Friday, March 6
Shadow
Kalli Hotunan Gawar Shugaban Kungiyar Hamass da Kasar Israela ta kashe ba kyan gani

Kalli Hotunan Gawar Shugaban Kungiyar Hamass da Kasar Israela ta kashe ba kyan gani

Yakin gaza da isra'ila
Kasar Israela ta sanar da kashe shugaban kungiyar Hamass Yahya Sinwar a wani bata kashi da sojojin Israelan IDF suka yi dashi. Rahoton yace an iskeshi ne da wasu dogarawansa 2 inda aka bude musu wuta. https://twitter.com/Currentreport1/status/1846897625875841522?t=Bzplp2zCBL4IsOEkk-IQEA&s=19 Yahya Sinwar dai an haifeshine a sansanin gudun Hijira kuma ya taso yana yaki da nemawa kasarsa 'yanci har mutuwarsa.

Yadda ake hada maganin infection

Magunguna
Magungunan infection na da yawa. A wannan rubutun zamu kawo muku magungunan Infection na gargajiya. Yogurt da Zuma: Yogurt da zuma ana iya hadasu a sha dan magance matsalar Infection, ana kuma iya samun Yogurt din wanda bai da suga ko wanda aka hada a gida a hada da zuba a shafa a gaban mace, kada a tura ciki,shima yana maganin infection sosai. Man kwakwa: Man Kwakwa na da matukar tasiri sosai wajan magance matsalar Infection musamman wanda yake sa yawan kaikai, yanda ake yi shine kawai a samu man kwakwa sai a shafa a gaban mace, ana iya yin hakan sau daya kullun har a samu sauki. Saka Tsumma Me sanyi: A samu ruwan sanyi a samu tsumma me tsafta a sakashi a ciki, sai a dora akan gaban mace. Hakan baya maganin infection amma yana sanyawa a samu saukin kaikayi da infection ke sawa. ...

Ganyen gwaiba na maganin infection

Magunguna
Ana amfani da Ganyen Gwaiba wajan magance matsaloli daban-daban na jikin dan Adam. Kuma infection musamman na gaban mata na daya daga cikin abubuwan da ake amfani da ganyen gwaiba wajan magance su. Saidai amfani da ganyen gwaiba wajan magance infection na mata a gargajiyance ne kadai ake hakan kuma ana yi ne ta hanyar dakashi ko markadashi a shafa a gaban macen. Hakanan a wani kaulin ana amfani dashi wajan magance kaikayin gaba na mata, shima ba turawa ake yi cikin gaban ba, shafawa ake yi. Saidai duka wannan a kimiyyar lafiya ba'a tabbatar dashi ba amma kuma ba'a bayyana wata illa da amfani da ganyen gwaban ke da ita ba wajan magance infection. Ma'ana mutum zai iya gwadawa da neman dacewa, saidai a bi a hankali kada a yawaita amfani da ganyen kwaban saboda duk kyawun abu i...

Alamomin nakuda

Haihuwa, Nakuda
Akwai alamomin nakuda da yawa, ga wasu daga cikinsu kamar haka: Jin matsewa a gabanki, zai rika matsewa yana budewa. Zaki rika jin shi kamar lokacin da kike jinin al'ada. Yayin da ruwa me kauri ya zubo daga gabanki. Ciwon baya. Jin kamar zaki yi kashi wanda hakan yana faruwane saboda yanda kan danki ke shirin fitowa waje. Da kin fara jin wannan alamomi to a garzaya a tafi Asibiti ko a kira ungozoma. Sauran Alamomin sun hada da zubar da jini. Abin cikinki ya daina motsi sosai.
Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima basa Najeriya, Saidai Fadar shugaban kasa tace Shugabancin Najeriya ba zai samu Tangarda ba

Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima basa Najeriya, Saidai Fadar shugaban kasa tace Shugabancin Najeriya ba zai samu Tangarda ba

labaran tinubu ayau
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima basa Najeriya. A yayin da shugaba Tinubu ya tafi kasar Ingila inda daga can ya wuce Faransa. Shi kuwa mataimakinsa, Kashim Shettima ya tafi kasar Sweden ne. Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya bayyana cewa hakan ba zai kawo tangarda ga shugabancin kasarnan ba. Yace a yanzu da ake da kafafen sadarwa na Zamani duk inda shuwagabannin suke suna gudanar da ayyukansu yanda ya kamata. Yace shugaba Tinubu ya tafi hutun sati 2 ne yayin da shi kuma Mataimakinsa,Kashim Shettima ya tafi kasar Sweden wajan gudanar wa da Najeriya aiki.
Me dokar Bacci:Kalli Bidiyon yanda dansandan Najeriya yawa karamar yarinya me shekaru 16 fyàdè a cikin ofishin ‘yansandan, Bidiyon ya nunshi yana tsaka da aikata laifin

Me dokar Bacci:Kalli Bidiyon yanda dansandan Najeriya yawa karamar yarinya me shekaru 16 fyàdè a cikin ofishin ‘yansandan, Bidiyon ya nunshi yana tsaka da aikata laifin

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Hukumar 'yansandan Najeriya ta kama wani jami'inta a South Ibie dake jihar Edo saboda zargin yawa karamar yarinya me shekaru 16 fyade a ofishin 'yansandan. Wata 'yarsanda mace ta dauki bidiyon faruwar lamarin inda aka ga dansandan na saka wando bayan an kamashi. Ya samu damar yiwa yarinyar fyadene bayan da ta fita hayyacinta. Kakakin 'yansanda na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an gano dansandan da yayi wannan aika-ai...
Hoto: An kama mahaifi da yawa diyarsa me shekara daya fyàdè

Hoto: An kama mahaifi da yawa diyarsa me shekara daya fyàdè

Abin Mamaki
'Yansanda a jihar Anambra bisa hadin gwiwar kungiyar 'yanci sun kama wani magidanci me shekaru 46 bisa zargin yiwa diyarsa me shekara daya fyade. Mutumin me suna Christopher Ugwunna Azubuike An kamashi ne a kauyen, Uratta Amaogwugwu dake karamar hukumar Isialangwa North a jihar. Diyar tashi ita daya ce tilo suka haifa wadda ke da shekara 1 da watanni 9 da haihuwa bayan sun shafe shekaru 5 da yin aure. An kai yarinyar Asibiti kuma likitoci sun tabbatar da cewa an mata fyade. Wanda ake zargin yana hannun 'Yansanda kuma ana ci gaba da bincike.
Akalla Mutane 90 ne Suka Rasu Yayin da Sama 50 Ke Asibiti Bayan Fashewar Tankar Man fetur a Jigawa

Akalla Mutane 90 ne Suka Rasu Yayin da Sama 50 Ke Asibiti Bayan Fashewar Tankar Man fetur a Jigawa

Jihar Jigawa
Rahotanni da ga jihar Jigawa na cewa a kalla mutane 100 sun rasa ransu biyo bayan fashewar tankar mai a garin Majia dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa. An ruwaito cewa fashewar ta auku ne a daren jiya Talata da misalin ƙarfe 11 na dare. Rahotanni na bayyana cewa akalla sama da mutum100 Kuma sun jikata sanadiyar fashewar tankar man, kamar yadda gidan Rediyon Sawaba FM Hadejia suka ruwaito.

Hanyoyin gyaran gashi

Gyaran Gashi
Kina son samun gashi me sheki, tsawo da lafiya? Ga hanyoyin da zaki kula dashi yanda ya kamata kamar yanda likitoci masu kula da gashi suka tabbatar. Ki kula da kalar gashinki sannan ki rika sayen man gashi wanda ya dace da kalar gashin kanki, watakila gashinki murdaddene, ko wanda yake a mike ne ko me kauri ne ko sirara ne, dan haka ki kula a wajan sayar da man gashi,mafi yawanci ana bayyana kalar gashin da ya kamata a yi amfani da kowane man gashi sai ki sayi wanda ya dace da gashin kanki. A rika kula da gashi yayi maski ko ya yi datti a rika wankeshi: Ya danganta da kalar gashin kanki, misali idan gashin kanki me tsawo ne kuma matsirar gashin na fitar da maski sosai to ya kamata kina wankeshi duk wata. Idan kuma gashinki yawanci a bushe yake, yana da kauri, kuma murdaddene,...