Saturday, December 20
Shadow
Da Duminsa: Mutum daya ya rigamu gidan gaskiya, wasu suka jikkata a Turmutsitsun daya faru a gidan karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle dake jihar Zamfara

Da Duminsa: Mutum daya ya rigamu gidan gaskiya, wasu suka jikkata a Turmutsitsun daya faru a gidan karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle dake jihar Zamfara

Duk Labarai
Turmutsutsu a gidan karamin ministan tsaro dake Gusau jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi sanadiyyar rasa rai daya wasu mutane 6 suka jikkata da yammacin ranar Alhamis. Rahotanni sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 7:30 na ranar Alhamis yayin da mutane suka taru a gidan nasa dan tarbarshi. Zagazola Makama yace wanda ya rasun sunansa, Khalifa Uzairu kuma dan kimanin shekaru 23 ne. Sannan akwai mutane 6 Ayuba Sani, Muhammadu Adams, Aliyu Aminu, Shaaban Hamisu, da Inusa Musa Shehu da su kuma suka jikkata suna karbar magani. An kai jami'an tsaro wajan sannan an fara binciken yanda lamarin ya faru.
Kalli Bidiyon abin ban mamaki: Wata tsohuwar malamar Jinya(NURSE) tace sukan canjawa mata jarirai bayan sun haihu, wani lokacin ma sukan dauke Jariri su ajiye ma me jego Mattaccen Jariri, su sayar da natan

Wata tsohuwar malamar Jinya, Nurse ta dauki hankula saboda irin bayanan data fitar kan irin yanda ta gudanar da aikinta. Tace wasu lokutan sukan canjawa me Jego Jariri ko kuma su dauke jariri me rai su ajiye matacce. Tace suna sayar da Namijin Jariri akan Naira Miliyan 4.5 ko Miliyan 3. Hakanan sukan sayar da macen Jaririya akan Naira Miliyan 2.5. https://twitter.com/instablog9ja/status/1989329219139051955?t=LzUAB8PG1hcsm4opoIK0ug&s=19
An baiwa ‘Yan Kwallon Najeriya kyautar Dala $120,000 bayan nasarar 4-1 da suka samu akan Kasar Gabon jiya

An baiwa ‘Yan Kwallon Najeriya kyautar Dala $120,000 bayan nasarar 4-1 da suka samu akan Kasar Gabon jiya

Duk Labarai
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu, sun baiwa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles Kyautar dala $30,000 akan kowace kwallo daya da suka ci, kamar yanda hukumar ta yi Alkawari. An basu wadannan kudaden a dakin canja kaya bayan kammala wasan. Kudin zasu kama jimullar Dala $120,000 kenan tunda kwallaye 4 'yan kwallon suka ci Gabon jiya. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1989341403743473669?t=PzA1PhpB30K0p8NJETDCqw&s=19
Kalli Bidiyo: Duk da Bidiyon da ya watsu kowa yaga abinda ya faru, Wike ya ce karya ake masa bai Zhagi Sojan Ruwa AM Yerima ba

Kalli Bidiyo: Duk da Bidiyon da ya watsu kowa yaga abinda ya faru, Wike ya ce karya ake masa bai Zhagi Sojan Ruwa AM Yerima ba

Duk Labarai
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, karya ake masa bai zagi sojoji ba a karawarsa da sojan Ruwa, AM. Yerima. Wike ya bayyana hakane a ganawa da manema labarai inda ya fadi cewa ya tallafawa ayyukan jami'an tsaro a matsayin Ministan Abuja da yayi. Saidai Sanata Dino Melaye ya bayyana mamaki da jin abinda Wiken yake fada. https://twitter.com/_dinomelaye/status/1989321220186091774?t=qXOAiy_fMZ_s0x7gov8G8A&s=19
Kalli Bidiyo: Ya zargi cewa, Saboda Naira Dubu 8 da rashin iya aiki, Asibiti a Abuja sun bar Jaririnsa ya Koma ga Allah

Kalli Bidiyo: Ya zargi cewa, Saboda Naira Dubu 8 da rashin iya aiki, Asibiti a Abuja sun bar Jaririnsa ya Koma ga Allah

Duk Labarai
Wannan mutumin Yayi zargin cewa, Wani Asibiti a Abuja ya bari jaririnsa ya mutu saboda rashin iya aiki da kuma Naira dubu 8. A Bidiyon da ya wallafa, an ganshi yana kuka a gaban asibitin yana zarginsu da rashin iya aiki da daukar 'yan Arewa aiki. https://www.tiktok.com/@talk2davic/video/7572121131570728199?_t=ZS-91OQ4G8xWG8&_r=1
Ni Dai da in Aikata Alfasha da Me Bakin Kyss wallahi gara Inyi Khadari abuna ya guntule>>Inji Ustaz Hussaini a yayin da suke musayar kalamai tsakaninsa da me bakin Kiss

Ni Dai da in Aikata Alfasha da Me Bakin Kyss wallahi gara Inyi Khadari abuna ya guntule>>Inji Ustaz Hussaini a yayin da suke musayar kalamai tsakaninsa da me bakin Kiss

Duk Labarai
Malam Dr. Hussain Kano dake fadakarwa a kafafen sada zumunta ya mayarwa da Me Bakin Kiss martani bayan zagin da ta yi masa. Malam yace yana mamakin mazan dake nemanta inda ya zargeta da kazanta. Kalli Bidiyon jawabinsa anan: https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7572492094338518328?_t=ZS-91OMOYZQMN6&_r=1
Kalli Bidiyo: Kirista ‘yar Jihar Borno ta zargi cewa Tunda Gwamna Zulum ya hau Mulki, Addininsa na Musulunci kadai da musulmai kadai yake taimakawa ba ya taimakawa Kiristoci

Kalli Bidiyo: Kirista ‘yar Jihar Borno ta zargi cewa Tunda Gwamna Zulum ya hau Mulki, Addininsa na Musulunci kadai da musulmai kadai yake taimakawa ba ya taimakawa Kiristoci

Duk Labarai
Wannan wata Kiristace da ta bayyana cewa, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum Musulmai da musulinci kadai yake taimakawa. tace baya taimakawa Kiristoci inda tace haka suke hada kudi su ginda coci amma a kona musu. Ta kuma zargi Gwamnan da yafewa 'yan Bìndìgà wanda tace daga baya suke zuwa su kara yiwa mutane tà'àddànci. https://www.tiktok.com/@ryma5570769784231/video/7572488734541614348?_t=ZS-91OLSctBVa4&_r=1
Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Duk Labarai
Shugaba Tinubu Ya Sabunta Nadin Buba Marwa A Matsayin Shugaban Hukumar NDLEA Har Na Tsawon Shekaru Biyar Shugaba Bola Tinubu ya sabunta nadin Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa Mai Ritaya, a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) na tsawon wa’adin shekaru biyar, a cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja ranar Juma’a. Marwa, wanda aka fara nada shi a shekarar 2021 a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi aiki a baya a matsayin Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kawar da Shan Miyagun Kwayoyi tsakanin 2018 da 2020. Sabon nadin zai kai tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar har zuwa shekarar 2031. Marwa wanda ya kasance tsohon gwamnan jihohin Lagos da Borno, ya samu horon soja a Nigerian Military School da ...