Saturday, December 20
Shadow
Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akumeya bayyana cewa, ko direbobin gidansa ba zai iya biyansu Naira dubu dari ba a matsayin mafi ƙarancin albashi

Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akumeya bayyana cewa, ko direbobin gidansa ba zai iya biyansu Naira dubu dari ba a matsayin mafi ƙarancin albashi

Siyasa
Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akumeya bayyana cewa, ko direbobin gidansa ba zai iya biyansu Naira dubu dari ba a matsayin mafi ƙarancin albashi. Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana haka ne a wajen taron Majalisar Koli ta (NEC) Yayin marabtar kungiyar Kiristoci ta (CAN) a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja.. Akume ya ce " ba zan iya biyan direbobi na Naira dubu dari ba domin su 4 ne ya zama wani karin nauyi akaina" Ballantana kungiyar kwadago.. A ina muke samun kudaden da kungiyar kwadago ta buƙata ? Inji shi
Hoto:Ni dai zan so diyata ta zama ‘yar madigo dan kada ta yi mu’amala da maza>>Inji Wannan matar

Hoto:Ni dai zan so diyata ta zama ‘yar madigo dan kada ta yi mu’amala da maza>>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wata Mahaifiya ta bayyana cewa ita zata so 'ya'yanta su zama 'yan Madigo dan kada su yi ma'amala da maza. Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace sauran mata ma tana basu shawarar su zama 'yan madigo dan gujewa ma'amala da maza. Ta bayyana hakane a matsayin martani kan kisan da wani mutum dan kungiyar asiri yawa 'yan mata 2.
‘Yan Bindiga sun kashe mutane 12 ciki hadda ‘yansanda 7 a jihar Zamfara

‘Yan Bindiga sun kashe mutane 12 ciki hadda ‘yansanda 7 a jihar Zamfara

Jihar Zamfara, Tsaro
A ranar Alhamis, 'yan Bindiga sun kai hari garin Magarya dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara inda suka kashe mutane 12 ciki hadda 'yansanda 7. A cikin wadanda aka kashe din akwai daya daga cikin Askarawan Zamfara, da kuma mutane 4 daga kauyen. Kwamishinan 'yansandan jihar, Muhammed Shehu Dalijan ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace 'yan Bindigar sun kai harinne akan mashina au kusan 300 inda suka zagaye 'yansandan suka bude musu wuta suka kashe 7 da jikkata da yawa daga ciki. Ya kara da cewa, 'yan Bindigar sun ji haushine 'yansanda sun hanasu kai hari kauyen shekaru 2 tun bayan da aka kaisu kauyen. Saidai yace zasu kara yawan 'yansanda a garin. 'Yan Bindigar dai sun kone gidaje 2 da mota daya da sauran wasu abubuwa.
Kalli Hoton matar da aka kama da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara, da kuma wasu ‘yan Boko Haram da suka tuba

Kalli Hoton matar da aka kama da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara, da kuma wasu ‘yan Boko Haram da suka tuba

Borno, Tsaro
Wannan matar an kamata da harsasai 2000 zata kaiwa 'yan Bindiga a jihar Zamfara. Jami'an tsaron sun kamata ne da makaman amma babu cikakken bayanan me ya faru. Hakanan wasu 'yan Boko Haram, Baana Duguri, Momodu Fantami, Abubakar Isani da Zainami Dauda sun mika kansu wajan jami'n tsaro inda suka ce sun tuba.  An kwace makaman Bindigar Ak47 guda 2, da Harsasai masu yawa, da wasu kananan bamabamai da mashina 2, da dai sauransu. Sun bayyana cewa, sun fito ne daga garin Damboa.
Halin ƴan siyasar Najeriya ya fi na sojoji muni – Dalung

Halin ƴan siyasar Najeriya ya fi na sojoji muni – Dalung

Siyasa
Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce shi a fahimtarsa Najeriya ba ta kai mizanin da ake so ba dangane da romon dimokraɗiyya. "A shekara 25 ɗin nan a gare ni ba ta haifi ɗa mai do ba....An sami komabaya a tattalin arziki na Najeriya domin a 1999 lokacin da aka kawo wannan dimokraɗiyya, canjin dala a lokacin yana ƙasa da naira 10 amma a yau muna maganar kusan naira 1500." In ji tsohon ministan. Dangane da ilimi, Dalung ya ce "ba ma za ka taba haɗa ingancin ilimi na wancan lokacin da na yanzu ba." Harkar noma da kiwo da zamantakewa da tsohon ministan ya yi magana a kai, ya ce duka komabaya aka samu. Da aka tambaye shi ko daga wane lokaci al'amura suka taɓarɓare kasancewar shi ma ya kasance a wata gwamnati a baya. Sai ya ce " tsarin ne ba mai kyau ba. Ida...
A yau Juma’a wata kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya shigar gabanta

A yau Juma’a wata kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya shigar gabanta

Kano, Siyasa
Nan gaba a yau, Juma'a ne wata babbar kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya shigar gabanta, inda yake neman kotun ta hana kama shi, sannan kuma a mayar da shi gidan sarki na ƙofar kudu. Cikin waɗanda sarkin ya shigar da su ƙarar har da ƴansanda da jami'an tsaro na civil defence. Ranar 28 ga watan Mayu mai shari'a Amobeda Simon ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake ƙarar kada wanda ya hana shi shiga gidan sarki na kofar kudu ko hana shi amfani da duk wasu abubuwan da ya cancanta a matsayin sarki. Sannan umarnin kotun ya ce kada fitar da duk wanda yake cikin gidan sarki ba bisa ka'ida ba, har zuwa lokacin da kotun za ta saurari buƙatar da aka gabatar mata. A yau ne kuma kotun za ta zauna don sauraren ƙorafin da Sarkin, na 15 na Kano ya shigar. ...
Kalli Hotuna: Yanda ‘yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Kalli Hotuna: Yanda ‘yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Jihar Naija, Tsaro
Rahotanni daga Bassa da Erena a jihar Naija na cewa mayakan kungiyar B0k0 Hqrqm sun kai mummunan hari a yankin. Majiyar Hutudole tace an kai harinne a garin Makuba Lantan Bakin Kogi Bassa inda aka kashe mutane 7 ta hanyar yi musu yankan rago. Harin ya farune a jiya, Alhamis kamar yanda majiyar tamu ta tabbatar. Masu fada a ji a yankin sun nemi mahukunta da su kaiwa mutanen yankin musamman wadanda suka rasa muhallansu dauki. Mun samu hoton kan daya daga cikin mutanen da aka yanke, Allah ya kyauta.
Kadan ma kuka gani: Gwamnatin Tinubu tace matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba sun fi wanda aka gani a baya tsanani

Kadan ma kuka gani: Gwamnatin Tinubu tace matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba sun fi wanda aka gani a baya tsanani

Siyasa
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba, sai sun fi na baya tsanani. Hakan na fitowane daga bakin Ministan yada labarai, Muhammad Idris. Ya kara da cewa daukar wadannan matakai ya zama dole dan canja fasalin Najeriya ta yanda zata ci gaba ta fannin tattalin arziki. Ya bayyana hakane a wani rahoto da aka wallafa a wata jaridar kasar Ingila. Minista Muhammad Idris ya kara da cewa, Shugaba Tinubu gwarzo ne dan kuwa ya dauki matakan da shuwagabannin da suka gabata, suka kasa daukar irinsu. Babban matakin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta dauka wanda ya damu al'ummar kasar shine cire tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyyar jefa mutane cikin halin kaka nikayi. Hakanan gwamnatin Tinubun ta kuma cir...