Friday, January 9
Shadow
Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Siyasa
Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC na can na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja. Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe sa'o'i da dama gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago suna yajin aiki a Najeriyar, inda asibitoci da makarantu da sauran ma'aikatu suka kasance a rufe. Gwamnatin shugaba Tinubu ta nemi 'yan ƙungiyar da su janye yajin aikin su koma bakin tattaunawa. Wannan tattaunawar ita ce zangon farko kafin wadda za a yi a ranar Talata.

Ba za mu shiga yajin aiki ba – Ƙungiyar likitoci Kano

Kano
Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen jihar Kano, (NMA), ta ce likitocin da ke aiki a asibitocin Kano za su ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ke gudanarwa. Sakataren ƙungiyar reshen jihar Kano, Dr Abdurrahman Ali, ya shaida wa jaridar Daily Trust ranar Litinin cewa " mu ƙwararru ne saboda haka ba a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago muke kuma saboda haka ba za mu shiga yajin aiki ba". Ya ƙara da cewa “dukkannin likitoci da sauran ma'aikatan lafiya za su ci gaba da kasancewa a wuraren aikinsu. Bai zama lallai a cimma hakan ɗari bisa ɗari ba amma dai ba za mu shiga yajin aikn ba. E akwai yiwuwar ka je ka ga ma'aikacin da zai fito da fayil ɗinka ba ya nan amma kuma mambobinmu za su kasance a wuraren aikinsu.”
Gwamnatin Najeriya ta roƙi ‘yan ƙwadago su janye yajin aiki

Gwamnatin Najeriya ta roƙi ‘yan ƙwadago su janye yajin aiki

Siyasa
Gwamnatin Najeriya ta roƙi haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta 'yan kasuwa TUC da su janye yajin aikin da suka fara a yau Litinin. Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya nemi 'yan ƙwadagon su koma kan teburin tattaunawa, kuma bayanai sun nuna cewa yanzu haka ma 'yan ƙwadagon na tattaunawa da wakilan gwamnatin a Abuja. "Wannan roƙo ne muke yi cikin sanyin murya ga ƙungiyoyin ƙwadago da su dawo teburin tattaunawa da gwamnatin Najeriya da na jihohi ƙarƙashin jagorancin kwamatin lalubo mafi ƙarancin albashi," in ji ministan yayin wani taron manema labarai. A matsayinmu na gwamnati, muna muradin a cimma matsaya cikin lumana kuma za mu yi duk mai yiwuwa wajen cimma hakan. Jiya shugabannin majalisa sun gana da 'yan ƙwadago, yau mu ma mun sake gayyatar su don cigaba da tattaunawar."...

Kalli Bidiyo yanda NLC ta kulle gidan rarraba lantarki na Kaduna(KEDCO)

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NUEE dake karkashin NLC ta kulle gidan rarraba wutar lantarki na Kaduna, watau KEDCO. Ta kulle gidan wutar ne a yau, Litinin dan tabbatar da yajin aikin da suke kan neman karin mafi karancin Albashi. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/channelstv/status/1797610368522740126?t=Bb2fuE322DgypwK9UrwOew&s=19 In compliance with the nationwide strike, the National Union of Electricity Employees(NUEE) has also shut down operations at the Kaduna Electricity Distribution Company (KAEDCO). The union officials on Monday morning locked the premises of KAEDCO Headquarters in Kaduna.
Ku koma Teburin Sulhu, Yajin aiki wahala kawai zai kawo>>Sarkin Musulmi

Ku koma Teburin Sulhu, Yajin aiki wahala kawai zai kawo>>Sarkin Musulmi

Siyasa
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci kungiyoyin kwadago da su saurari Gwamnatin Najeriya domin yajin aikin zai jefa kasar cikin kunci. Abubakar ya ce bai kamata kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da Takwararta su gaji da tattaunawa da Gwamnati ba. A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Sarkin Musulmi ya bukaci kungiyar kwadago da ta janye yajin aikin. Sarkin Musulmi ya ce, “Ya kamata shugabannin kungiyoyin kwadago su yi la’akari da illar da yajin aiki yake da shi ga jin dadin ‘yan Nijeriya wanda suke iƙirarin don su suke yi da nufin kare muradun ƴan ƙasa, don haka su yi watsi da matakin na shiga yajin aiki. Muna kira ga kungiyoyin kwadagon da kada su sake jefa al’ummar kasar cikin wani hali na kuncin rayuwa domin abin da zai faru kenan idan suka aiwatar da shirins...
Mexico ta zaɓi mace ta farko shugabar ƙasa

Mexico ta zaɓi mace ta farko shugabar ƙasa

Siyasa
An zabi Claudia Sheinbaum a matsayin shugabar ƙasa mace ta farko a Mexico bayan gagarumar nasara da ta yi a zaɓen da aka gudanar a jiya Lahadi. Hukumar zaɓen ƙasar ta Mexico ta ce sakamakon farko da aka gudanar ya nuna tsohuwar shugabar birnin Mexico City ƴar shekara 61 ta samu tsakanin kashi 58 da kashi 60 na kuri'un da aka kaɗa a zaben. Hakan ya ba ta jagorar kusan kashi 30 cikin 100 a kan babbar abokiyar hamayyarta, 'yar kasuwa Xóchitl Gálvez. Ms Sheinbaum za ta maye gurbin jigonta a siyasa, shugaba mai barin gado Andrés Manuel López Obrador, a ranar 1 ga Oktoba, na wannan shekara.
Ƴan ƙwadago sun rufe hanyar shiga kamfanin man fetur na Najeriya

Ƴan ƙwadago sun rufe hanyar shiga kamfanin man fetur na Najeriya

Tsaro
Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya sun rufe hanyar shiga babban ofishin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) da ke Abuja, babban birnin ƙasar. Hakan ya zo ne jim kaɗan bayan fara yajin aikin ƴan ƙwadago, wanda ƙungiyoyin NLC da TUC suka kira kasancewar an gaza cimma matsaya tsakanin ƴan ƙwadagon da gwamnati game da albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikata. Yanzu haka dai ana cikin hali na rashin tabbas kan tasirin da yajin aikin zai yi, sai dai ana fargabar zai iya tsayar da al'amura a faɗin ƙasar. Ƴan ƙwadagon na buƙatar gwamnati ta amince da naira 497,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, sai dai gwamnati ta tsaya a kan naira 60,000.