Sunday, December 21
Shadow

Kwamitin sulhu na MDD ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kwamitin sulhu na MDDr ya yi, wani mataki ne na goyon bayan samar da zaman lafiya. Linda Thomas-Greenfield ta ce ƙasashen duniya sun haɗa kai kan yarjejeniyar da za ta ceci rayuka, da mayar da mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su gida da kuma taimaka wa fararen hula Falasdinawa. A rubuce dai ƙudurin na nuna cewa Isra'ila ta amince da yarjejeniyar wadda shugaba Biden ya sanar a watan jiya. Ita ma Hamas ta yi maraba da ƙuri'ar da Majalisar ta kada, amma har yanzu ba ta mayar da martani a hukumance ba. Wakiliyar BBC ta ce Amurka ta ce za ta ba da tabbacin cewa Isra'ila zata yi biyayya ga yarjejeniyar, muddin Hamas ta amince da ita. A yau Talata ne sakataren harkokin wajen Amurk...
An kashe sojojin Isra’ila huɗu a Rafah

An kashe sojojin Isra’ila huɗu a Rafah

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta hudu a Rafah da ke kudancin Gaza. A cewar wata sanarwa, sun mutu ne a lokacin da wani gini da aka maƙare da bama-bamai ya ruguje. Biyu daga cikin sojojin ƴan shekara 19 ne, wanda ya girme musu kuma yana da shekara 24. Sanarwar ta ƙara da cewa ƙarin wasu sojoji da dama kuma sun samu munanan raunuka. Kimanin sojojin Isra'ila 300 ne suka mutu tun bayan kaddamar da mamaya a Gaza. Yayin da yaƙin ya yi sanadin rasuwar Falasɗinawa 37,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.
Matatar Dangote ta ɗage fara samar da fetur a Najeriya

Matatar Dangote ta ɗage fara samar da fetur a Najeriya

Duk Labarai
Katafariyar matatar mai mallakar hamshaƙin ɗankasuwan nan, Alhaji Aliko Dangote ta ɗage ranar da zata fara fitar da man fetur domin sayarwa a cikin ƙasar zuwa watan Yuli. Attajirin ya ce an ɗage ne saboda sun samu wani jinkiri, amma ya bayar da tabbacin fara samar da man fetur ɗin a tsakiya zuwa ƙarshen watan goben, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta bayyana. Tuni dai wasu dillalan man suka yi rajista da kamfanin domin fara ɗaukar man tare da rarraba shi a fadin ƙasar. Haka kuma kamfanin ya fara sayar da man dizil da na jirgin sama a ƙasar. Tun a watan Disambar 2023 ne matatar ta fara aiki, inda ta ke tace gangan danyen mai 530,000 a rana. Mahukunta a ƙasar na fatan fara samar da man fetur daga matatar ta Dangote za ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ƙaran...
Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Labaran Atiku Abubakar, Siyasa
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwamnati...

Mataimakin shugaban Malawi ya mutu

Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulos Chilima ya mutu sakamakon haɗarin da jirgin da ke ɗauke da shi ya yi ranar Litinin. Shugaban ƙasar ta Malawi, Lazarus Chikwera ya ce "jirgin nasa ya daki dutse" ne inda jirgin ya tarwatse kuma mista Chilima da dukkan waɗanda ke cikin jirgin suka rasu. An dai samu tarkacen jirgin ne a kusa da wani tsauni. An dai kwashe awanni ana bincike domin gano jirgin saman da ke ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi. Jirgin saman ya ɓace ne a ranar Litinin da safe. Ana tunanin ya faɗi ne a dajin Chikangawa Forest da ke arewacin ƙasar. Ya fuskanci rashin kyawun yanayi abin da ya sa aka hana jirgin sauka a filin jirgin sama na Mzuzu. Shugaban Malawi ya ce ya ba da umarnin a ci gaba da aikin ceto mataimakinsa Saulos Chilima har sai an gano ...
Kaduna: Kotu Ta Dawo Da Wani Babban Basarake da El-Rufa’i Ya Tsige

