Ya ake gane cikin namiji
A yayin da kika dauki ciki zaki ta samun mutane suna miki magana da bayyana ra'ayoyinsu akan cewa, namiji ne kike dauke dashi ko mace.
Akwai dai maganganu na al'ada da camfe-camfe wanda a wannan rubutu zamu muku bayani dalla-dalla yanda lamarin yace a ilimance.
A ilimin likitanci, sun ce da zarar maniyyi ya shiga mahaifane ake tantance cewa namiji ne mace zata haifa ko mace.
Hakanan sunce kuma kalar ido, kalar gashi, da sauransu duk daga shigar maniyyi da kwan mace mahaifa duka ake tantancesu.
Al'aurar abinda ke cikinki zata fara bayyana ne a yayin da kika kai sati 11 da daukar ciki. Saidai duk da haka, ko da gwaji aka yi a wannan lokacin ba za'a iya tantance namiji ne zaki haifa ko mace ba.
Maganganun da basu da inganci da ake amfani dasu wajan cewa kin dauki cikin mace ko ...



