Saturday, December 20
Shadow
DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

Siyasa
Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun ki amincewa da tayin Naira dubu 60 mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta ga. Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, Hajiya Halimah Salihu Ahmed ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a. A tuna cewa a ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, suka shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan sun ki amincewa da tayin N60,000 da gwamnatin tarayya tayi a matsayin mafi karancin albashi. Amma daga baya sun sanar da cewa za su sassauta yajin aikin na tsawon mako guda domin ba da damar tattaunawa da gwamnatin tarayya, wadda ta yi alkawarin kara albashin daga N60,000. Sai dai gwamnonin sun ce mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 60 ba mai yiwuwa ba n...
Mu daina jin tausayin Mutane, idan Allah ya dandana musu, suka sha wuya zasu dawo hayyacinsu>>Dr. Ahmad Gumi akan yanda mutane suke wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai da kuma kasa kalubalantar Azzaluman shuwagabanni

Mu daina jin tausayin Mutane, idan Allah ya dandana musu, suka sha wuya zasu dawo hayyacinsu>>Dr. Ahmad Gumi akan yanda mutane suke wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai da kuma kasa kalubalantar Azzaluman shuwagabanni

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa a kyale mutane su dandana wahalar Rayuwa watakila hakan zai sa su shiga taitayinsu ta yanda zasu rika kalubalantar azzaluman shuwagabanni. Ya bayyana hakanne da yammacin yau, Juma'a, 7 ga watan Yuni yayin da yake karatun littafin Muktasar a masallacin Sultan Bello dake Kaduna. Malam ya kara da cewa, mutane suna da wakilai a majalisar tarayya idan akwai abinda basa so zasu iya gayawa wadannan wakilai cewa shugaban kasa ya canja idan ba haka ba ...
Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin Kasafin kudi

Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin Kasafin kudi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin kasafin kudi. Gwamnatin zata ciwo bashinne a wannan shekarar ta 2024 kuma zata yi hakan ne dan samar da kudin da zata biya tallafin man fetur wanda zai lakume Naira Tiriliyan 5.4. Kafar yada labarai ta Reuters ce ta ruwaito wannan labari. Saidai Gwamnatin tarayya ta ci gaba da nanata cewa ita fa har yanzu bata biyan tallafin man fetur.
Na cika duk Alkawuran dana daukarwa ‘yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

Na cika duk Alkawuran dana daukarwa ‘yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, a yayin da ya cika shekara daya da fara mulkin Najeriya, ya cika alkawuran da ya daukarwa yan kasar. Tinubu ya bayyana haka ta bakin ministan yada labarai, Muhammad Idris. Ministab yace tun bayan hawansa mulki, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cika alkawuran tada komadar tattalin arziki. Yace ya cire tallafin dala dana nera da sauransu. Ga bayanin sa kamar haka: “Since taking office a year ago, President Tinubu has done what he promised on the economy: he has removed the fuel subsidy, floated the Naira, and instituted a raft of other reforms including changes to the tax code and waivers for foreign investors in critical industries including mining, energy, and infrastructure.”
Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Hajjin Bana, Tsaro
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama wasu mahajjata a otal din Emerald Hotel dake Ladipo a jihar Legas suna hadiye hodar Iblis da zasu tafi da ita kasa me tsarki. An kamasu ne ranar Laraba, 5 ga watan Yuni kamin tashin jirgin su zuwa kasa me tsarkin. Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace wadanda aka kamadin, Usman Kamorudeen na da shekaru 31, sai kuma Olasunkanmi Owolabi me shekaru 46, akwai kuma Fatai Yekini me shekaru 38, sai Ayinla Kemi.me shekaru 34. Yace an kwace dauri 200 na hodar Iblis din daga hannun wadanda ake zargi.