Kaduna: Kotu Ta Dawo Da Wani Babban Basarake da El-Rufa’i Ya Tsige

Siyasa
Kotun masana’antu ta kasa da ke zamanta a Kaduna a ranar Litinin din da ta gabata ta yi watsi da tsige babban sarkin Piriga da ke karamar hukumar Lere, Cif Jonathan Pharaguwa Zamuna. Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bashir Attahiru Alkali, bayan ya tabbatar da cewa kotun masana’antu ce ke da hurumin sauraron shari’ar, ya ce gwamnatin tsohon Gwamna El-Rufai ba ta bi ka’ida ba wajen tsige sarkin Piriga mai daraja ta uku tare da ayyana aikin ya sabawa kundin tsarin mulki, ba bisa ka'ida ba, rashin adalci, maras amfani, kuma ba shi da wani tasiri. Kotun ta bayar da umarnin mayar da Cif Zamuna kan karagar mulki tare da biyan duk wani albashi da kuma alfarmar da aka ba shi. Sannan ta umarci gwamnatin jihar Kaduna da ta biya Cif Zamuna diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye masa hakkins...
Duk Wani Jami’in Zabe Da Ya Aikata Cin Hanci Da Rashawa Da Rashin Da’a Zai Fuskanci Hukunci — INE

Duk Wani Jami’in Zabe Da Ya Aikata Cin Hanci Da Rashawa Da Rashin Da’a Zai Fuskanci Hukunci — INE

Siyasa
INEC ta gargadi jami'anta Gabanin zaben gwamnonin da za a yi a ranakun 21 ga watan Satumba da 16 ga watan Nuwamba, 2024 a jihohin Edo da Ondo. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi gargadin cewa duk wani ma’aikacin hukumar da ya aikata cin hanci da rashawa da rashin da’a zai fuskanci hukunci mai tsanani a karkashin doka. Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Sabon Jagorancin Hukumar Kula Da Ayyukan Yan Sanda

Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Sabon Jagorancin Hukumar Kula Da Ayyukan Yan Sanda

Siyasa
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Mai Ritaya) a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC). Shugaban ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakatare da DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya) a matsayin mamba a hukumar. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC). Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar, shi ne wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce DIG Hashimu Argungu (Mai ritaya) ne sabon shugaban hukumar. Majalisar dattawa za ta tabbatar da nadin. Za a nada sauran mambobin hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda a kan lokaci, inji Ngelale. Bugu da kari, shugaban kasar ya amince da nadin Mr. Mohammed Sheidu a matsayin...
Ranar Dimokuradiyya: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar 12 Ga Watan Yuni a Matsayin Ranar Hutu

Ranar Dimokuradiyya: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar 12 Ga Watan Yuni a Matsayin Ranar Hutu

Siyasa
Daga Shafin Dimokradiyya: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokradiyya ta shekarar 2024. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babbar sakatariya ta ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Aishetu Ndayako, ta fitar ranar Talata a Abuja. Ndayako ta bayyana cewa ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar wannan rana. Ya ce a yayin da al’ummar kasar ke bikin ranar dimokuradiyya a tarihinta, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi tunani a kan irin kokarin da iyayenmu suka yi wajen ganin Nijeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya. Tunji-Ojo ya kara da cewa, ya kamata Najeriya ta kasance cikin kwanciyar hankali da zam...

Sojoji Ne Suka Ƙaƙaba Mana Obasanjo Ba A Barmu Munyi Zabin Mu Ba – Ambasada Wali

Siyasa
Sojoji Ne Suka Ƙaƙaba Mana Obasanjo Ba A Barmu Munyi Zabin Mu Ba - Ambasada Wali Ɗaya daga cikin jigo a siyasar Arewacin Najeriya kuma tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali ya ce gabanin zaben shekarar 1999, sojojin da za su miƙa mulki ga farar hula ne suka ƙaƙaba wa 'yan siyasa Cif Olusegun Obasanjo wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a waccan shekarar. Ambasada Wali wanda yana cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar PDP a shekarar 1998, ya ce "lokacin PDP da aka je kulla yarjejiniya a Jos a shekarar 1998, wanda kuma a lokacin soja ne ke mulki, ba a bar mu mun zaɓi abin da muke so ba." "Da sai a ƙyale mu mu zaɓi wanda muke so. Amma haka ba ta samu ba. Ba don shigowar soja ba, suka dan saka hannunsu, watakila da Obasanjo bai zama ɗan takara ba". "Kuskuren da muka yi lokac...