Wani bincike ya nuna cewa yin jima'i sau daya a sati yana baiwa ma'aurata natsuwa.
Hakanan kuma wasu masana halittar dan adam sun bayyana cewa, yin jima'i kasa da sau 10 a shekara na nufin cewa ma'aurata na cikin auren da babu jima'i, watau hakan yayi kadan matuka.
Saidai kuma wani bincike ya nuna cewa, idan aka yi sabon aure, yayin da suke amarya da ango, ma'aurata kan yi jima'i kusan har sau 3 ko 4 a rana.
Hakanan, idan ma'aurata na son samun haihuwa, shima sukan yi jima'i da yawa da tunanin ko ciki zai shiga.
Magana mafi inganci itace, babu wata matsala idan mutum na yin jima'i a kullun.
Masana sunce, Jima'i na saka mutum farin ciki nan take kuma yana yayewa mutum damuwa.
Jima'i yakan iya zama yana da illa ne kawai idan:
Ya zamana ya hana ka yin ayyukan ci gaban ra...