Amfanin lemun tsami ga mace
Lemun tsami (lemon) na da amfani mai yawa ga mace.
Ga wasu daga cikin amfanin sa:
Inganta lafiyar fata: Lemun tsami na dauke da Vitamin C, wanda yake taimakawa wajen kawar da kuraje, sassauta fata, da kuma gyara lalacewar fata sakamakon dadewa a rana inda zaka ga fuskar mutum ta yi duhu.
Kwari: Zaki iya amfani da lemon tsami wajen rage kiba da taimakawa wajen narkar da abinci. Yana taimakawa wajen rage kitsen jiki da kuma narkar da abinci yadda ya kamata.
Ciwon mara na al’ada: Lemun tsami na taimakawa wajen rage radadin ciwon mara na al'ada saboda yana dauke da wasu sinadaran dake rage kumburi da kuma ciwon, ana hada lemun tsami da citta a sa a ruwan dumi ko a tafasasu a bari ruwan ya huce a sha lokacin jinin al'ada dan maganin ciwon ciki.
Karfafa garkuwar jiki: Vitamin C ...


