna: An kama wadannan malaman makarantar mata bayan da suka yi yunkurin yin taron dangi suwa dalibinsu fya-de

Abin Mamaki
Wasu malaman makaranta a kasar Amurka sun yi ritaya bayan da aka kamasu suna yunkurin yin taron dangi dan yiwa dalibinsu fyade. Malaman mata sunansu Alexsia Saldaris da kuma Jennifer Larson dake koyarwa a makarantar Joseph Craig High School dake garin Janesville dake jihar Wisconsin. An gano cewa, daya daga cikin malaman har ta aikewa da dalibin hotonta na batsa. Bayan da aka tunkareta da maganar, ta amsa cewa lallai ta aikawa da dalibin hotunan batsa. Hakanan sun kuma nemi dalibin ko zai sako musu karin wani dalibi ya zo su yi lalatar tare dashi. Yanzu haka dai hukumar 'yansanda ta garin Janesville tana bincike kan lamarin.
‘Ana samun ƙaruwar bautar da ƙananan yara a Najeriya’

‘Ana samun ƙaruwar bautar da ƙananan yara a Najeriya’

Abin Mamaki
Wasu alƙaluman hukumomin kare haƙƙin dan adam a duniya sun nuna cewa ana samun ƙaruwar cin zarafin ƙananan yara a wasu ƙasashen duniya musamman na Afrika, ta hanyar bautar da su, ko sanya su aikin wahala. Bayanai sun nuna cewa akwai yara fiye da miliyan 87 a duniya da ke aikin karfi ko aikatau, kuma sun fi yawa ne a arewaci da kuma yammacin Afrika. Arewacin Najeriya na daga cikin wuraren da wannan matsalar ke karuwa a cikin ƴan shekarun nan. Bincike ya gano cewa matsalolin cin zarafin da yara kanana ke fuskanta na dakushe musu rayuwa, da janyo musu tsangwama a cikin al'uma da sauran su. Kungiyar ba da agajin ta Save the Children ta ce tana bakin kokarinta wajen ganin an magance matsalolin, da tabbatar ganin an tallafawa wadanda suka samu kan su cikin irin wannan halin domin ing...