Monday, December 15
Shadow
Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi, zata shiga yajin aiki

Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi, zata shiga yajin aiki

Siyasa
Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi. Wannan shine tayi na 4 da gwamnatin tarayya tawa NLC a cikin watanni 2 da aka shude ana tattaunawar. NLC dai ta sakko daga bukatar ta ta cewa sai an biya Naira 615,000 a matsayin mafi karancin albashi inda ta nemi yanzu a biya N118,000 zuwa N497,000. Wakilin NLC, Benson Upah ya bayyana cewa, Gwamnatin ba da gaske take ba da take cewa zata biyasu Naira Dubu sittin(60,000). Yace Gwamnatin ce ta jawo wannan matsala inda ta kawo tsare-tsare wanda suka saka al'umma cikin wahala
Yanzu-Yanzu:Kotu tace a fitar da Sarki Muhammad Sanusi II daga gidan Sarki na Kofar Kudu

Yanzu-Yanzu:Kotu tace a fitar da Sarki Muhammad Sanusi II daga gidan Sarki na Kofar Kudu

Kano
Babbar Kotu tarayya dake da zama a Kano tace a fitar da Sarki Muhammad Sanusi II daga gidan Sarki dake Kofar Kudu Kotun ta kuma ce a hukuncin da ta fitar yau, Talata, a mayar da Sarki Aminu Ado Bayero kan kujerar mulkinsa sannan a bashi dukkan abubuwan da doka ta bashi na sarauta. Alkalin kotun, S.A Amobeda ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne dan amfanin al'ummar Kano da zaman lafiyar jihar.
An ji harbin bindiga a kusa da fadar sarkin Kano

An ji harbin bindiga a kusa da fadar sarkin Kano

Kano
Rahotanni sun bayyana cewa, ranar Litinin an ji karar harbin bindiga a kusa da karamar fadar sarkin Kano dake Nasarawa. A nan ne dai Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune inda ya kafa fadarsa bayan da aka saukeshi daga sarautar Kano. Rahoton Premium Times yace an yi harbinne dan hana kama Aminu Ado Bayero wanda kotu ta bayar da umarnin fitar dashi daga fadar ranar Litinin. Wannan harbi da aka yi yasa mutane suka rika canja hanya suna komawa da baya. Rahoton yace ba'a tabbatar da ko jami'an tsaro ne ko masu tsaron fadar bane suka yi harbinba.
Tunda Ake Ýàķì Ďa Bòķò Hàràm Ķo Baŕàýìñ Ďaji Ba Mu Taba Ganin ‘Yan Sanda Sun Sito Sun Ce Suna Hadin Gwiwa Da Sojoji, DSS, Civil Defence, Road Safety Da Kwastam Ba, Sai Akan Dambarwar Masarautar Kano– Inji Barista Audu Bulama Bukarti

Tunda Ake Ýàķì Ďa Bòķò Hàràm Ķo Baŕàýìñ Ďaji Ba Mu Taba Ganin 'Yan Sanda Sun Sito Sun Ce Suna Hadin Gwiwa Da Sojoji, DSS, Civil Defence, Road Safety Da Kwastam Ba, Sai Akan Dambarwar Masarautar Kano. – Inji Barista Audu Bulama Bukarti, ƙwararren Lauya Mai Fashin Baƙi Kan Al'amuran Da Suka Shafi Tsaro Me za ku ce?
Sarautar Kano: Duk Gwamnatin Ganduje ce ta fara kawo matsalar nan ta raba kan ‘yan Uwan gidan Sarauta>>Sani Musa Danja

Sarautar Kano: Duk Gwamnatin Ganduje ce ta fara kawo matsalar nan ta raba kan ‘yan Uwan gidan Sarauta>>Sani Musa Danja

Kano
Tauraron Fina-finan Hausa, Sani Musa Danja ya bayyana cewa bai kamata ana amfani da siyasa wajan kawo rabuwar kai a jihar Kano ba. Sani Musa Danja ya bayyana hakane a wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Yace duka sarakunan nan 'yan uwan junane kuma duka mutanen kirki ne, bai kamata a zo a kawo wani abu da zai iya kawo gaba ko rashin jituwa a tsakaninsu ba. Ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano data gabata ce, watau ta Umar Abdullahi Ganduje ce ta kawo wannan matsala. Ya bada shawarar yin abinda ya kamata dan kawo zaman lafiya me dorewa a jihar ta Kano
Ya kamata majalisar tarayya ta yi dokar da zata hana ‘yan siyasa saukewa da wulakanta Sarakai>>Sheikh Dahiru Bauchi

Ya kamata majalisar tarayya ta yi dokar da zata hana ‘yan siyasa saukewa da wulakanta Sarakai>>Sheikh Dahiru Bauchi

Kano
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna rashin jin dadinsa kan sauke Aminu Ado Bayero da Gwamnatin jihar Kano ta yi. A jawabin da ya fitar ta bakin kakakinsa, malamin yace yana baiwa majalisar tarayya shawara ta yi dokar da zata hana 'yan siyasa saukewa da wulakanta sarakai. Gwamnatin jihar Kano, Karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero inda ta mayar da Sarki Muhammad Sanusi II akan kujerar. Lamarin ya jawo tashin hankula a jihar ta Kano inda Sarki Aminu Ado Bayero ya dawo yake ikirarin cewa shima sarkine.
Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi  kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Duk Labarai
Mahajjatan Najeriya a kasar Saudiyya sun koka da kalar abincin da ake basu duk da biyan Naira Miliyan 8 a matsayin kudin aikin hajjin bana. Daya daga cikin mahajjatan me suna Babagana Digima ne ya wallafa hoton kalar abincin da ake basu a shafinsa na facebook. Abincin dai koko ne da kosai guda 3. Babagana Digima ya kara da cewa, mahajjata yanzu sun koma bara dan neman abinda zasu ci saboda kudinsu dala $300 daya rage daga cikin dala $500 da suke da ita har yanzu ba'a basu ba. Hukumar Alhazai ta kasa, National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) da take martani akan lamarin, tace ta sa a yi bincike kan lamarin.
Kasar Japan zata gina Lifter wadda zata rika kai mutane sauran duniyoyi dake wajen Duniyar mu dan su ga yanda al’amura ke gudana

Kasar Japan zata gina Lifter wadda zata rika kai mutane sauran duniyoyi dake wajen Duniyar mu dan su ga yanda al’amura ke gudana

Duk Labarai
Wani kamfani na kasar Japan me suna Obayashi Corporation wanda shine ya gina gini mafi tsawo a kasar na shirin gina Lifter wadda zata rika kai mutane wajen Duniyar mu dan su ga yanda lamura ke gudana. Kamfanin yace zai fara wannan gini ne a shekara me zuwa watau 2025 wanda ake tsammanin kammalashi a shekarar 2050. Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki amma wanda yace zai hadiye kota sai a sakar masa a gani.