Yadda ake zobo mai dadi
YADDA AKE ZOBO DRINK
Abubuwan buqata
Sobo/zoboCucumberBawon abarbaDanyar cittaKanumfariFlavorSugarBevi mix cola da Bevi mix mangoKamshi (Wanda ake samu a cikin kayan yaji amma optional ne)Sai barkono kadan (optional)
Da farko za a tsince dim dattin da ke cikin zobo sai a zuba a tukunya babba a markada cucumber a wanke bawon abarba dik azuba akai,a zuba barkono kadan da kamshin kayan yaji (optionals ne) a zuba kanumfari da jajjagaggiyar citta akai sai a zuba ruwa a Dora kan wuta ya tafasa sosai a tace a kara ruwa akai a sake tacewa har sai zobon ya salamce sai a ajiye domin ya rage zafi sai a zuba sugar,flavor na ruwa,da kuma Bevi mix (wadanda ba sa so wannan zasu iya Saka iya sugar kawai) sai juya su su hade jikinsu sosai a kara tacewa sai a juye a jug or a kulla a Leda ko a robob...