Hotuna: Da cikina wata 4 kika shiga gidan mijinki kuma sai aurenki ya lalace, soja, Ibrahim ya gayawa Budurwarsa, Rukayya wadda yace ta yaudareshi
Wani soja me suna Ibrahim dake aiki a runduna ta 86 dake Ojo ya bayyana cewa budurwarsa, Rukayyat ta yaudareshi ta yi aure ba tare da saninshi ba.
Sojan ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook inda yace sun hadu da ita a watan Janairu kuma ta gaya mai ta na dauke da cikinsa.
Yace zai samu lokaci ya koma gida dan a fara maganar aurensu dan har 'yan gidansu sun san da ita.
Yace yana komawa gida yace mata ya dawo sai ta kashe wayarta ta canja layi, dalili kenan da basu hadu ba.
Ya kara da cewa, haka ya koma ya ci gaba da aikinsa, can kawai sai ya ga ta aika masa da sakon neman abuta ta Facebook.
Ko da ya amince sai take gaya masa cewa ta yi aure, nan ya ji ransa ya baci yace to ina maganar cikinsa da take dashi?
Sannan kuma ya mata alakawarin sai ya mata mugun abu, duk da b...







